← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 80

Sashe 3

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aisha kije ki sanar wa farida nache ta shirya hiyana ta mata duk abun da ya dache ta kai ta part ɗin mijinta, ita kuma salma ta shirya Zahra itama ta kai ta part na mijinta, ke kuma hauwa'u ki sanar da mardiya akan ta shirya lamrat da amrat suma ta kai su part na mazajen su, suyi sauri yana kai karshen maganar ya miƙe ya nufi betroom nashi.

Kallon Ummi Ammi tayi chikin fargaba da tsoro abun da zai biyo baya tace "ki tashi muje mu isar da sakon ko? "To kawai Ummi tache a tare suka miƙe suka bar palon

After some hours

Aunty farida da Hiyana ne zaune a bakin gadon a É—akin su hiyana Aunty farida ta tsara mata make up sosai

hiyana tayi kyau sosai kamar ka sache ta ka gudu da ita, sanye take chikin wata danƙareriyar lace pink colour ta yafa mayafi fari a kanta, chikin nitsuwa Aunty farida ta fata magana

"My Hiyana na san baki son Yaya prince Amma kiyi hakuri wan nan itache kaddarar ki kuma kisani hakan kamar jarabawa che Allah ya jarab cheki to kiyi kokari ki chinye jarabawar ki, kuma awan nan karon mu zaki tai makawa kinji ko? ina mai rokonki da ki daure nasan kina da hakuri sosai kuma nasan zaki iya to ki kara hakuri nasan zaki sha wahala zama da yaya prince amma ki daure In Sha Allah zamuyi nasara a kanshi kinji ko? kuma In Sha Allah kema zaki fara son shi yanzu zan faÉ—a miki ta yadda zamu fara yakar sa
abu na farko duk da nasan baya san ganin mace a kusa da shi amma ya zama dole kirin ƙa kasanche kusa dashi koda kuwa baya so

Abu na biyu ki dai na saka hijabin da kike sawa ki koma saka kananan kaya idan kin san yana gida, na uku zan roki maki alfarma a wajensa ko da yake ma koban roke saba nasan Abba zai che ke zaki rinƙa kai masa abinchi, kinga a nan ma zamu iya yin nasara, san nan idan ya dawo daga wajen aiki kiyi kokari ki saba masa da chire masa takalmi da socks da kan ki, nasan zaki sha wahalan hakan Kuma nasan zai iya chewa baya so to amma ko yache hakan karki dai na kirin ka yimasa kinji koh?

Kuka Hiyana take sosai kamar ranta zai fita rungumota Aunty farida tayi sosai tana bubbuga bayan ta tana bata hakuri awan nan yanayi Ammi ta shigo ta samesu "feeda Abban ku fa yace kiyi sauri ki kai Hiyana part na mijinta tun ɗazun fa su salma suka kai su Zahra" "to kawai Aunty farida tace tare da miƙewa ta kamo hannun Hiyana suka sufi wajen

Wani hawayen farinchiki Ammi taji ya zo mata burinta ya chika hiyana ta zama matar ɗan ta, sai dai awani ɓangare na zuchiyar ta kuma tana tausayawa hiyana sosai dan tasan Hiyana ba karamin wahala zata sha a wajen Bgs ba amma ta ɗauki kudirin taya hiyana yaki ta kowani hali

Maiduguri

É—ankareriyar mota kirar marcedes Benz che ta shararo a guje gudu mai motar yake sosai kamar zai tashi sama,ji kake kiiiiiii mai motar ya kwashe wata mahaukaciyar yarinya da ta zo tsallaka titi, wata mahaukachiyar birki yaja chikin sauri ya buÉ—e kofar motar ya fito kyakkyawa ne sosai fari tas dashi, chike da tashin hankali ya nufi inda yarinyar ke kwanche a saman titi ko motsi batayi kamar ta mutu ga jikin ta duk jini kanta ya fashe sosai, wani dogon salati yayi kafin ya karisa in da take juyawa yayi gabas da yamma babu kowa a kan hanyar, dawo da kallon sa yayi kan yarinyar, zuba mata manya manyan fararen idon sa yayi yana kallonta, gani yayi hannunta ya É—an motsa alamar bata mutuba chikin sauri ya duka ya É—auke ta ya nufi mota da ita gidan baya ya buÉ—e ya kwantar da ita ya rufe kofar ya buÉ—e gidan gaba ya shiga da sauri ya kunna motar yaja ta da gudu ya nufi asibiti da ita

Yana yin parking a chikin asibitin ya fito ya ɗauke ta chak ya nufi chikin asibitin da ita, kai tsaye office na Babban Dr ya nufa, batare da yayi Sallama ba dan tsabar ruɗewa shiga office ɗin yayi kai tsaye, Dr na zaune yaga an shigo masa office chikin sauri ya miƙe yana faɗin "Ahzan lfy!? subhanallah wan nan fa!? Yayi maganar yana nuna yarinyar da Ahzan ɗin ke ɗauke da ita chike da tashin hankali Ahzan yace " Dr walid ka taimake ni wlh yanzu shigowata garin nan ke nan ina sauri na karisa gida na buge yarinyar nan

Hannu Dr walid yasa yana masa nuni da gadon dake chikin office É—in yana faÉ—in "ka kwantar da ita tun da Allah yasa kai ma babban police ne yanzu zamu fara dubata, Ahzan bai jira Dr walid ya karisa maganar ba ya nufi gadon da sauri ya kwantar da yarinyar, chikin sauri Dr walid ya fara shirya kayan aiki

Fitowa waje Ahzan yayi ya zauna saman wata kujera tare da chiro wayar sa daga aljihu kira ya danna tare da manna wayar a kunnen sa, kira É—aya akayi picking, chikin rawar murya Ahzan ya fara magana "eh dady na shigo amma fa akoi matsala" chikin tsorata dady yace "wani matsala kuma Ahzan? "Accident na samu na buge wata mahaukachiyar yarinya che yanzu haka muna asibiti" "subhanallah ka turomin address É—in Asibitin da kuke ganin nan zuwa" to kawai Ahzan yace tare da katse kiran ya shiga massage turawa dady address din asibitin yayi san nan ya mai da wayar aljihun sa ya dafe kan sa da hannu biyu....

Dan girman Allah kumin afuwa jiya nache zanmuku page 2 to ina baku hakuri da rashin chika alkawari da nayi wlh ban samu charji bane sai wuraren 4 shiyasa amma In Sha Allah zuwa gobe zakuga sako masu zafi amin afuwa

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*💫STAR LADY💫*3

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 3*

Da sallama É—auke a bakin ta Aunty farida ta shigo chikin palon Bgs rike da hannun Hiyana daketa faman sharara kuka dan ita gani take shike nan kwanan ta ya kare, kai tsaye betroom nashi suka nufa ita kanta Aunty farida fargaban shigar betroom É—in take

Zaune yake a bakin katafaren gadon sa sanye da jallabiya baka ya dafe kansa da hannu biyu yana kallon kasa da alama wani tunani yake, jin Sallamar Aunty farida che ya sa ya ɗan ɗago kai kaɗan, batare da ya kalli in da suke ba kasa kasa ya Amsa sallamar, ƙarisowa chikin ɗakin sukayi jin shesshekar kuka yasa ya ɗago idon sa kallo ɗaya ya musu ya kauda kansa gefe yana kara yamutse fuska gefen gadon Aunty farida ta zauna tare da zaunar da Hiyana a gefenta, Chike da So da kaunar ɗan uwan nata tafara magana

"Prince ina ne ɗakin Hiyana? Shiru yayi kamar bai ji me Aunty farida tace ba "Prince Magana nake maka fa nache inane ɗakin Hiyana!? Ta karisa maganar tana ɗan kwaɓe fuska alamar bataji daɗin shiru da ya mata ba, shiru dai Bgs bai yi magana ba kamar ma bai san da shigowar mutane ɗakin ba, shiru Aunty farida tayi bata sake yi masa Magana ba dan a tsorache take da shi Almost 10mnt suna zaune shiru chikin muryan rarrashi Aunty farida ta fara magana

"Haba prince dan Allah ka bani amsa mana nasamu naje na kaita ta kwanta ta ɗan huta" shiru shiru kamar bai san da zaman su a ɗakin ba ganin hakan yasa Aunty farida ta miƙe ta kama hannun Hiyana ta nufi waje da ita ɗakin dake kusa da nashi Aunty farida ta shiga rike da hannun Hiyana, komai na chikin ɗaki iri ɗayane da nashi sai dai ban ban chin colour domin komai na ɗakin sa farine tas na hiyana kuma sky blue, a bakin katafaren gadon dake chikin ɗakin Aunty farida ta zaunar da Hiyana ta juya batare da tayi magana ba ta nufi waje gaba ɗaya ji tayi jikin ta yayi sanyi wani mugun tausayin hiyana ne ya sake dira a ranta, tunani take tana tafiya lallai Prince ya tabbata baya son hiyana ko kaɗan Allah sarki bai war Allah, ɗakin Bgs ta koma

Da Sallama tashigo É—akin kamar yadda ta barshi haka ta dawo ta same sa gefen sa ta dawo ta zauna chike da fargaban abun da zai biyo baya ta fara magana

"Kayi hakuri Prince na san ba'a kyau ta maka ba amma idan ka daure kayiwa iyayen mu biyayya zamuyi nasara arayuwa kaji? shiru Bgs yayi bai yi magana ba da alama bai da niyar magana kwata kwata, chigaba da magana Aunty farida tayi "pls É—an uwana kaji tausayin yarinyar nan marainiya che ba uwa ba uba kuma kana sane da irin wahala da ta sha arayuwar ta to dan Allah ko da ba zakuyi zama a matsayin mata da miji ba ina neman alfarma da ka É—auke ta kamar yadda ka É—auke ni dan Allah idan kamin hakan ka gama min komai pls" wani iska mai zafi ya furzar daga bakin sa kafin ya fara magana
Chapter 3 · 0% Book details