Sashe 57
Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune a palo ya samu Aunty Amarya tana shan fruits tsabar sauri a tsakiyar palon ya karisa sallamar tasa kallo É—aya Aunty Amarya ta masa ta kawar da kanta gefe saman sofa mai zaman mutun 3 ya zauna yana faÉ—in "barka da hutawa" shiru Aunty Amarya tayi bata tanka shi ba gyara zama yayi ya fara magana "Aunty Amarya dama magana nake san muyi da ke akan zulaihat" yana kokarin chi gaba da magana kenan wayar sa tayi kara alamar shigowar sako,chikin sauri ya duba wayar sakon Bgs ne kamar haka "kache mata kana son sanin suwaye iyayen yarinyar ne dan É—an uwan ka yana sonta domin daman sun kawo yarinyar gida ne saboda ni idan ka sanar da ita haka zata faÉ—a maka in da iyayen ta suke karka manta ka mata magana ta yadda zata fahimta kuma kada ka nuna mata kamar akoi wata matsala ka kula da yadda zaka mata magana dan uwace a garemu sannan ka bata hakuri dan fushi take da kai"tsaki Aryan yaja baya ya kammala karanta sako tunani yake me ya yiwa Aunty Amarya kuma da take fushi da shi gyaran murya yayi ya chi gaba da magana chikin nitsuwa "daman Bgs ne yake tambayar yarinyar da kuma iyayen ta dan yana son ta da Aure ne" da sauri Aunty Amarya ta ajiye apple dake hannunta ta juyo da kyau tana kallon Aryan chike da farinchiki ta fara magana "haba dai ai wannan abune mai sauki yanzu dai yarinyar bata nan daman kasan tana karatu a makka ne daman hutu tazo yanzu ta koma ne amma zan yi magana da mamanta sai musan ya za'ayi" chikin sauri Aryan yace "no yanzu dai ki faÉ—a mana gidan maman nata zamu kai mata ziyara sai muyi magana baki da baki zai fi amma zan so ache da baban ta zamuyi magana ba maman ba dan maganar Aure ba wasa ba zai fi muyi magana da baban ta" washe baki Aunty Amarya tayi tana ta farinciki tace "ai baban ta baya zama a kasar nan amma idan kunje wajen maman ta zata muku bayani yadda ya dace amma yaushe shi Safras É—in zai zo? "Next week zai zo amma Aunty Amarya me tsakanin ki dasu zulaihat É—in? "Yar aminiya tace" shiru Aryan yayi yana tunani yanzu awani layi zai sanya mahaifiyar sa mutuniyar kirki ko mutuniyar banza ache irin su zulaihat take hurÉ—a da su kai ina itama dole suyi bincike a kanta dan yanzu ya fara zargin ta itama
ganin yayi shiru ne ya sanya Aunty Amarya tace "Aryan lfy kuwa?" É—an firgigit yayi tare da É—ago ido yana kallon ta "lfylou yanzu dai ki bani address É—in maman yarinyar tare da number wayar ta" jiki har kerma yake wajen karanto masa number wayar tare da address É—in maman Zulaihat yana É—ago kai idon sa ya sauka kan diyana dake tsaye a bakin kofa ta harÉ—e hannu a kirji
alama ya mata da ido akan ta koma waje kar Aunty Amarya ta ganta turo baki tayi tare da juyawa ta fice miƙewa shima yayi yana faɗin "gobe zan kai wa maman yarinyar ziyara" "dawo ka zauna ai bamu gama magana ba wato kai bakada kishi ko? Da ka shigo bakaga ina fushi da kai bane?" Komawa yayi ya zauna yana faɗin "to uwata ta kai na me nayi kike fushi da ni? Harara ta wurga masa kafin tace "kana ji kana gani kake zaune da yarinyar da ta sanya hannun ta bugi mahaifiyar ka ko? Dan tsabar mutuwar zuciya tsabar sun mallake ka ko?" Dafe kansa yayi a ransa yana faɗin "wata sabuwa yau kuma tana Aunty Amarya ta ɓullo kenan shi idan ma ba dole ba me zai kawo sa wajen ta" afili kuwa zamowa yayi daga kujerar sa ya tsugunna kasa ya kamo kafafun ta ya fara magana "haba my mum kiyi hakuri kin san fa lokacin da abun ya faru bata a hayyacin tane amma ina mai baki hakuri a madadin ta" "au ita yarinyar tafi karfin tazo ta bani hakuri kenan? Girgiza kai yayi kafin yace "aa yanzu ma ba sai anjima ba zan kirata dole ta duka ta baki hakuri barina kirata" ya kai karshen maganar tare da miƙa wa ya fice daga palon tsaki Aunty Amarya taja tare da ɗaukar wayar tafara neman layin haj sadiya
Bugu É—aya haj sadiya ta É—auki wayar chike da farinchiki Aunty Amarya ta sanar da ita Bgs yace yana son zulaihat kuma gobe zasu kawo mata ziyara chike da farinchiki haj sadiya ta fara magana "kai ai shiya sanya na yarda da malamai na wlh na san aikin su kamar yan kan wukane yanzu duk bama wanna ba kin san dai zulaihat bata nan ko? sai kiran layin ta nake amma baya shiga kila tana chan tana sharholiyar ta takashe wayar ta ajiye wlh awannan karon idan Zulaihat ta dawo dole na kira dadyn ta yazo ya bada Auren ta na huta dan Allah ki san me zaki faÉ—a musu idan suka zo karsu tambayeta" tsaki Aunty Amarya taka kafin tace"na faÉ—a musu ta koma makaranta daman hutu tazo naija amma ina son ki sani wlh Safras ba kanwan lasa bane minti 2 ya masa yawa ya gano in da zulaihat take matikar yana da number wayar ta dan haka ki san yadda zakiyi ki nemo ta tun kan kiyi biyu babu " "In Sha Allah kar ki damu nan da kwana biyu zulaihat zata dawo dan dole awannan karon dadyn ta ya nemomin ita tun da ta kashe wayar ta" "yauwa haj sadiya kin ma tunamin kin fa san su Safras ba sa wasa akan abu ko bata lokaci yanzu ma sai da suka chemin da dadyn ta suke son yin magana dan da Aure yake son zulaihat sai kiyi kokarin ki sanar da dadyn nata" "zan sanar masa baya kasan ne shi ya sanya amma idan munyi waya zan faÉ—a masa na san yana jin chewa neman Auren zulaihat yar sa É—aya tilo a duniya za'a zo zai ajiye duk wani abu da yake ya zo Nigeria dan daman bashi da wata buri da ya wuce yaga ya aurar da ita" "hmmmm ke dai ki sanar da shi zamuyi waya anjima" tana gama faÉ—in hakan ta katse kiran tare da ajiye wayar a gefen ta
A ɓangaren Aryan kuwa a tunanin sa diyana na waje ko da ya fito bata nan kai tsaye part nasu ya koma tsaye a tsakiyar katafaren gadon sa ya hangota har ta sauya kaya zuwa riga da wando tana ta tikar rawa ba tare da waka ba abun ta mamaki ne ya kama shi ya ma kasa shigowa chikin ɗakin itako bata ma lura da shi awajen ba sai rawar ta take tika kamar babu kashi a jikin ta kai kache zata karye almost 30mins Aryan na tsaye ya zuba mata ido daya ga dai diyana ba dai na rawa zata yi ba sai ya tako zuwa chikin ɗakin shi yama rasa yarinyar nan wace irin yarinya ce mutunce karasa gane mata yanzu fa kafin ya fita take zaune shiru har da che masa tsoron yan ta'addan bai sake taba amma daga fitar sa yaje ya dawo har ta zama Michael Jackson wajen rawa kai sai dai yace Allah ya shirya masa matar nan tasa
Har ya haura saman gadon diyana bata dai na tikar rawa ba bata ma san ya shigo ba sai da ya sanya hannu ya riko ta sanna ta dakata tana mai da numfashi "my jidda daman kin iya rawa haka? Taɓe baki tayi kafin ta fara magana "eh mana a gidan Aunty farida na koya idan Aunty farida bata nan sai mu kunna waka ni da Junior muyi ta rawa yanzu ma na rasa ta ina ake kunna waka a jikin Tv kan nan ne shi ya sanya nake ta rawana ba waka" murmushin ya ɗan yi kafin yace "to yanzu dai sa hijabi muje ki bawa Aunty Amarya hakuri" waro idon tayi waje tana faɗin "me nayi mata da zan bata hakuri? "Babu komai kawai kizo kije kice tayi hakuri" turo dan karami bakin ta tayi ta fara magana "ni fa ba zan je ɗakin taba kuma ban son ta dan naji tace tasan wanchan yarinyar da tache zata maka fyaɗe wato ma Aunty Amarya che ta sanya akamamu a kashe mu kenan?Wlh na tsane su dukkan su ni na manta ma baka faɗa min menene fyaɗe bama" dafe kan sa yayi kafin yace "ba sai na faɗa miki menene fyaɗe ba nan ba da jimawa zan miki wani abu makamancin hakan yanzu dai umarni nake baki kizo ki bawa Aunty Amarya hakuri" zatayi magana ya ɗaure fuska sosai yace "bana son wata magana kiyi abun da nace miki kuma daga yau idan kika sake chewa baki son Aunty Amarya to nima ki sa aran ki bana son ki dan ba zan so wan da baya son mahaifiya ta ba" ganin ransa ya baci sosai ya sanya ta faɗo jikin sa tana faɗin "kayi hakuri zanje kuma ai bani na fara chewa bana son taba itace tace bata son mu ita da Aunty Maryam" ta karisa maganar kamar zatayi kuka rungumota yayi ajikin sa sosai yana faɗin "tana son ki mana tana sun ku gaba ɗayan ku kamar yadda take san mu kawai rashin samun fahimtar juna ne" hannu ta tura chikin gashim kansa tana faɗin "yaya Aryan yaushe zan maka kitso ne? Gashin kan nan yayi tsawo da yawa"ɗago habarta yayi yace "kin iya kitso ne?" chikin sauri ta ɗaga masa kai alamar eh "to muje ki bawa Aunty Amarya hakuri sai mu dawo ki yimani" chikin sauri ta sake sa ta ɗauko hijabin ta ta nufi waje tana faɗin "to karfa ka tafi wani waje ina dawowa yanzun nan" "to" kawai yace mata yana kokarin zama sai wani tunani ya faɗo masa "yanzu idan diyana ta je bawa Aunty Amarya hakuri ita kaɗai zaa iya samun matsala dan idan Aunty Amarya tayi wani magana da bai wa diyana daɗi ba diyana zata iya mai da martani dan bata bari ko ta kwana" tuna hakan yasa yayi saurin mikewa yabi bayan ta dan sulhu yake nema da Aunty Amarya ba zai so a sake samun wata matsala ba