← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 80

Sashe 22

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

tana É—ago blue eyes nata karaf sai kan face nashi yana tsaye a bakin kofar shigowa É—akin yana latsawa waya, chike da ruÉ—u da tashin hankalin ta diro kasa daga gadon ta sungunna, murya na rawa tace "ina kwana taya price, shiru kamar bai ma san da mutun awajen ba sai latsa wayar sa yake, Almost 15mins yana tsaye yana latsa waya ita kuma tana sugunne.

Chikin tsawa yace "in my room!! On my bed!! Chikin rawar murya tace "kayi hakuri yaya prince wlh ba zan... Bata kai karshen maganar ba ya daka nata wani uban tsawa wadda yasata mikewa ba shiri "shoot up!! Oya fara frog jump, daga yanzu har na dawo aiki! yana kai karshen maganar ya karisa shigowa chikin É—akin bai ko kalli in da take ba, ya wuche toile

tsallen kwaÉ—o hiyana ta fara, tun tana yi da sauri sauri har ta fara a hankali hankali, kuka kasa kasa ta fara dan ta gaji gashi yace daga yanzu har karfe 2pm idan ya dawo aiki, gashi mutun ne da idan yayi magana baya sauyawa dan haka No need ta bashi hakuri dan kota bashi bata bakin ta zatayi idan ma batayi Sa'a ba ya kara mata da wani hukunchin.

Wanka yayi ya fito ya shirya chikin wandon jeans blue da t-shirt ash, ya gyara lallausan bakin gashin kannan nashi ya watsa a baya ba tare da ya ɗaure gashin ba, booth blue ya sanya a kafar sa ya ɗaura wata danƙareriyar agogo diamond a hannun sa, wayar sa ya ɗauka ya nufi waje yana jin hiyana na kuka tana tsallen kwaɗo amma ko ajikin sa kamar ba mutun che ke kuka ba yayi fuchewar sa.

A harabar gidan ya sami Fahad na tsaye ya harÉ—e hannu a kirji shima ya shirya chikin wandon jeans blue da t-shirt fari, yana ganin Bgs ya fara É—aga masa gaisuwa, ba tare da ya amsa gaisuwar ba kasa kasa yace "yauma bina zakayi? Ya kamata ka fara Aikin ka fa, "yaya prince to ai kai ya kamata ka samomin aikin ko? "Aiki kam ai yana zaune yana jiranka duk time da ka shirya kuma duk matsayin kujerar da kakeso yanzu dai ina Yusuf da Khalid? "Basu fitoba" batare da ya sake magana ba ya wuche ya nufi waje motochin sa, Fahad ya bi bayan sa, dai dai lokacin Yusuf ya fito shida Lamrat ta rakosa har waje suna rungume da juna, ganin Fahad da Bgs yasa Lamrat kwache jikin ta da sauri ta fara gaidasu, Fahad ne kawai ya tsaya yana amsa gaisuwar tata shiko Bgs ko kallon in da suke bai yi ba yayi wuchewar sa.

Fahad na gama ansa gaisuwar lamrat shima ya ɗagawa Yusuf gaisuwa, da fara'a Yusuf ya amsa tare da tambayar "ina yaya khalid? "Bai fitoba" Fahad ya bashi amsa lokachin da yake wuchewa ya nufi wajen Bgs, juyowa Yusuf yayi yana fuskantar Lamrat, ya fara magana "my baby ki koma chiki sai mun dawo" "yanzu yaya Yusuf da gaske ba zaka tsaya kayi breakfast ba? "My baby na faɗa miki sauri muke akoi rundunar da yaya prince zai je ya sanya hannu a kan takardun su zasu tafi yaki da yan kunan bakin wake, jiya sun kama mana manya Manyan sojojin mu to shine za'a tura runduna 2 suje su yake su su kwato mana sojojin mu, baki ga gaba ɗaya jiya ran yaya prince a bache ba, kinga har yanzu ma ransa a ɓache dan haka bari nayi sauri karya hukuntani shi baya son jira sai dai a jirashi" kiss lamrat ta masa a kumatu tana faɗin "to a dawo lfy Allah ya tsare mani kai ya kareku da kariyar sa" "eyeee my baby yau ba fullanchin kenan ba jin kunya har da kiss na samu wow i can't forget this day" sunkuyar da kai kasa tayi tace "amma ai yaya Yusuf ba da kai zaa je yakin bako? Murmushi yayi tare da kama hanyar tafiya wajen Bgs yana faɗin "ba da ni za'a jeba ki koma chikin gida" "to kawai lamrat tace tare da juyawa ta goma chikin gida

Chikin motar Bgs ya isko Bgs da Fahad zaune nashi motar ya shige ya zaune.

"Kai Fahad kiramin layin Khalid" chewar Bgs yayi maganar yana kokarin chiro wayar sa daga aljihu dan yaji tayi kara alamar shigowar sako, yana kunna hasken screen É—in sai yaga sakon khalid ne, chere pin na wayar yayi ya shiga massage "kai Fahad kyale batun kiran khalid É—in nan muje kawai" "to yaya prince amma shi yaya khalid É—in yau lfy ba zai je wajen aikin sa ba? Shiru Bgs yayi kamar bai ji me Fahad yace ba, umarnin ya bawa sojojin sa akan sutafi, da gudu suka kunna mitochin suka bar gidan.

Tun hiyana na iya kuka har ta kasa sai dai numfashinta dake fita da sauri sauri, sai wani wahalallen nishi da takeyi, tun asuba har zuwa karfe 8am tana frog jump.

Tun tana iya É—aga kafarta har ta kasa ta yanke jiki ta faÉ—i kasan karfet É—in sumammiya

Maiduguri Nigeria
Chapter 22 · 0% Book details