← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 80

Sashe 48

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

slowly ya kai bakin sa saman nata da niyar ya sumbace ta amma sai ya zarce ya fara kissing nata ba tare da ya sani ba, sosai yake kissing nata tare da kara jawota jikin sa sosai duk abun da yake mata tana jin sa dan daman batayi barci ba da gangan ta faɗo jikin sa yaya Khalid ne ya rubuta mata a massage kar ta yarda ta rinƙa barci ba a jikin sa ba tarinƙa nuna masa kamar barci take ta mirgino jikin sa ta nuna kamar bata san ta faɗo jikin na shi ba,kara matse ta yayi sosai a jikin sa yana bata hot kiss tula tulan breast nata dake sokin sa a kirjin sane ya fara damun sa ɗan sassauta rungumar da ya mata yayi dan ya samu su ɗan raba jiki, kaɗan kaɗan yake jin feeling akan ta sai da yayi kissing nata mai isar sa sanna ya zame bakin sa daga nata tare da raba jikin su ya ɗan juya ya lumshe ido shi duk a tunanin sa tana barci bata ji me ya mata ba ita kuwa mutuwar kwanche tayi dan gaba ɗaya ya gama kashe mata jiki ya ruɗar da ita dannewa kawai take tunani ta shigayi anya zata iya biyewa shawarar yaya Khalid da yaya Aryan kuwa? Gaskiya wanna aiki ne mai wahala ba zata iya ba gaskiya sai dai su kawo wani shawarar da wanan tunani barci yayi awon gaba da ita, kusan tare barci ya ɗauke su

KANO NIGERIA

Auty Amarya na kokarin fita bedroom nata dan lokacin chin abinci yayi tasan yanzu gaba É—aya su Abba sun haÉ—u a palo dai dai zata fita wayar ta dake bedside drawer tafara rigging kamar bazata je ta É—auka ba sai kuma ta fasa ta koma taje ta É—auki wayar sunan hajj sadiya che ta bayyana saman screen É—in wayar zama tayi a bakin gado kafin tayi picking call É—in tare da manna wayar a kunnen ta

Daga ɗayan ɓangaren hajj sadiya tace "Hello hajj ya hajara Ykk"dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace "lfy Ykk" "Alhadulillah daman nakira na sanar da ke ne yanzu gagarabadau ya mutu sai dai na kaiwa malamina dake bayalsa ya yi mana aikin Farida da Aisha" miƙewa tsaye Aunty Amarya tayi tare da dafe kirji chike da raza na tace "yaushe ya mutu!? "Yanzun nan gani nan ma a kofar gidan sa yanzu baafi minti ɗaya ba"komawa Aunty Amarya tayi ta zauna gaba ɗaya jikin ta ya mutu tama rasa me zata che wa haj sadiya "haj ya hajara ina zulaihat ne? Tun shekaran jiya bata kirani awaya ba itama malamin mu na Niger ya kusa kammala aikin ta tsakanin ta da Safras"tsaki Aunty Amarya ta ja kafin tace "zulaihat bata koma wajen ki ba ai ni tun shekaran jiya da na ganta da safe ban sake ganin taba na yi tunanin ta gaji da zama da nine ta koma wajen ki ai" "aa zulaihat bata dawo waje naba kai amma wanna yarinyar yanzu a gidan naki ma sai data fita yanzu tana chan kila wani saurayin nata tabi yarinya kwata kwata bata jin magana ni Allah yasa malamin nan ma ya gama aikin nan da wuri mu sa mu ayi auren nan kila idan ta shiga gidan Safras ɗin ta rage yawon banzan nan,barima na kira layin ta dan uban ta koma ina take ta wuce ta dawo" guntun tsaki Aunty Amarya taja dan ita gaba ɗaya yanzu haushi ma suke bata daga zulaihat ɗin har Haj sadiyar "haj sadiya sai munyi waya yanzu zanje palo muyi breakfast ne kowa ya hallara saura ni zamuyi waya anjima" tana gama faɗin hakan ta katse kiran ba tare da ta jira amsar haj sadiya ba mayar da wayar tayi saman drawer gefen gadon ta miƙe ta fice daga ɗakin tana mai bakin ciki mutuwar gagarabadau

Da sallam É—auke a bakin ta ta shiga palon Abba gaba É—aya wayan da suka rage a gidan suna zaune saman table diyana na zaune kusa da Aryan É—in ta tayi shiru ta kasa chin abinci zama Aunty Amarya tazo tayi a kujerar kusa da Abba tana harara Aryan da diyana

"my diyana kici abinci mana" chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana,sai lokacin Aryan ya ɗago kai tare da ajiye wayar sa a gefe saman table ɗin ya jawo plate na abincin nata ya ɗauki spoon ɗin ya ɗibo chips ɗin ya kai mata bakin ta, shiru tayi bata buɗe baki ba kuma bata ɗago ba tana kallon kasa, mai da spoon ɗin yayi chikin plate ɗin ya ɗan rungumota da hannu ɗaya yana faɗin "my jidda menene kuma....bai karshen maganar ba yaji ta sake masa jikin ta gaba ɗaya a jikin sa kokarin faɗuwa take dan bai riƙe ta da kyau ba chikin zafin nama ya rikota da kyau yana faɗin "my jidda lfy me ya faru" miƙewa Abba yayi yana faɗin "suma fa tayi Aryan" tun Abba bai gama rufe baki ba Haidar ya miƙe da sauri ya nufi fridge ya ɗauko ruwa, ɗaukan ta Aryan yayi chak suka koma tsakiyar palo ya shinfiɗe ta saman karpet Haidar ya miƙo masa ruwa, chikin sauri ya balle bakin robar ruwan ya tarbo a hannu ya fara shafa mata a face nata gaba ɗaya su Ammi sun kewaye su suna jiran farfaɗo war ta zama saman sofa Abba da Aunty Amarya su kayi Ammi da Ummi kam sun kasa zama suna tsaye Omar Haidar suma suna tsaye,sai kwaɓe fuska Aunty Amarya take

Sau uku Aryan na zuba mata ruwa amma shiru bata farfaÉ—o ba sai a na huÉ—un ne taja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuchiya tun bata buÉ—e ido ba ta fara sambatu "Aunty farida yaushe ne jirgin mu zan tashi wlh na kosa na ga su hiyana ina kewar yaya Aryan kin san me Aunty farida ina zuwa gida Ammi zan fara runguma sai yaya Aryan sai kuma hiyana da Aunty Zahra aa na manta Ammi ce first sai Abba tukun nan yaya Aryan" shiru palon yayi suna sauraron sambatun diyana Allah sarki wato shine maganar ta na karshe tana cikin hayyacin ta lokacin guda Abba yaji idon sa ya chiwo da kwalla ba karamin tausayi diyana ta basu ba,mutun ya zauna chikin fitar hayyaci ba karamin abu bane, amma Alhadulillah dan da alama ta dawo hayyacin ta tun da har tana iya sambatu da sunayen yan gidan

Ji Aryan yayi ba zai iya chi gaba da jin sambatun nan nata ba tana tayar masa da hankali hannu ya sanya ya shafa fuskar ta tare da matsowa kusa da ita ya riƙe hannun ta ɗaya chike da kaunar ta ya fara magana "my jidda buɗe idon ki kallemu ai tun ɗazun jirgin naku ya iso gida" jin muryan Aryan ya sanya ta waro blue eyes nata da sauri tare da miƙawa zaune tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya miƙewa tayi da sauri ta rungumi Ammi tana murmushin tana faɗin "Ammi nayi kewar ki daman na faɗawa Aunty farida muna isa ke zan fara runguma" sosai Ammi ta rungume itama tana faɗin "my diyana nima nayi kewar ki sosai amma yanzu dai duk bamu ya kamata ki fara runguma ba mijin ki ya kamata ki fara nunawa farimcikin ki dan ya fimu bukatar ganin hakan" turun diyana ta tsaya chike da mamaki tace "Ammi miji kuma yaushe na samu miji" Abba ne ya ansa zanchen da chewa "Eh my daughter mijin ki" sakin Ammi tayi ta kariso wajen Abba tana faɗin "Abba wanene kuma mijin nawa? Da hannu Abba ya Nuna mata Aryan dake tsugunne ya kasa mikewa dan gani yake kamar har yanzu bata dawo dai dai ba a wani bangare na zuchiyar sa kuwa farincike yake yana godewa Allah da dawowar matar sa hayyacin ta

Kallon sa diyana tayi kafin ta ɗago ta kalli sauran jamaar palon chikin nitsuwa tace "Abba ni yaya Aiman nake so ba yaya Aryan ba da yaya Aiman mukayi alkawarin Aure ba yaya Aryan ba" tirkashi gaba ɗaya zuba mata ido jama'ar palon sukayi Aryan jin kalaman nata yake tamkar ana zuba masa garwashi a zuciya ashe Aiman yayi gaskiya shi diyana ke so chije lips nashi yayi lokaci guda idon sa ya sauya jijiyoyin kansa suka miƙe huci ya fara yi kamar wani zaki diyana ta haɗa masa zafi biyu lokaci guda na farko ta tuna masa da Aiman na biyu tace ba shi take so ba zuciyar sa zafi yake masa jiyake tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje,chikin zafin nama ya miƙe yana kokarin barin palon da sauri Abba ya dakatar da shi ta hayyar riko hannun sa yana faɗin "koma ka zauna" ba musu ya koma saman sofa ya zauna tare da dukar da kai kasa umarni Abba yayiwa su Ammi akan su zauna zama sukayi gaba ɗayan su, saman sofas

"Kai Omar kaje É—akin Aryan zakaga wata jaka baka mai É—an girma ka kawomin" chewar Abba da sauri Omar ya juya ya fice daga palon
Dawo da kallon sa Abba yayi kan diyana dake zaune kusa da Ammi ya fara magana "my daughter kiyi hakuri da Auren da na miki ba tare da na tambayeki ba, abu na gaba Allah ya yiwa Aiman rasuwa inason ki anshi Aryan a matsayin miji domin da Aryan da Aiman duk abu É—aya ne kuma Aryan ya riga Aiman fara son ki kema kuma Aryan ki ka fara so ba Aiman ba nasan kinche Aiman kike so ne ba dan komai ba sai dan alkawarin da kika masa akan zaku yi Aure nasan da kin san Aiman ya rasu ba zaki che hakan ba,ina jinjina miki da kokarin chika alkawari da ki kayiwa Aiman duk da ba shi kike so ba" shiru palo yayi ba abun da kakeji sai kukan diyana kuka take sosai kukan da take ne ya sanya Aryan É—agowa baya san kukan ta ko kaÉ—an idan tana kuka zuciyar sa zafi yake masa
Chapter 48 · 0% Book details