← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 80

Sashe 13

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawowa chikin ɗakin yayi ya ɗauki Lamrat chak kamar yar baby ya koma chikin toilet ɗin da ita, chikin baf ɗin wanka ya sanya ta, da sauri ta damke hannun sa dan zafin da ruwan yayi masa, wani irin ihu azaba ta saki tare da kankame hannun sa da karfi, kawar da kansa gefe yayi dan bai san ganin tashin hankali dake kan face nata, sosai lamrat ke masa kuka, jin kukan nata yake har chikin ranshi amma ba yadda zai yi dole ya nema mata lfy, sau uku yana chanza mata ruwa kafin nan ya mata wanka sarki ya saɓota a kafaɗar sa sudawo chikin ɗakin saman sofa mai zaman mutun 3 ya kwnatar da ita yaje ya ɗauko bargo ya rufe ta saboda rawan sanyi da take, komawa yayi wajen gadon gaba ɗaya ya kwashe gayan dake kan gadon, kama daga bargon bet shirt fillows gaba ɗaya ya kwashe su ya kai wajen ajiye kayan wanki ya dawo ya shiga dressing room ya ɗauko wani set na bet shirt da blanket, yazo ya shinfiɗa da kansa, ya koma ya ɗauko ta ya dawo da ita kan gadon sai kuka take, a hankali hankali idan ba ka kasa kunne sosai ba bazakaji kukan nata ba dan voice nata baya fita sosai, shiru yayi yana tunani wani kaya ya kamata ya sa mata dan bata da kaya ko set ɗaya a gidan nan basu ɗauki komai ba sai da safe daman zasuje shopping su saya musu kayan sawa, komawa chikin dressing room ɗin yayi jim kaɗan ya fito rike da jallabiyar sa a hannun, hayewa gadon yayi ya ɗagota ya zura mata jallabiyar tallaɓota yayi da kyau a kirjin sa chike da so da kauna ga wani mugun tausayin ta da ya dira masa a rai kasa kasa ya fara "my baby am so so sorry pls ki dai na kukan nan kinji idan kinayi har chikin raina nakeji pls kiyi shiru kada kanki yayi chiwo kinji? Ko kallo in da yake lamrat batayi ba ta chigaba da kukan ta mai tsuma zuchiya, dafe kai yayi yana kara dana sanin abun da ya kai kata mata, wayar sa ya ɗauko yana kokarin kiran yaya Aryan, sai ga kiran Khalid ya shigo, kwantar da lamrat yayi ya miƙe ya koma gefe dan kar Khalid ya ji kukan lamrat, picking call ɗin yayi tare manna wayar a kunnensa ya fice daga ɗakin ya koma Palo "Hello yaya Khalid" daga ɗaya ɓangaren Khalid yace "Yusuf ka fito muci Abinci mana tun ɗazun muke jiran ka "No yaya Khalid kuchi kawai ni bana jin chin abinchi gaskiya" yana gama faɗin hakan ya katse ba tare da ya jira amsar Khalid ba dan baya son ya jefo masa wata tambayar da ba zai iya amsawa ba.

layin yaya Aryan ya fara kira, kira ɗaya Aryan ya ɗaga, chikin dashewar murya yace "Yusuf kun sauka lfy? "lfy lau yaya Aryan ya karfin jiki? "Alhamdulliah" "yauwa yaya Aryan pls alluran barchi nake son yiwa Lamrat" "akan wani dalili zaka mata Alluran barchi" shiru yayi yama rasa amsar da zai bawa yaya Aryan "Yusuf kana jina koma me dalilinka kasani dai alluran barci yana da illa ba kasafai akewa mutun ba sai idan ya zama dole, ka rabu da yar mutane karka sa mata wani chuta "to yaya Aryan wani magani ya kamata na bata domin ni gaskiya bana son kai ta asibiti kasan yadda tsarin kasar nan yake basu da Addini sosai" shiru yaya Aryan yayi yana nazari kuma yana son ya gano dalilin Yusuf na neman magani dan shima bai son tambayar Yusuf ɗin tun da yaga sai wani kauche masa Yusuf ɗin yake alamar bai son asan meke damun matar tashi, amma dole dai ɗayan biyu ne ko dai ta fara period ko kuma, yau ta karɓi bakonchin Yusuf "yaya Aryan ya kayi shirune? "Yusuf matar taka ta fara period ne? "Aa yaya Aryan ba period bane fa kawai" sai kuma yayi shiru, murmushi gefen fuska yaya Aryan ya saki dan ya gano me Yusuf ke ɓoyewa "zan tura maka message ɗin drugs da ya dache ka bata" "ok kawai Yusuf yace tare da katse kiran ya koma chikin ɗaki.

Gaba É—aya sun haÉ—u a babban palon kasa domin chin abinci ban da Yusuf da Lamrat sai Bgs da baya nan shima, abinchi suke chi chikin kwanchiyar hankali chike da tausayi da tunanin me zai biyo baya Khalid ya dubi Hiyana ya fara magana "sister tashi kije ki kaiwa yaya prince abin chin sa ko" kallon Khalid yaya Ahmad yayi ya buÉ—e baki zai yi magana, cikin sauri Khalid ya É—aga masa hannu yana girgiza kai yace "bana bukatar maganar kowa wan nan umarnin Abba ne dan haka dole abi ko ana so ko baa so" jin haka yasa yaya Ahmad yayi shiru ita kuma Hiyana ta mike jiki ba kwari ta nufi kichin nasu, already jourfree mai Aikin su ya gama shirya abin chin yaya prince a chiki wani haÉ—aÉ—É—en katowar trey da kyar hiyana ta iya É—aukan trey É—in ta fito ta nufi É—akin nashi, tafiya take Kamar wadda kwai ya fashewa a chiki

Da sallama É—auke a bakin ta tashiga É—akin nashi yana kwanche saman katafaren gadon sa yana latsa waya daga shi sai short wannan haÉ—aÉ—É—iyar suran jikin nashi dake rikita mata da maza awaje lallausan bakin gashin kan nan nashi ya kwanto masa har kan fuska, kasan chewar bai É—aure ba kuma gashin na da tsawo sosai dan zai iya kai kusan tsakiyar bayan sa, É—amtsen hannun san nan kuwa kamar zasu fashe saboda karfi da samun horo mai kyau baki lallausan gashin dake kwance saman faffadar kirjin san nan kuwa sai kyalli yake, ga wani gashi mai tsantsi da taushi kwanche a chinyoyin sa har zuwa yatsun kafar sa haka ta sama ma gaba É—aya hannun sa baki lallausan gashin me mai kyau da sheki ne kwanche awajen har kan yatsun sa na hannu,

saman table dake tsakiyar ɗakin Hiyana ta ajiye trey ɗin, ta karisa Wajen gadon ta sugunna tare da sunkuyar da kai kasa, murya na rawa tace " yaya prince ina wuni" shiru bai amsa ba ko kallon in da take bai yiba latsa wayar sa kawai yake "yaya prince ga abin chin ka chan na kawo maka"shiru kamar bai san da shigowar mutun a ɗakin ba, jiki ba kwari hiyana ta miƙe ta fice daga ɗakin, tana fita wani kukan bakin chiki ne ya zo mata da gudu ta wuche ɗakin ta tafaɗa kan gado ta fara rera kukan ta, chikin kuka take faɗin "ni me nayiwa yaya prince yamin irin wan nan tsana haka sai kache ba musulmi ba ya Allah idan yaya prince ne alkhairin a gareni Allah ka kawomin mafita ta yadda zan samu kansa idan kuma shi ba alkhairi bane a gareni ya Allah ka gaggauta chiremin son sa a raina dan isar ka da karfin mulkin ka ya Allah nasan ba wan da ya isa ya bani abun da baka bani ba haka zalika ba wanda ya isa ya kwachemin abun da ka bani ya Allah ka dafamin, ya Allah kasan ina son sa ina kaunar sa tun farkon gani na da shi ya Allah ka dafawa rayuwata, kukan da yachi karfin tane yasa tayi shiru ta dai na magana ta chigaba da kukan ta mai tsuma zuchiyar mai sauraro har barchi yayi awon gaba da ita.

Yola Nigeria

A hankali Inna ta waro idon ta wani haske ne ya kashe mata ido da sauri ta runtse su

sake buÉ—ewa ido tayi a hankali, bin in da take kwance da kallo take sai wani jujjuya ido take sama, karaf idon ta ya sauka kan yaya Bello dake tsaye a Kanta ya harÉ—e hannu a kirji yana kallon ta, chike da mamaki tace "bello kai ne? Ina ne nan kuma? Waye ya kawoni? Ajiyar zuchiya yaya bello ya sauke tare da saukar da hannun sa kasa ya kariso in da take kwanche ya zauna a gefen ta burman nata ya fara magana "eh goggo habiba nine, nan kuma wajen mai magani ne, kuma ni na kawoki" yun kurawa tayi zata tashi amma ta kasa komawa tayi ta kwanta "yanzu Bello duk irin takurawa rayuwan ku da nayi bai sa kaki taimako na ba" "aa goggo habiba ki daina faÉ—in haka ko ba komai uwa É—aya uba É—aya kuke da Bappan mu kuma ni duk abun da nakeyi inayin sane dan Allah ba dan wani ba" kuka mai tsuma rai Inna ta fashe dashi chikin kuka take faÉ—in "Allah mai iko dan Allah Bello ku ya femin "goggo habiba kiyi shiru kinga yanzu kina chikin chiwo ni na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana tare" Shiru sukayi sai kuka kasa kasa Inna take, yaya Bello na rarrashin ta.

KANO

slowly zulaihat dake kwanche saman sofa ta tada kai da chinyar Aunty Amarya ta buÉ—e ido, da murna Aunty amarya ta fara faÉ—in "alhamdulliah alhamdulliah Allah mun godema ta farfaÉ—o" Ammi dake zaune a gefe guda ta taso ta nufo wajen tana faÉ—in "masha Allah" dogon tsaki Aunty amarya taja kafin tace "karki zo nan munafuka ba duk É—an ki bane yaja ai wlh da ya kashe yar mutane zai gane kurenshi" shiru Ammi tayi ta dakata da nufar tasu da take, Ummi dake zaune saman sofa mai zaman mutun 1 ta mike ta kama hannun Ammi ba tare da tayi magana ba suka fice daga É—akin sukayi part nasu.

Washegari Uk
Chapter 13 · 0% Book details