← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 80

Sashe 51

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Suna shiga chikin shopping ɗin Abdol yayi saurin ɗauko masa kujera ya zauna tsayuwa hiyana tayi kusa da shi dan ita gaba ɗaya wajen ma tsoro yake bata da ɗan tsawa Bgs yace "ki wuce kije ki ɗauki abubuwan da kike bukata mana kina ɓatamin lokaci!" Tsuke fuska tayi kafin tace "ni wlh yaya Prince tsoron wajen nake ji ba zan iya zuwa ni kaɗai ba sai dai ka rakani" a sukwane ya ɗago kai yana kallon ta lokacin guda taji numfashi ta ya tsaya dan irin kallon da ya mata tsoro take kar yace an fasa sayan komai su koma gida,kallon ficekar hiyana Abdol yayi kafin ya juyo ya kalli Bgs chikin girmamawa yace "sir let me escort her tun da tana tsoro" wani mugun kallo Bgs ya wurga masa wadda ya sanya shi juyawa ba shiri ya ɗauke kansa daga garesu ya mayar yana kallon kofar shigowa,miƙewa bgs yayi yana faɗin "wuce a mai daki gida tun da ba sayyayyar zaki yi ba" yayi maganar tare da kama hanyar fita chikin sauri ta riko hannun sa tana faɗin "dan Allah yaya Prince kayi hakuri ka rakani karkace mu koma wlh ina bukatar kayan ne" ta karisa maganar kamar zatayi kuka juyowa yayi ya kalleta kafin ya saukar da kallon sa kan hannun sa da ta riƙe ganin hakan ya sanya ta sake masa hannun sa da sauri chigaba yayi da tafiya har ya fice daga wajen,tsayuwa tayi a ranta tana faɗin "yau zan gani rashin imanin ka ya kai ka iya tafiya ka bar ni a nan ne ko kuma akoi sauran imani a zuciyar ka kuma wlh ko kasheni zakayi bazan fita shopping ɗin nan ba har sai mun yi sayayyan nan bare ma ba abun da ka isa kamin yanzu dan Ammi ta sanar dani bazaka kara buguna ba wlh yau sai nayi maganin ka sai ka sauke girman kan nan naka yau" tana tsaye tana kallon su ta chikin glass har suka tada motocin su suka fice daga shopping ɗin waro ido waje tayi tana kallon su har suka kurewa ganin ta hawaye ne ya fara gangarowa a kan kuncin ta nan take tafara na damar dama bata biyewa zuchiyar taba da ta bishi sun tafi ta hakura da sayayyar yanzu ya zatayi tayiwa mijin ta laifi yayi magana ta ki bin maganar sa wai menene ya shiga kanta wayyo Allah" chikin kuka ta sanya hannu a aljihun jallabiyar jikin ta ta chiro wayar ta ta kira layin yaya Khalid bugu ɗaya ya ɗaga chikin kuka ta sanar da shi abun da yake faruwa dariya Khalid yayi kafin yace "kiyi sauri fitowa daga wajen ki ɓuya ta inda ba wan da zai ganki ganinan zuwa dan ina da tabbacin zai aiko a ɗauke ki amma bari muyi wasa da hankalin sa kaɗan" haka ko akayi chikin sauri ta fito daga wajen kamar yadda Khalid ya umarce ta ta boye ta bayan wani hospital dake kusa da wajen, bata fi 10mins da tsayuwa a wajen ba sai ga motar yaya Khalid,kiranta yayi awaya akan ta fito su tafi da sauri ta fito har tana haɗawa da gudu ta shiga motar Khalid suka bar wajen suna tafi ba jimawa sai ga Abdol ya dawo shi kaɗai a chikin mota yazo ɗaukan ta chikin shopping ɗin ya shiga batanan tambayar mutanen wajen yayi suka sanar da shi ta fita tun ɗazun juyawa yayi ya koma wajen motar sa ya ɗauko waya ya fara kiran layin Bgs sau biyu yana kira Bgs bai ɗaga ba sai a na uku ne ya ɗaga murya har rawa yake Abdol yace "sir madam fa bata wajen ta fita ta tafi" daga tsayan ɓangaren Bgs ya ja tsaki kafin yace "to ina ruwa na ka dawo ka chigaba da aikin gaban ka" yana gama magana ya katse kiran,shiru Abdol yayi yana tunanin hali irin na ogan sa wani lokaci abun ma mamaki yake bashi mutun ne kamar ba mutun ba bazaka gane me yake so me baya so ba yanzu fa shi yache nazo na ɗauko yarinyar nan amma danache bata nan ya nuna halin ko in kula bayan kuma kallo ɗaya zaka masa kasan ya ɗauki yarinyar da mahimmanci kai Allah dai ya shiryamin oga na amma gaskiya zan so ganin ya wanna wasan nasu zai kare shida sister nan tasa Allah ya sama kar a ganta har dare muga ya zaiyi dolene ma yaje neman ta ko dan iyayen su, da wanna tunani Abdol ya shiga motar sa ya bar wajen

to masu karatu mu koma Nigeria muga me sukeyi kafin mudawo kila yaya Khalid ya dawo mana da hiyanar mu

Kano
Chapter 51 · 0% Book details