← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 80

Sashe 8

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr walid ne ya shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakin sa hanan da Nurse biyu suna biye da shi a baya, zuwa yayi ya fara mata yar gwaje gwaje sa da zaiyi yayi yar dube duben sa, san nan ya dawo da kallon sa kan su Ahzan da gaba ɗaya sun zuba masa ido suna sauraron suji me zai che "Alhadulillah yarinya dai ta samu sauki amma akoi yar matsala bazata iya yin magana ba yanzu wata kila gaba zata iya chigaba da magana sai kurinƙa sata a addu'a, shiru sukayi ba wan da ya sake magana, Dr walid ya kwashe kayan aikin sa ya nufi waje

KANO

Khalid da Yusuf ne zaune a palon Abba suna hira "amma yaya Khalid kana ganin Bgs zai so yarinyar nan kuma ya zauna da ita a matsayin mata kuwa? Murmushi Khalid yayi kafin yace "inaga duk gidan nan ba wan da ya kai Ni sanin halin Bgs, ko Aryan bai kai Ni sanin halin saba domin Aryan baya shiga abun da baa shigar da shiba ni kuma ko da Bgs bai shigar da niba in dai naga abun da bai min ba sai nayi magana shiyasa nafi Aryan shiga jikin Bgs sosai wlh kaji na rantse maka ko? Ko Bgs zai so yarinyar nan tofa inaga sai mun haɗu gaba ɗayan mu mun dangana da ɗakin gaba mu ɗauki shekara ba barchi dare mu kwana muna sallah muna masu addu'a idan ba haka ba abu mai wuyar gaske ne Bgs yaso sister shifa da mace da namiji duk ɗaya yake kallon su ba shi da wani shauki baya jin wani filling shifa bai ma san kyau ba bare muche idan yaga kyan sister zai iya ruɗe wa yace yana son ta, to bai ma san kyau ɗin ba shi idan ba kyan bindiga boom da kuma bullet ba bai san kyan komai ba, kai in ta kai che maka ma idan kaga Bgs ya ɗaga ido ya kalli sister to wlh a rashin sani ne sai kache baka ma san shiba kake min irin wan nan tambaya mutumin da ko Aryan baya ɗaga ido ya kalla ka dubi yadda suke da Aryan ɗin nan fa, kuma wlh ba wai Bgs baya son mu bane ni nasan yana matikar son mu shi yasa duk wani iskilancin da zai min bata damu na nariga da nasan haka halin sa yake ina da tabbacin idan ba mu da muke tare da shi ba sai kuma Abba da Ammi tofa ba wan da a gidan nan zai che ga kalan voice ɗin Bgs kai a gidan nan ma akoi wayan da basu taɓa jin voice nashi ba bare ma su riƙe kalar ta" dakatawa da magana Khalid yana kallon Yusuf da ya sunkuyar da kai kasa kamar mai tunani

"Yusuf tunanin me kakeyi kuma? Ɗago kai Yusuf yayi tare da sakin murnushin mugunta yana kallon Khalid "lfy kake irin wan nan murmushin haka Yusuf? "Kasan me yaya Khalid wlh idan na tuna wata rana sister zata fito ɗauke da chikin Bgs sai abun ya rinƙa bani dariya zan ga wan nan lokachin kuma wani irin iskanci zai mana shin zai chi gaba da chewa kallo ɗaya yakewa wace da namiji ne ku kuma alokachin zai fara bamban tasu" "amma gaskiya Yusuf baka da dama wlh wai daman tunanin baby Bgs da sister kake ko to sai kayi kokari ka dage da yi musu sallar dare kana rokon Allah daya sanya soyayyan da tausayi da imani a zuchiyar Bgs dukka dan wani lokaci idan Bgs yayi wani abun ni tunani nake anya yana da imani kuwa "aa yaya Khalid dolefa wata rana Bgs zai hakura ya rungumi kadda ya kama matar sa domin dai kaji me Abba yace ko mutuwa yayi bai yadda Bgs ya saki hiyana ba to kaga zama da ita ya zama masa dole" "eh hakane Yusuf kana da gaskiya zama da ita ya zama masa dole amma yanzu ta yadda sister zata juri zama da shine abun dubawa domin wlh zata sha wahala ba kaɗan ba gashi baya magana baya kallon mutane idan ka masa magana ba zai am saba idan kayi tunanin bai ji bane ka mai mai ta ya daka maka tsawa kai duk wani abun da zakayi ka burge ɗan adam idan ka yiwa Bgs hukun taka zai yi shikam babu wani abu a duniya dake burge sa inaba Gun da bullet ba mutun ne bazaka taɓa gane hagun sa ba bare dama"

"Ai yaya Khalid kai baka ma sani bane wlh gaba É—aya wajen aikin mu kama daga manya har kananun sojoji masu tasowa da zarar an ambaci sunan Bgs kowa jikin sa rawa yake Hmmm ai a gida ma yana muku sassauci sai kaje wajen aikin mu watara zaka sha mamaki dan akoi wata rana da wani soja yayi laifi yaya Aryan yace Bgs ne zai masa hukuncin wlh sojan nan yana jin anche Bgs ne zai hukunta tashi yasa bindiga ya harbi kansa ya mutu, kai bama wani ba ko ni da kai na idan misali yanzu nayi laifi a che Bgs ya hukun tani to ina mai tabbatar maka harbe kai na zanyi na mutu dan da Bgs yamin hukun chi gara na mutu na huta dan hukunchin sa ba kyau ba zai kashe ka ba amma zaka gwanmachi mutuwa idan ya fara hukun taka, kana gani gaba É—aya faÉ—in London idan aka ambaci sunan shi sai kasar ta girgiza daga manya manya masu faÉ—a aji a kasar har kananan yan siyasa mutuwar tsoron sa suke koda super market kaje chikin wasa ka amince sunan sa nan take zakaji jama'a sun nitsu ba zaka rasa masu furta kallamar shahada a chikin su bama"
"To ai Yusuf wan nan dalilin ne yasa nache maka wani lokaci idan Bgs yayi wani abun sai naga kamar bashi da imani mu dai yanzu sai dai mu dage mu taya sister da addu'a" dariya Yusuf yayi kafin yace "ba dole na taya sister da addu'a ba domin idan Allah ya dai dai ta komai É—an da zasu haifa ba karamin kyau zai yiba madara da madara ne suka haÉ—u kyau iya kyau baa magana shiyasa na yanke hukunci first born na Bgs nawane awaje na zai zauna, amma Allah yasa ya É—auki blue eyes na sister" tsaki Khalid yaja san nan yace "wlh Yusuf kai dai baka da aiki wato har ka tsara yadda É—an su zai kasan che ko to in ban da kai ma da wani zanche Ai da Bgs da sister kaman nin fuskar su É—aya basu da wani banbanci idan ba na kalar ido ba" Yusuf zai yi magana kenan idon sa ya sauka a kan Abba dake tsaye a bakin kofar Betroom nashi ya harÉ—e hannu a kirji ya zuba musu ido yana kallon su

chikin sauri Yusuf ya miƙe ya kama hanyar fita yana faɗin "my baby na kirana miƙewa Khalid ma yayi batare da ya lura da Abba ba ya bi bayan Yusuf yana faɗin "to ai nima sis love ɗina na jirana binsu da ido Abba yayi har suka fice daga Palon sauke nauyayyar ajiyar zuchiya yayi kafin ya fara magana

"Na tabka babban kuskure arayuwata nayi da na sanin haɗa Bgs da hiyana ido na ya rufe bani da burin da ya wuche in samo wa ɗana mace ta gari batare da na yi la'akari da halin da ita yarinyar zata shigaba, gaskiya da baa ɗaura Auren nan ba da ba abun da zai hanani in aura wa Ahmad ita ni da kaina na jefa rayuwar marainiyar Allah a chikin kunchi da damuwa innalillahi wa inna ilaihir rajiun Ya Allah kana gani ban yi hakan da nufin chutar da itaba ban yi hakan da nufin kun tata ma rayuwar taba,nayi hakan ne da kyakkyawar niya da kuma yakinin wata rana zai sauya ban san chewa abun nashi ya kai har haka ba daga chewa Bgs ne zai maka hukunci kawai sai ka harɓi kanka da bindiga to inaga yarinyar da aka haɗasu dole kuma anya bazan raba auren nan ba kuwa kai dole nayi magana da Aisha tun abu bai yi nisa ba musan abun yi, ya Allah ka kawo min agaji Allah ka kawowa hiyana mafita yana kai karshen maganar ya juya ya koma chikin betroom na shi

Kwanche yake a saman katafaren gadon sa yana latsa waya kiran Aunty farida che ta shigo wayar sai da wayar ta kusa tsin kewa san nan yayi picking tare da manna wayar a kunnen sa, daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tace "Hello Prince Ykk Y gida? Shiru ya ɗan yi na yan sakanni kamar ba zai yi magana ba "lfy Ykk?ya faɗa a takaice yayi maganar yana kawar da fiska gefe kamar yana gaban ta "Ina lfy dan Allah prince magana nake son yi da hiyana kuma kaga bata da waya pls ka kai mata wayar ka muyi magana" ta karisa maganar chike da fargaban abun da zai biyo baya, Aunty farida na gama magana batare da ya bata amsa ba ya katse kiran tare da yin block na number Aunty farida yayi wurgi da wayar gefe guda, wani dogon tsaki yaja tare da miƙewa ya fice daga ɗakin ya nufi part na Aryan

Kwanche saman sofa mai zaman mutun 3 ya isko Aryan ya É—ora hannun sa É—aya a saman fuskar sa dai dai sai tin ido É—ayan hannun kuma ya É—ora a kan chikin sa yayi shiru, shiru Bgs ya tsaya a bakin kofa yana kallon yadda Aryan ya rame sosai yayi baki ya sauya gaba É—aya ya fita hayyachin sa kamar ba shi ba nan take wani mugun tausayin Aryan ya dira masa a rai
Chapter 8 · 0% Book details