← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 80

Sashe 18

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Yaya khalid naje ɗakin Aunty hiyana fa ban ganta ba"chewar Zahra dake tsaye tana rike da jallabiyar da yaya khalid ya ɗauko wa hiyana a ɗakin Bgs "Auta mata da mijin ta kuma kike tambayar ina take wata kila tana wajen yaya prince" "haba yaya Khalid kasan dai bazata je wajen sa bakam" "ok to kije ɗakin nashi mana ki dubota sai mu tabbatar" da sauri Zahra ta wuche ta ajiye jallabiyar a saman sofa tana faɗin "kai aa tayi zaman ta ako ma ina take" dariya Khalid yayi kafin yace "to saiki ɗauki hijabin ki muje ai tun da kin ki zuwa ki dubo mana ina sister take su Yusuf suna jiran mu a palo" "to yaya Khalid yanzu kenan zamu tafi ba tare da Aunty hiyana ba? "Eh to mata tana wajen mijin ta zamuje muche tazo muje ne? ki kyaleta idan munje sai ki zaɓa mata kawai idan kuma da wani abun da take bukata sai mu koma gobe" " to kawai Zahra tace san nan ta ɗau hijabin ta Khalid ya riko hannun ta suka nufi waje

A babban palon kasa suka sami su Yusuf, sun gama shiri suna jiran su "ina Hiyana kuma? chewar Yaya Ahmad" "muje kawai ba zata jeba" chewar khalid, tare suka jera ba wadda ya sake magana suka fita waje, mota 5 sukayi É—aya Khalid da Zahra É—aya Fahad da amrat É—aya Yusuf da Lamrat É—ayan kuma Ahmad, shi kaÉ—ai É—ayan kuma jibga jibgan sojoji yan rakiyar sune a chiki, da gudun gaske suka bar gidan

Chike da jin kunya hiyana ta tafito daga toilet É—aure da towel É—in Bgs a kirjin ta wadda yazo mata har guiwa kamar yadda ta barshi kwanche lumshe da ido haka ta fito ta same sa, saman sofa ta koma ta zauna sai rawan sanyi take, jingina kanta tayi da jikin kujerar har barchi yayi awon gaba da ita a haka

Maiduguri Nigeria

A yaune aka sallami su Ahzan daga hospital suka koma gida ba laifi jikin yarinyar yana samun sauki sosai sai dai har yanzu bata magana sai dai kallon mutane kawai take.

Misalin karfe 4pm yarinyar na zaune a palon gidan su Ahzan tayi shiru tana kallon kasa, sanye take da doguwar riga abaya baki wadda mum Ahza ta bata, Ahzan da mum nashi suka fito daga ɗakin mum suka fito palon saman sofa ɗaya suka zauna, a nitse mum ta fara magana "bai war Allah gashi bamu san iyayen ki ba amma ina fatan zaki iya zama damu? a chikin gidan nan ko, abun mamaki sai yarinyar ta amsa da "eh zan iya" a razane Ahzan ya miƙe chike da mamaki yace "daman kin fara magana? Gyaɗa masa kai tayi alamar eh Ahzan da Mum har suna haɗa baki wajen chewa "Alhadulillah Alhamdulliah" "baiwar Allah ya sunan ki? Chewar mum shiru yarinyar tayi kamar mai tunani chan kuma ta fara girgiza kai tana faɗin "ban sani ba" kallon juna Ahza da mum sukayi wayar Ahzan ya fitar daga aljihun sa ya shiga kiran layin Dr walid, bugu ɗaya Dr walid ya ɗauka

"Hello Dr ya Aiki? Daga ɗayan ɓangaren Dr yace "lfy lau Ahzan ya mai jiki" "jiki da sauki dan ita ma na kira yanzu "ok to me ya faru? Ajiyar zuchiya Ahzan ya sauke kafin ya fara magana "Dr yarinyar nan ta fara magana amma abun mamaki mun tambayeta sunan ta tache bata sani ba shin daman ta samu matsala a kwakwalwan tane? "Aa Ahzan ba wata matsalar da kwakwalwan yarinyar nan ya samu lfy lau take kila ta shiga ruɗani ne ku barta ta kara hutawa zata dawo dai dai In Sha Allah" "to shike nan Dr nagode sai munyi waya, yana gama faɗin hakan ya katse kiran ya dawo da kalon sa kan mum, chikin nitsuwa yayi mata bayanin yadda sukayi da dr, addu'a samun lfy mum tayiwa yarinyar, amin Ahzan ya amsa da shi shiru suka zauna ba wan da ya sake che da ɗan uwan sa kala

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 11*

Maiduguri

misali karfe 1 na rana gaba É—aya gidan ba kowa sai yarinyar da Ahzan ya buge da mota, hanan ta tafi school
Mum tana wajen aikin ta a babban hospital

zaune take a palon mum Ahzan tana chin pop corn, tana kallon film a chikin makekiyar Tv dake manne a bango.

jin motsin mutun a kantane yasa ta ɗago kai, kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta dan taga alamar bai yi kama da mutanen kirki ba, shiru tayi tana tunani anya wan nan ba shine yaya deen ɗin da Aunty hanan ta taɓa bata lbr ba kuwa, dama Aunty hanan tace min ɗan iskane ashe da gaske ne kaga wani gashi kamar shekan tsuntsu.

Chike da iskilancin deen yace "ke chika yaushe kika zo gidan nan? Baa faɗamin nazo na latsaki ba irin wan nan kaya ai sai ni, wai ma wacece ke? Waya kawo ki ko dai ke yar uwar wanchan matar ne? Shiru yarinyar tayi kamar ba da ita yake ba ta chigaba da chin pop corn nata "ke chika wai ba dake nake bane!? Ko kallon in da yake batayi ba, hannu ya kai zai taɓata chikin sauri ta mike tsaye tare da yar da roban pop corn ɗin chike da izza tace "wlh idan ka kuskura ka taɓani sai na sharara maka mari! "Wow kai kaji wata voice mai shegen daɗi, gaskiya ne ke barikiji tun da kika zo gidan mu tofa taɓaki ya zama dole, idan ma zaki saki jiki gwara ki saki jiki idan kuma kinki to zaki sha wahala "kai har ka isa ka bani wahala ni bari kaji mutumin kirki ma bana tsoran sa bare mutumin banza Allah kaɗai nake tsoro" wani wawan mari ya sakar mata a kuma wadda yasa ta fasa ihu kwashe kafafunta yayi ta faɗi kasa, chikin tsawa yace "ni zaki chewa ɗan iska to wlh yau sai kin gwammachi da baki zo gidan marigayi Alhaji Abbas ba" sake dungule hannu yayi zai kai mata bugu charaf Ahzan ya rike hannun sa ta baya chike da jin haushi ya wanka wa deen wani wawan mari chikin tsawa Ahzan yace "me ya kawo ka part ɗin nan!? Chike da rashin kunya deen ya fara magana "tambaya kake ko neman sani wai shin Ahzan ko ka manta Alhaji Abbas ne ya gina gidan nan ba kai ba to idan ka manta na tuna maka kuma kamar yadda kake ɗan shi nima haka nake ɗan shi har Alhaji Abbas ya bar duniya bai taɓa yiwa wani iyaka da shiga wani part a chikin gidan nan ba kuma koda yayi ma kasan dai ni bai isa ya hanani ba" afusache Ahzan ya sake ɗaga hannu zai mari deen chikin fushi deen ya rike hannun nashi yana girgiza kai "bari kaji Ahzan ko ɗazun da ka mare ni bansan zaka kawo marin bane shisaya har ka samun daman marin nawa, yanzu lokachin ka bugeni na barka ya wuce, dan ni ba yaro bane! Kwache hannun sa Ahzan yayi chikin fushi ya fara bugun deen, damko kafar sa yayi, yayi wurgi da shi, chiro belt nashi yayi ya fara bugun deen ɗin kamar Allah ne ya aiko sa, ihu deen yake yana faɗin "mugu azzalumi kawai dan kaga kafi karfi na ko to ai baka fi karfin Allah ba, duk zaluncin da zakamin wlh tarawa nake idan ya chika sai na rama, wani naushi Ahzan ya kai wa deen a baki dan yayi shiru amma ina yaki yin shiru, gaba ɗaya Ahzan ya fasawa deen baki sai jini ke zuba, da gudu yarinyar ta miƙe ta bar palon ta nufi ɗakin hanan tana kuka.

Sosai Ahzan ya bugi deen amma duk wan nan budu daa deen yasha hakan bai sa bakin sa tayi shiru ba daga karseh hakuri kawai Ahzan yayi ya kyalesa, ya juya ya bi bayan yarinyar, deen kuwa bajewa yayi a kasa awajen ya cigaba da ihun sa yana surutai.
Chapter 18 · 0% Book details