← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 80

Sashe 47

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kwance saman katafaren gadon sa ta kasa barci duk bayan minti ɗaya sai ta duba time shiru shiru Bgs bai dawo ba tun abun baya damun ta har ta fara shiga damuwa miƙewa tayi zaune saman gadon tana tunanin ina ya tafi Allah dai ya sa lfy tun da sukazo gidan nan bai taɓa wuce 12:10am a waje ba shin me ya daɗar da shi yau, gajiya tayi da zama ta miƙe tsaye ta fara kai kawo tunawa tayi ɗazun ta kalli waya a saman table ɗin da yake ajiye ta kardu da system nashi da sauri ta nufa wajen tana addu'ar Allah ya sa akoi sim a chikin wayar,hannun ta har karma yake wajen ɗaukar wayar ta kunna haske screen ɗin,wani Cool murmushi ta saki lokacin da ta ga akoi sim a chiki already ta haddace number sa a kai chikin sauri ta shigar da number ɗin sa chikin wayar burinta kawai ta kira shi batayi tunanin me zai je ya dawo ba, sau biyu tana kiran wayar sa bai ɗaga ba sai a na uku ya ɗaga tattara nitsuwar ta tayi gaba ɗaya chikin sanyin murya tace "ina wuni yaya Prince" shiru yayi na ɗan lokacin kafin yace "me menene!? "Babu komai daman naga baka dawo bane har yanzu shine nace.... Bata kai karshen maganar ba ya daga tar da ita ta hanyar chewa "kawomin black tea ɗakin bincike" "yaya Prince ban san ɗakin ba ai"guntun tsaki yaja kafin yace "ki fito palo awajen da ake ajiye remote ki duba zakiga farin remote ki ɗauka ki sai ta sama ki dan na open stair case zai sauko sai ki haura ina wajen" yana gama faɗin hakan ya katse kiran, murmushi ta saki kafin ta ajiye wayar ta fice daga ɗakin

Kitchen ta nufa ta haɗa masa black tea kamar yadda ya buƙa ta ta dawo palo kamar yadda ya sanar da ita haka tayi, tasha ruwan mamaki lokacin da ta ga wani ɗan siririn stair case na saukowa bayan ta danna remote,mutun ba zai taɓa zaton akoi wani abu a saman nan ba wai shi stair case tsoro hawa taji dan kar ta hau ta makale amma da ta tuna yaya Prince ɗin ta na wajen sai ta samu kwarin guiwa,
Chikin zafin nama ta haye saman stair tana hawa stair case É—in ya naÉ—e kansa da kansa

wani katafaren ɗaki ne awajen mai chike da computers da na urori da ban daban gaba ɗaya ɗakin gauraye yake da hasken computers, yana tsaye gaban wata makekiyar desktop ya sanya wata na'ura a idon sa kamar glass sai aiki yake tika,tsayuwa tayi tana bin ɗakin da kallon kafin ta mai da kallon ta kansa sanye yake da yar gakeren wando wadda ta ɗame sa sosai babu riga a jikin sa da alama wandon ma dolece ta sanya ya sa dan kallo ɗaya zaka masa ka gane haka asalin kyakkyawar suran jikin sa ta bayyana gaba ɗaya hannayen sa da chinyoyin sa baki lallausan gashi ne a kwance awajen sai sheki yake kai kallon ta tayi saman ɗamtsen hannun sa daƙe murɗe dama dama wani mugun farinciki take a duk lokacin da ta kalli kyakkyawar bakin gashin dake kwance a saman faffaɗar kirjin, Cool murmushi ta saki lokacin da idon ta ya sauka a kan haɗaɗen bakin gashin kansa wadda ke baje har bayan sa kasan chewar bai ɗaure gashin ba ya sake ta har baya
duk da sanyin Ac dake É—akin hakan bai hana shi zufa ba saboda Aikin da yake tika kusa da shi tazo ta tsaya tace "sannu da Aiki yaya Prince" bai an sa ba kuma bai juyo ba aikin sa yake sosai da alama aiki ne mai muhimmanci

Tana tsaye shi kuma yana ta aikin sa almost 10mins da zuwan ta sanna ya chire na'uran dake fuskar sa ya juyo kallon É—aya ya mata ya É—auke kai kayan barcine riga da wando a jikin ta fari tas masu laushi sai É—an karamin hijabin da bai wuce kirjin ta ba ta sanya a kanta baki

ansan cup ɗin hannun ta yayi ya ɗora saman wasu takar du dake wajen chikin sanyi murya yace "wayace ki ɗauki waya har ki kirani? Banche duk wanda zaki kira sai kin sanar da ni ba!? Baya baya ta farayi tana girgiza kai tana addu'a a zuchiyar ta Allah ya sa kar ya bugeta,takowa ya farayi a hankali yana bin ta tana baya baya, "ba dake nake mana bane? Kasa magana tayi ta chigaba da yin baya tana girgiza yana bin ta kai har suka kure bango,runfa ya mata da faffaɗar kirjin sa chikin tsawa yace "bazaki bani amsa ba sai na ɓallaki"slowly ta ɗago kanta tana kallon saitin wuyar sa ta fara magana "daman naga baka dawo bane shi ya sa na kiraka amma kayi hakuri ba zan sake ba" har chikin ran sa yaji daɗin amsar ta dan duk yan uwan sa ba wanda ya taɓa damuwa ko ya kirasa awaya idan ya wuce lokacin dawowarsa ɗan garama Aryan daman shi duk abun da suke a tare suke duk kuma in da zasuje tare suke zuwa for the first time yau sister sa ta damu da bai dawo ba har ta kirasa awaya wow wanan abu yayi,afili kuwa ɗaure fuska yayi sosai chike izza yace "idan kika saƙe ɗaukan waya kika kira sai na hukun taki!" Ɗago kai tayi sosai dan ya fita tsawo sosai idan suna tsaye tana son kallon face na shi sai ta ɗaga kai sosai kwata kwata tsawon ta bazata wuche kirjin sa ba da kanta da komai

Kallon face na shi tayi kafin tace "In Sha Allah ba zan sake ba amma dan Allah idan ba zaka dawo da wuri ba ka faÉ—amin kafin ka fita" abu guda É—aya ne ke burgesa da yarinyar nan koda batayi laifi ba idan ka mata faÉ—a tana ansan laifin tace kayi hakuri bata damuwa wajen dole dole sai ta sanar da kai ba tayi laifi ba da tayi da bayayi ba zatache kayi hakuri bazata sake ba kuma tana kokarin taga ta kiyaye abun da kayi magana a kai, yana sane ba ita take faÉ—awa Ammi yana mata mugun taba amma da yace idan tasake faÉ—a sai ya bugeta duk da ba ita É—in che ta faÉ—an ba bata nuna ba ita É—in bace hasalima hakuri ta bashi ta ansa laifin da ba tayi ba

Shiru suka tsaya yana kallon face nata, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jiran taji me zai che da ita gaba
saukar hannun sa taji saman kanta zame mata É—an karamin hijabin jikin ta yayi a jefar kasa shafa gashin kanta ya shigayi tare da jawota jikin sa, jin abun tamkar mafarki Hiyana take, sun daÉ—e a haka yana shafa gashin kanta kafin ya zame hannun sa daga kan nata ya É—ago habar ta suna kallon juna matso da face nashi yayi dai dai nata chikin sauri ta runtse ido kirjin ta na dukan uku uku kasa kasa yace "ki shirya gobe zan sanya a kira muku masu gyaran gashi" yana kai karshen maganar ya sake ta tare da juyawa ya koma wajen aikin sa ya É—aukk tea É—in da ta kawo masa ya koma saman sofa dake a É—akin ya zauna,ya fara sha chikin nitsuwa

Juyawa tayi zata fita sai ta tuna da massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa idan ya saura kamar kwana biyu alluran ya sake sa kirin ƙa yawan zama kusa da shi kina yawan yimasa magana ko da ba zai amsa ba domin awan nan lokacin duk karfin alluran ya ragu yana gab da karewa ne gaba ɗaya alokacin zai ɗan fara jin feeling kaɗan kaɗan,tuna hakan ya sanya ta koma wajen sofan da yake zaune ta na kokarin tsugunnawa kasa ya nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauƙe kafin ta zauna kusa da shi tana satar kallon sa ta kasan ido, kaɗan ya sha tea ɗin ya ajiye ya miƙe ya koma bakin aikin da yake yana miƙewa ta kwanta a wajen dan daman ta fara jin barci tana kwanchiya ba jimawa barci yayi awon gaba da ita

2am ya kammala aikin da yake gaba ɗaya ya kashe duk wani kayan wuta dake ɗakin nan take duhu ya gauraye ɗakin haske wayar sa ya kunna kasa kasa yace "tashi muje" shiru bata amsa shi ba tsaki yaja kafin ya nufi wajen da take kwance hannu ɗaya ya sanya ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗa ya nufi hanyar fita da ita sai da ya kai tsakiyar ɗakin ya danna remote stair case ɗin tayi kasa ya sauka yana sauka stair ta koma kai tsaye bedroom ya wuce,saman katafaren gadon sa ya shin fiɗe ta ya wuche ya nufi toilet wanka yayi chikin sauri yayi shirin barci dan dare yayi sosai, saman gado ya dawo ya haye tana kwance yadda ya kwantar da ita gefe ya kwanta ya karanto addu'oe in barci ya shafa sannan ya lunshe ido

Kamar jira take yana lumshe ido yana lumshe wa ta mirgino ta faɗo jikin sa slowly ya waro green eyes na shin karaf sai saman face nata, zuba mata ido yayi yana kallon ta barcin ta take chikin kwanchiyar hankali yauche rana ta farko da ya karewa face nata kallon, shafa nashi face ɗin yayi kafin yace "haka ne fa kamannin mu ɗaya da yarinyar nan" dawo da kallon sa yayi saman ɗan karamin bakin ta ya zuba mata ido zuchiyar sa na ingizashi akan ya sunbacheta ɗayan ɓangaren na zuchiyar sa yace "idan ka sunbace ta ka sunbaci wa keman?" da sauri ɗayan ɓangaren yace "ka sunbaci sister ka kuma zaka iyayin komai da ita a matsayin ta na sister ka, kawai ka ɗauke ta a matsayin abun rage kewar ka,shiru yayi sai tunaninnuka daban daban yake a zuchiyar sa amma ya rasa wanne ɗaya sai kama ji yayi ba zai iya jure kallon lallausan lips nata ba batare da ya sumbata ba
Chapter 47 · 0% Book details