← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 80

Sashe 50

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

saman table ta ajiye masa trey mai ɗauke da kayan breakfast ɗin,tana kokarin zama saman sofa sai ta tuna massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa ta rinƙa taya bgs sanya kaya da sauri ta fasa zamar ta miƙe ta karisa wajen sa dai dai lokacin yana sanya buttin ɗin rigar, ba tare da tayi magana ba ta sanya hannu chike da tsoro kirjin ta na dukan uku uku ta fara tayashi sanya wa, kasa kasa yake satar kallon ta mamaki ne ya kama shi wato yarinyar nan ta dai na tsoron sa kenan,amma duk da hakan ya ji daɗi sosai har chikin zuciyar sa da ta taya shi sanya buttin ɗin afili kuwa ɗaure fuska yayi chikin tsawa yace "ke me haka!? Chikin sauri ta chire hannun ta daga saman rigar nashi da cool voice tace "kayi hakuri ba zan sake ba" ko kallon ta bai sake ba ya chi gaba da sanya buttin ɗin sa bayan ya kammala ne ya wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna da sauri ta karisa wajen ta fara sarving na shi sai da ta gama komai ta tura masa gaban sa sanna ta tsugunna chikin girmamawa tace "yaya Prince dan Allah ka kiramin Aunty farida" da hannu ya mata nuni da wayar sa dake saman bedside drawer ba tare da yayi magana ba miƙewa tayi ta ɗauko wayar ta dawo ta miƙa masa tare da ɗan tsayawa daga gefe layin Aunty farida ya kira wayar na fara ringing ya miƙa mata

Ansar wayar tayi ta nufi kofar fita dan ta koma palo bata son yaji me zatace tsawa ya daga mata wadda ya sanya ta juyowa ba shiri "in zaki je!? "Palo zanje" ta bashi amsa chikin tsoro batare da ya kalli in da take ba ya mata nuni da hannun sa akan ta wuce wajen hutawar sa tayi wayar achan,ba musu ta wuce ta nufi wajen already Aunty farida tayi picking call É—in tun ringing na farko duk abun da ya faru a kunnen ta ya faru tana jin su, zaman saman sofan dake wajen hiyana tayi kafin ta manna wayar a kunnen ta ta fara magana

"Hello Aunty farida in kwana" "my Hiyana kina ji yanzu ba gaisuwa zamuyi ba kin ga wayar sa ne kuma lokacin tafiyar sa wajen Aiki yayi kawai muyi abun da ke gaban mu yanzu wani chi gaba aka samu"shiru hiyana tayi tana ɗan muku muku bazata iya faɗaqa Aunty farida chewar Bgs yayi kissed nata ba,jin tayi shirune ya sanya Aunty farida tace "my hiyana karki ɓoyemin komai ki faɗa min da wuri kinga bamu da time ko, sunkuyar da kanta kasa kayi tamkar Aunty farida na gaban ta chike da jin kunya ta fara bata lbr duk abun da ya faru tsakanin ta da bgs,murna sosai Aunty farida tayi kafin tace "yanzu bari na faɗa miki kayan da ya dace kirin ka bashi da lokacin da suka dace idan ya dawo aiki kinga yana bukatar ya huta ya sha iska to wannan lokaci kananan kaya zaki fitar masa dan su yake buƙata idan ya shiga wanka da daddare kiyi sauri fitar masa da kayan barci masu laushi kuma Prince ya fison abu fari komai nashi farine yana son kalan fari sosai sai ki kula da wanna ma idan da safene to kayan Aiki zaki fitar masa idan kuma ranar weekend ne to ki karanche sa shin yana fita weekend ne idan yana fita to kaya masu kyau da tsada zaki fitar masa irin jeans da t-shirt ba manyan kaya ba aikema ranar kinyi wauta Prince baya sanya kayan hausawa idan ba dole ba, abu na gaba idan kuma baya fita weekend to jallabiya zaki fitar masa sanan ki rinƙa rigasa tashi sallar asuba dan idan ya shiga wanka ki fiddo masa da jallabiya da zai sanye yaje masallaci,yanzu dai sai mu bari haka sai anjima zan kira ku ta wayar Auta akoi wani shirin da zamuyi kuma ki dage akan shawarar Khalid da Aryan yanzu ki mai da masa da wayar sa dan naga lokacin ya tafi zaije wajen aikin sa kar kije kiyi laifi rike masa waya da kikayi" miƙewa tsaye tayi kafin tace "to Aunty farida na gode sosai" "ba sai kin min godiya ba ke dai ki chigaba da yin abun da na faɗa miki In Sha Allah mun kusa nasara" a chikin zuchiya ta amsa da amin tare da chiro wayar daga kunnenta bata iya komai a wayar san nan ba dan haka bata katse kiran ba ta mai da masa da wayar yana zaume saman sofa kamar yadda ta bashi haka ta dawo ta same sa kusa da shi ta zauna tare da miƙa masa wayar tana faɗin "gashi yaya Prince Nagode" an sar wayar yayi tare da miƙewa ya fice daga ɗakin,bin bayar sa da kallo tayi har ya fice, tana kokarin miƙewa sai gashi ya dawo ɗakin a tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da miƙa mata hannu sa alamar tazo ta ansa miƙewa tayi chikin sauri ta kariso wajen sa sim card nata ya miƙa mata tare da faɗin "now zaki iya kiran kowa sister ki ta dawo dai dai" yana kai karshen maganar ya juya chikin sauri tace "yaya Prince to dan Allah kasamin kati awayar" ba tare da ya juyo ba yace "akoi card a chiki" "to yaya Prince dan Allah ina neman wata alfarma ma" sai lokacin ya juyo yana kallon ta tare da dakatawa da tafiyar da yake takowa tayi a hankali tazo kusa da shi chikin sanyi murya tace "yaya Prince ina son abubuwa da ɗan dama ina son perfume ina son kayan sawa ina son...sai kuma tayi shiru ta fasa faɗe, kallon ta yayi from head to toe kafin yace "wayace ki sanya min perfume na? Waro ido waje tayi tana nadamar tambayar sa da tayi yanzu gashi ta tonawa kanta asiri, harara ya wurga mata kafin ya sake chewa "ki shirya muje" yana kai karshen ya juya "yaya Prince bani da kayan masu hankali a chikin akwatin wanda zan sanya na fita" "ki sanya jallabiya ta" ya kai karshen maganar tare da ficewa tsalle ta buga tana dariya da sauri ta wuche dressing room nashi ta ɗauko jallabiyar sa ta sanya jallabiyar ya fi karfin ta har jaa yake a kasa sosai itakam bata damu da yawan da jallabiyar ya mata ba sai murna take ta fito daga ɗakin baya palo dan haka sai ta wuche ta nufi harabar gidan

Yana zaune chikin motar sa sunyi reading tafiya da alama ita suke jira tsayuwa tayi ta rasa wani mota zata shiga chikin sauri Abdol ya buÉ—e motar ya fito ya buÉ—e mata gidan baya in da Bgs ke zaune,satar kallon sa tayi ta kasan ido taga ko ya kalli abun da Abdol yayi kuwa ganin ko kallon in da suke bai yi bane hankali sa na kan system dake saman chinyar sa, hakan ya sanya ta tako jiki ba kwari ta shiga kusa da shi ta zauna tana jiran taji me zai che rufe motar Abdol yayi ya buÉ—e gidan gaba ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar da matsanancin gudu suka bar gidan

wani katafaren shopping mall suka shiga bayan sunyi parking Abdol ya fito ya buɗewa Bgs ɓangaren sa sanan ya buɗe wa hiyana,kusan a tare suka fito sai kallon wajen take tana satar kallon sa gaba yayi ta bi bayan sa Abdol ya rufa musu baya tun kafin su shiga chikin wajen ya sanya face mark a face na shi
Chapter 50 · 0% Book details