← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 80

Sashe 41

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa oga zaune yake yana waya da Aryan
"Ykk Aryan? ya jikin su Aunty Amarya? Daga ɗayan bangaren Aryan yace "Suna lfy nakira na sanar da kai ne zan wuce yola yanzu" shiru Bgs ya ɗan yi kafin yace "aa ba yau ba kuma ba gobe ba zanyi bincike a kai kafin na baka izinin zuwa yanzu dai ka chigaba da bata magani da wanchan wawan ke bata,kafin na tattara bayanai" "amma Bgs kasan fa wannan maganin idan yayi yawa zai ja mata wata matsalar ko" "Aryan baka da zaɓi just kayi abun da nache kawai" yana gama faɗin hakan ya katse kiran dai dai lokacin da hiyana ta kariso wajen hannun ta ɗauke da try abinci

Saman table ta aji masa abincin ta É—au plate ta fara serving nashi bayan ta cammala komai ta ajiye masa saman table É—in ta matso masa da table É—in gabansa,tsugunnawa tayi a gaban na sa daga É—an gefe chikin raunanniyar murana tace "yaya Prince dan Allah ka kiramin Ammi inason in tambayeta an gane diyana ne,wayar da yaya Khalid ya sai min card É—in ciki ya kare" shiru yayi bai yi magana ba sai ma É—aukan spoon da yayi ya fara chikin abinci sa,

shiru shiru bai yi magana ba ita kuma tana tsugunne a gaban sa ko kallon in da take bai yi ba har ya kusa kammala chin abin chin chike da kunan rai ta miƙe da gudu ta bar wajen tana hawaye,ko kallon ta bayyi ba ya chigaba da chin abincin sa

Saman katafaren gadon sa ta faɗa tare da sakin wani marayar kuka, tana zanchen zuci wai yaushe ne yaya Prince zai chanza a rayuwar sa mutun kamar ba mutun ba baka taɓa gane me yake so me baya so, yana bala'i son su yaya Fahad amma har yanzu ya kasa gane kamar yadda yake son yan uwan sa kowama haka yake son nashi, wlh ina da tabbacin na fishi kaunar yan uwana sune duniyata sune komai nawa wai ni yaushe ne bakin ciki zai kare a rayuwa ta, ya Allah kamin zaɓi mafi alkhari kamin zaɓin da ya dace da ni, ya Allah ka karemin yar uwata a duk in da take a faɗin duniyar nan, tabbas ina ji a jikina diyana na raye sai dai aduk lokacin da na tuna tana raye nakanji gabana na faɗuwa ya Allah kasa ba chikin wata musibar ta faɗa ba,

Sai da tayi kukan ta mai isarta sannan ta miƙe ta nufi toilet ta wanke fuskar ta tayi wanka ta fito ta sake shiryawa chikin wata shegiyar doguwar riga mai bala'i kyau rigar ta kamata sosai rigar bata da hannu launin pink color an mata kwalliya da wasu duwatsu farare masu kwalli daga guiwar rigar har zuwa kasa an tsaga ta ta gaba

gaban mirrow taje ta tsaya tana kallon kanta tsaki taja ganin yadda ta zama kamar wata karuwa ji take kamar taje ta damko Zahra ta mata shegen duka hannun ta na kerma ta ɗauki wani perfume dake wajen ta ɗan sanya a jikin ta kaɗan wai dan karya ji kamshin ya gane, drawer wajen mirrow ta buɗe tana yar dube dube hannun ta sai kerma yake alamar tsoro, wani kyakkyawar hoto ta chikaro da shi awajen jikin ta har bari yake wajen saurin ɗauko hoton sai tagama ashe hotunan biyu ne ba ɗaya ba, tasha ruwan mamaki lokacin da idon ta ya sauka kan face ɗin matar dake chikin hoton matar kamannin su ɗaya da hiyanar kamar an tsaga kara matar na tsaye a kasar wata katuwar bishiyar kuka tana riƙe da kwaryar nono, jikin ta sanye da kayan fulani riga zuwa chibiya da sani an mata manya manyan kitso guda biyu wadda gashin nata ya zubo har kan chibiya bakin kirin sai sheki yake kwata kwata matar bazata wuche 17 years ba, sosai hiyana ta kurawa matar ido tana son sanin wacece wanan mai mugun kama da ita haka,shiru tayi tana tunani to ko dai Ammi ce lokachin da take yanmata dan tasan idan ba Ammi ba ba wacce yaya Prince zai ajiye hoton ta awajen sa ganin tunani da take ba zata samu amsa ba yasanya ta ajiye hoton ta ɗauko ɗayan, ba karamin mamaki ta shigaba lokacin da idon ta ya sauka kan ɗayar hoton, gaba ɗaya Family su Ammi ne awajen tabbas hiyana ta san wasu daga chiki musamman Innar ta dake tsaye kusa da Ammi a lokacin kurawa tsohon da ke tsakiyar su ido tayi tana kallon sa yana ɗauke da yar yarinyar da baza ta wuchi shekara 2 ba murnushi hiyana tayi lokacin da ta gano chewa itace kan kafar tsohon nan domin tana da hoton ta tana karama dawo da kallon ta tayi kan tsohon ta zuba masa ido, na ɗan lokacin kafin ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, bata san lokacin da hawaye ya fara bin kuncin taba lokacin da idon ta ya sauka kan fuskar bappa dake tsaye yana ta murmushi, kallon sa take kamar ta kira shi ya amsa jin motsi takun Bgs ne ya sanya tayi sauri mayar da hoton ta goge hawayen ta chikin sauri ta juya zata barwajen dai dai lokacin shi kuma ya shigo kallo ɗaya ya mata ya kawar da kai gefe,ya wuche chikin ɗakin da sauri itama ta wuce ta ɗauki hijabin ta, ba tare da ta ɗaure gashin taba ta sanya hijabin ta wuche ta nufi wajen hutawar dan ta kwashe kayan abincin da yaci

Bayan ta kwashe kayan abincin ta mayar kitchen ne ta dawo ta gyara wajen tana gamawa ta dawo chikin betroom ɗin tana kokarin wuchewa palo sexy Voice nashi ya daki dodan kunnen ta "come here" chikin sauri ta juyo ta nufoshi yana kwanche saman gado, tana kokarin tsugunnawa a kasa yayi saurin nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, in da ya nuna mata ta zauna miƙewa yayi zaune shima suna fuskantar juna

Chikin sanyin murya ya fara magana "already an gane yar uwar ki tana gida" ai hiyana bata san lokacin da ta miƙe ta rungume sa tana dariya ba tana faɗin "wayyo Allah na Alhamdulila Alhamdulila" shiru yayi abun ma mamaki ya bashi sai da tayi dariyar ta mai isar ta sanna ta ɗago kai kallon face nashi ba karamin tsoratata yayi ba bashiri ta sake sa ta koma ta zauna a gefe ta nitsu ta manta ɗazun fa mafarki take yanzu kuma gaskiya ne, kara ɗaure fuska yayi sosai chikin izza ya fara magana "idan kika sake min irin haukar nan sai na ɓallaki ki nitsu kiji abun da zan che miki first menene sunan ki? Nitsu ta karayi chikin sanyin murya tace "hiyana"ɗan sakin fuskar sa yayi kaɗan kafin yace "what about your sisters Name" "diyana itace mai bina sai lamrat mai bi mata sai amrat auta" shiru yayi ɗan yi kafin yace "What about Your mother? Narai marai tayi da ido tana kokarin kuka,hannu ya ɗaga mata alamar kar ta kuskura ta fara masa kuka a nan ba tare da yayi magana "wacece maman ki yar ina ce? kuma aina take yanzu?chikin dakiyar zuchiya ta fara magana "ta rasu tun ina yarinya amma bayan rasuwar ta da jimawa bappa ya bamu lbr ta kuma yace zai ajiye mana wani sako ko bayan ranshi idan muka girma mu binciki ɗakin sa zamu samu sakon akan innar mu sakon yake tafiya"
"Ok mahaifiyar ta ku yar ina ce? "Bappan mu yace mana ita yar sudan ce" shiru yayi kafin yace zaki iya tuna a sudan a wani gari? Girgiza masa kai tayi kafin tace "aa bai faÉ—a mana awani waje bane mu dai yace mana ita yar sudan ce" "tana da yan uwa a nan Nigeria ne?shiru hiyana ta É—an yi kamar mai tunani chan kuma ta girgiza kai tana faÉ—in "aa bata da kowa" shiru yayi bai sake magana ba sai chiro wayar sa da yayi ya fara kiran Aryan video call, bugu É—aya Aryan ya É—aga

Wani Cool murmushi Aryan ya saki lokacin da idon sa yayi masa tozali da hiyana zaune gefen Bgs yana son ya yi magana akan hakan amma yasan halin Bgs yanzu yana magana zai iya korin ta awajen

"Aryan ina yarinyar nan take? Chewar Bgs
da gangan Aryan yace "wace yarinya kuma" yana magana ya guntse dariya so yake ya É—an kure Bgs,dogon tsaki Bgs yaja tare da wurga ma sa harara ta chikin wayar "zaka bata wayane ko ko" harara wasa shima Aryan ya wurga masa kafin yace "2dys ba muyi bane shi ya sanya yau nake maka tsiyar" ya kai karshen maganar tare da komawa kusa da diyana dake kwance saman gado tana barchin wahala,mikawa hiyana wayar Bgs yayi hannun ta har kerma yake ta ansa tamkar diyana na jin ta haka tafara surutai

"diyana ina kika shiga kinsan tashin hankali da na shiga bayan tafiyar ki kuwa? dan Allah ki tashi daga barchin nan ko zan samu naji daɗi a rayuwata alhadulillah Allah mai kyauta mai kari ko iya ganin ki kawai danayi ya kawarmin da duk wani tashin hankali da damuwa dana ke chiki, dan Allah diyana ki tashi kimin magana kinji buɗɗon bappa kin tuna sunan ko" tana magana tana kuka hawaye sharɓa sharɓa, shi kanshi Aryan kawar da fuskar sa yayi daga gaban Cameran dan idon sa sun cika da kwalla lokacin guda Bgs yaji mugun tausayin yaran ya kama shi ashe ba shi kaɗai yake son yan uwan sa kaman ran saba Allah sarki marayun Allah first time a rayuwar sa da yaji zai iya tsayawa mace zai iya share mata hawaye.
Chapter 41 · 0% Book details