← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 80

Sashe 14

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanche Lamrat take kan gado ta tada kai da chinyar yaya Yusuf sai kuka take,
Da kyar yaya Yusuf ya iya shawo kan ta ta dai na kuka kwata kwata taki chin abinci ita dai dole ya mai data wajen Ammin ta tun da kasheta yake sonyi, "my baby kiyi hakuri na miki alkawari ba zan sake miki hakan da zafi ba" waro ido waje Lamrat tayi chike da jin haushi tace "au daman yaya Yusuf zaka sake yimin hakan kenan? "My baby dole na sake yi maki mana idan ban miki ba taya zamuyi mu samu baby's" "nifa yaya Yusuf bana son baby's ɗin na hakura kawai ka mai dani wajen Ammi na" "haba my baby idan na mai daki wajen Ammi ni kuma fa dawaye zan zauna kenan? "Ka zauna kai kaɗai mana ai daman kai kaɗai kake zaune ba da ni ba "to shike nan tun da haka kika che yanzu dai zan mai daki wajen Ammi ni kuma sai na samo wata baby na Aura ta aifamin baby's masu kyau" kuka mai karfi Lamrat ta fashe dashi a razane yaya Yusuf yace "my baby lfy kukan me kuma kike "ni yaya Yusuf ka kaini wajen Aunty hiyana ta wlh ni yanzu bana son ka tun da dai wata mata zaka aura" dariya mai karfine ya kwache masa, dariya yake sosai har da rike chiki, ganin yana mata dariya ne yasa ta kara sautin kukan ta sosai, ba shiri ya dakata da dariyan da yake "sorry my baby tuba nake ni ai ke kaɗai kin ishe ni ba ruwa na da wata mace ni kam wasa nake" "ni dai yaya Yusuf ka kaini wajen Aunty hiyana tun jiya fa ban ganta ba"tana magana tana shesshekar kuka "to kiyi shiru idan kina son zuwa wajen su nima yanzu zanje na shirya na je wajen aiki sai karfe 2 na rana zamu dawo sai mu kai ku wajen shopping dan ku zabi kayan da kuke bukata" "to nayi shiru ka kai Ni" mikewa yayi batare da ya sake magana ba ya kwantar da kanta a saman gadon ya sauko kasa ya shiga dressing room jim kaɗan ya fito hannun sa ɗauke da jallabiya baki ya dawo kan gadon ɗagota yayi ya zura mata jallabiyar san nan ya miƙe ya ɗauke ta chak ya nufi waje da ita, a babban palon kasa ya samu su Zahra gaba ɗayan su suna zaune suna hira hiyana ce kaɗai bata wajen, saman sofa mai zaman mutun 3 ya direta chike da jin kunya lamrat ta fara gai da Zahra, shi ko juyawa yayi chikin sauri Zahra na gai da shima bai bi ta kan taba ya haye sama.

Da sallam hiyana ta shiga betroom ɗin Bgs sanye take chikin doguwar hijabi har kasa fari tas, hannun ta ɗauke da katon trey mai ɗauke da kayan breakfast nashi, tsaye yake gaban mirrow sanye da uniform na sojoji yana kokarin ɗaure gashin kansa ta baya, kasa kasa hiyana ke satar kallon sa ba karamin kyau kayan suka masa ba kamar dan shi akayi su, sai wani fitinannen kamshin da yake zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikin sa, sosai take shakar kamshin turaren nashi

table ɗin tsakiyar ɗakin ta nufa da niyyar ajiye masa abincin, turus ta tsaya ganin abincin da ta kawo masa jiya da daddare ma ko taɓawa bai yi ba, shiru ta tsaya tana tunani shin na ajiye masa breakfast ɗin ko zai chi ne ko kuma dai na haɗa har da na jiyan na mayar kitchen tun da ba zai chi ba, tayi nisa chikin tunanin da take, sai ganinshi tayi ya wucheta ya nufi kofar fita, chikin sauri ta tsugun na kasa murya na rawa tace "ina kwana yaya prince" ko kallon in da take bai yiba ya fice daga ɗakin, shiru tayi ta kasa miƙewa dan ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya mutu, yanzu ya zatayi da abincin nan, da ƙyar ta miƙe ta fice daga ɗakin ta mai da breakfast ɗin kitchen san nan ta dawo ta ɗauki na jiyan ma ta mai da kitchen chike da ɓachin rai ta koma ɗaki ta kwanta

Misali karfe 2pm gaba ɗayan su suna zaune a palon kasa suna hira wayar Zahra dake hannun Lamrat ya fara ringing, chikin sauri Lamrat ta miƙawa Zahra wayar, ansa Zahra tayi ganin sunan Aunty farida ne ya bayyana a kan screen ɗin yasa ta yin picking da sauri ta sanya wayar a hand-free dan su hiyana su gaisa da ita gaba ɗaya, daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tace "Auta ykk? Ya Uk? "Aunty farida muna lfy ya junior? "Junior yana lfy ina Hiyana? "Gatanan Zahra tayi maganar tana miƙawa hiyana wayar, chikin sanyin murya hiyana ta fara magana

"Aunty farida ina wuni" "lfy lau my Hiyana ykk y mijinki? "Muna lfy ya junior" "yanzu dai bar zanchen wani junior mu fiskanchi abun dake gaban mu, kinga yanzu mijin ki yayi blocked ɗina, waro ido waje Hiyana tayi "yau Aunty farida ke da kanki yaya prince yayi blocked? "Eh my Hiyana nima na sha ruwan mamaki amma wan nan duk bashine matsalar ba kinaji kyalesa idan ya huche zai buɗe Ni, yanzu dai kina yin abubuwan da na tsara miki ne? ko kuma dai kin chigaba da zama shiru shiru "Aa Aunty farida inayi jiya ma na kai masa abinchi yau ma kuma na kai masa" "good my Hiyana abu na gaba da zan faɗa miki ya kamata ki rage tsoronsa kuma na faɗa miki ki daina sanya manya manyan hijaban nan da kike sanya wan kina jina ko? Zan sanya yaya Khalid ya sai muku waya gaba ɗayan ku dan mu rinƙa waya sosai kinji ko? Hiyana zatayi magana sukaji diran motochi su Bgs a chikin gidan alamun sun dawo daga wajen Aiki, chikin ruɗu hiyana tace "Aunty farida gasu yaya prince sun dawo aikin" "good my hiyana yanzu yana shigowa ki bishi ɗaki nasan yana shiga ɗaki zai zauna saman sofa yaɗan huta to yana shiga ki bishi ki chire masa takalmi da socks kinji? Shiru Hiyana tayi tana tunanin ta yarda zata fara tunkaran Bgs har ta chire masa shoe "my Hiyana kimin alkawarin zaki min hakan kinji? "Aunty farida na miki alkawari zanyi tana magana wasu zafafan hawaye na bin kunchin ta, hannu Zahra tasa tana gege mata hawaye chike da tausayin ta, katse kiran tayi ta ajiye wayar a gefe ta rike hannun Zahra tanan kokarin fara magana kenan, sukaji takun tafiyar su Bgs nan take suka nitsu ɓoye fuska hiyana tayi chikin chinyoyin ta dan hawayen nata sunki tsayuwa kuma bata son su yaya Yusuf suga tana kuka.

Bgs ne a gaba ya shigo kafin Zahra ta ɗaga masa gaisuwa ma ya haye sama abun sa, miƙewa Hiyana tayi chikin sauri ta bi bayan sa, a tare su Khalid suka shigo gaba ɗayan su suka baje a palon kowa ya zauna kusa da matar sa, chike da so da kauna suke gaisawa da juna "ke Amrat tashi kije ɗaki ki ɗauko min laptop di na" chewar yaya Fahad, da gudu Amrat ta miƙe ta haye sama

A ɓangaren hiyana kuwa

Tana zuwa bakin kofar É—akin yaya prince ta tsaya ta goge hawayen ta, san nan ta shiga É—akin da sallama yana zaune saman sofa mai zaman mutun 2 ya É—an jingina da jikin sofan ya lumshe ido, a nitse ta tako zuwa gaban sa jikin ta har rawa yake, ta sungunna, ta kai hannunta kan takalmin sa, da kyar ta ita sai ta hannun ta ya dai na rawa, igiyar ta kalman tafara kwanchewa, da kyar ta iya É—an É—aga kafar tasa ta zame ta kalmin haka ta zame É—ayar ma, É—an É—aga kafar wandon nasa sama tayi ta kama bakin safar kafar tasa ta zame ta a hankali, zubawa kafar tasa ido tayi, ba karamin kyau dogayen yatsun kafan sa suka mata ba, ga wani bakin lallausan gashi a kwanche a kan yatsun, farchen (kunba) kafar sa farare tas sai kyalli suke bata san lokachin da ta kai hannun sa saman yatsun nashi ta shafuso su ba wani gigitachen mari ya sakar mata a kumatu wadda yasa ta mikewa tsaye ba shiri tare da fasa wani razanannen ihu chikin tsawa yace "get out" a guje ta fice daga É—akin ta nufi nata

Tana shiga ɗakin ta ta chire hijabin jikin ta, ta sanya karfi ta yagashi gida uku chikin sauri ta ɗauko face Mark ta sanya a fuskar ta ɗaukan hijabin nata tayi ta taka saman gadon ta ta ɗaura hijabin a jikin Ac tanayi tana kuka mai suma rai, daure hijabin nata tayi sosai chikin kuka tace "banga anfanin rayuwata ba wlh Bappa ya rasu Inna ta rasu diyana ta ɓata yaya prince da yake matsayin mijina ya tsane ni to me kuma ya ragemin sosai ta gyara face Mark dake fuskantar ta yadda zatayi saurin mutuwa kar numfashi ta ya fita ɗaure wuyar ta tayi da kyau san nan ta sauka daga kan gadon kafar ta na lilo a tsakiya sai karkarwa take ta zaro blue eyes nata waje sosai saboda shake wuyar ta da hijabin yayi,

Amrat na fitowa daga ɗakin su rike da laptop ɗin yaya Fahad, daga ɗakin hiyana taji wani irin numfashi da take da sauri ta nufi ɗakin tana nura kofa taga hiyana na kokarin mutuwa dan gaba ɗaya har jikin ta ya fara saki, wani razanannen ihu Amrat ta saki wadda ya dira a dodon kunnen kowa dake gida, gaba ɗaya su Khalid suka miƙe a tare suka hauro dai dai lokacin Bgs ma ya fito daga ɗakin sa dan jin irin ihu da Amrat ta saki, kusan tare suka shiga ɗakin Hiyana.
Chapter 14 · 0% Book details