← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 80

Sashe 44

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

____da sauri hiyana ta koma palo ta ɗauko wayar ta lokacin da ta dawo ɗakin zaune a bakin gado ta same sa gaba ɗayan kunyar sa take ji yanzu gaban shi tazo ta tsugunna tare da miƙa masa watar tana faɗin "yaya Prince gata" batare da ya kalleta ba yace "sim ɗin zaki chire ki bani" zaro ido waje tayi sai yanzu ta fahimci me yake son yi wato bayaso tayi waya dasu diyana ko,shiru tayi ta kasa ko da motsi dan gaskiya tun da diyana ta dawo bazata iya kwana ɗaya basuyi waya ba,ita yanzu ya zatayi, ganin tayi shiru bata chire sim ɗin bane ya sanya ya ɗago kai ya kalle ta yayi niyar yi mata tsawa amma sai ya fasa saboda tausayin ta dayaji musamman daya ga face nata yadda ya sauya lokacin guda kasa kasa da sanyin murya yace "chiro sim ɗin ki bani idan kina son magana da su sai ki kirasu ta wayata"sunkuyar da kanta tayi kasa kafin tace "dan Allah yaya Prince kayi hakuri ka barmin kaga kai wani lokaci baka dawowa da wuri kuma kullun da rana muna waya da Aunty farida da Ammi" kawar da kansa yayi daga kallon ta ya ɗaure fuska sosai ya fara magana "ba dan su Aunty farida zan ansa sim naki ba nasan ko nace karki kira yar uwar ki sai kin kirata kuma idan kikayi haka ba ke kaɗai ba kuna gefa Aryan chikin tashin hankali da damuwa sister ki bata da lfy idan taji Voice naki tana kara birkichewa Aryan kema nan ki zauna kiyi ta kuka mara amfani addu'a zaki mata dan haka bani sim ɗin,duk lokacin da kike son magana da su Aunty farida ki furta afili kina son yin magana da su duk in da nake zan jiki ko nayi ni sa zan sanya a haɗaki da su" jikin ta har bari yake wajen chire sim ɗin kamar zatayi kuka haka ta chiro ta miƙa masa chikin sanyi murya tace "to yaya Prince ina son ganin Aunty farida da Ammi wlh ina kewar fuskar su" shiru ya ɗan yi kafin ya mata nuni da hannun sa akan ta zaun na gefen sa a saman gadon ba tare da yayi magana ba,chikin sauri ta koma saman gadon ta zauna kusa da shi

remote ya ɗauko daga bedside drawer ya kunna makekiyar Tv dake chikin ɗaki tana sai tin gadon sa, Cameras da ban da ban ne a jikin Tv tafiya yake kai tsaye ya shiga Cameran gida zai wuce idon sa ya sauka kan wata tsohuwar Camera na ɗakin da Ahmad ya kwanta rashin lfy bai san ma ta ya akayi ta shiga Cameran ba, tsaki yaja yana kokarin fita dai dai idon sa ya sauka lokacin da hiyana ta fara yiwa Ahmad addu'a da tsawar da taji da duk wani abu da ya faru a ɗakin, dakatawa yayi ya fasa fita ya chigaba da kallon ita kan ta hiyana waro ido waje tayi ta chigaba da kallo dan ita kwata kwata tama manta da yaya Ahmad ya taɓayin wani chiwo a rayuwar sa tun daga farko har karshen yanar da Ahmad ya warke sai da suka kalla a tare

nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke lokacin da suka kammala kallo satar kallon ta yayi ta kasar ido yayin da itama take satar kallon sa tana jiran taji me zai che, shiru yayi yana tunani idan dai hakane zuchiyar yarinyar nan take bai kamata naki ansar ta a matsayin sister na ba,tabbas ko dan taimakon É—an uwana da tayi ya kamata itama na fara tausayin ta na É—auke ta kamar Zahra Auta, da wanna tunani ya fita Cameran É—akin Ahmad ya shiga na gidan Aunty farida tare da É—aukar wayar sa ya kira layin Aunty farida

lokacin da kiran Bgs ya shigo wayar Aunty farida tana bedroom, nata Camera kuma a iya palo Bgs ya sanya shiya sa ya kirata domin ta fito palo, zubur Aunty farida ta miƙe tsaye lokacin da ta ga sunan mai kiran ta dogon numfashi ta ja tare da sauke ajiyar a fili tace "yau kuma an tuna da ni kenan yau kuma ko meya sanya Prince ya kirani ko dai ya hakura ya sauko ya chireni a blacklist ɗin ne,jiki na rawa ta ɗauki kiran tare da manna wayar a kunne tana faɗin "hello" ba tare daya amsa ba yace "ki fito palo" yana gama faɗin hakan ya katse kiran, chikin zafin nama ta nufi palo jikin ta har bari yake ita duk tunanin ta yazo gidan tane dan bata taɓa tunanin akoi Camera a gidan na ta ba

pitowa palo tayi amma bataga kowa ba zama tayi saman sofa tana jiran taji me zai faru kuma gaba, massage ne ya shigo wayar ta tana dubawa ta ga Bgs ne ya turo mata, "kunna cameran system naki" abun da aka rubuta a sakon massage ɗin kenan tunani ta shigayi anya Safras lafiyan sa kuwa anya bai sha wani abun ba kuwa? Mutun ne kamar wani aljani bai da aiki sai bawa mutane umarni kamar shi ya haifesu to idan nace ba zan kunna cameran bafa dan iskanci tun yaushe bamuyi waya da shi ba amma ko ya tambayi ya nake, wani tunanin ne ya sake faɗo mata to idan abu mai mahimmanci zai nuna mata fa ai gara ta kunna cameran dan tasan shi dai Safras baya chewa ayi abu haka kawai sai da dalili, tuna hakan yasa ta miƙe chikin sauri ta karisa wajen table ɗin tsakiyar palon ta ɗauko system ɗin duk abun da take Bgs da hiyana suna kallon ta tana kunna system ɗin ta shiga Camera tana shiga Bgs yayi connecting nasu,

Aunty farida bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba ganin Bgs da hiyana zaune waje guda saman gado ɗaya kawar da kai gefe Bgs yayi yana faɗin "ya Junior? Ba karamin haushi Aunty farida taji ba wato ma ba zai gaishe ta ba sai ya wani kawar da kai yama faɗin ya Junior wai shin yaushe Safras zai chan za ne shikan a rayuwar sa, hiyana ce ta katse ta da chewa "Aunty farida ina wuni dawo da kallon ta Aunty farida tayi kan hiyana lokacin guda ta saki wani Cool murmushi tana son suyi gulma da hiyana amma ba hali tana so ta tambayeta ya akayi suke tare waje ɗaya da Bgs bayan ada tasan ko fuskar hiyana bai san gani amma duk ba daman yin haka dan yana zaune ya chiro wayar sa yana latsawa duk da hankali sa na kan wayar sa yana jin duk abun da suke sosai hiyana da Aunty farida ke zuba hira suna dariya kamar wasu kawaye kwata kwata hiyana ta manta ma Bgs na jinsu ta saki jiki sai zuba hira suke sai da ya gaji sun chika masa kunne dan shi ba mai son surutu bane chikin sauri ya ɗauki remote yayi disconnecting da Aunty farida ko sallama bai bari sun yi ba

wajen Ammi ya shiga ya ha É—asu da Tv palon ta dan a iya palo kawai yake sanyawa matan Camera kannan sa maza ne yake samu su har bedroom na su

Ammi na zaune a palo tana shan fura ga Tv a kunne tana kallon News, kamar daga sama taga kallon ya ɗauke sai ganin hiyana da Bgs tayi zaune a bakin gado,tasha ruwan mamaki amma sai ta ɓoye mamakin nata chikin farinchiki kamar bakin ta ba zai rufu ba tace "my hiyana a ɗo jam (my hiyana kina lfy)? "Lfy lau Ammi ina wuni? Ammi dai tama kasa yin wani dogon magana gaba ɗaya farinciki da murna ganin hiyana ya sanya harshen ta yayi nauyi "Ammi ya su yaya Haidar? Hiyana ta sake jefo mata tambaya
Sai lokacin Ammi ta samu damar chewa "my hiyana yaya jiffina oɗo wanna ma ko haɗi ko? to owala wanna ma dai dai a yacha am (my hiyana yayan ki ya sauko yana miki abun da ya dace ko idan fa baya miki ko yana miki wani abun da baki so to ki sanar da ni karki ɓoyemin kin ji) Ammi tayi magana chikin harshen fullanci ne dan bata son Bgs yaji me suke faɗe satar kallon sa hiyana tayi ta kasan ido dan ita dai tasan Bgs na jin fullaci ta taɓa jin sa yana magana da harshen fullanci a waya ko kallon in da suke bai yi ba latsa waya kawai yake kai kace kwata kwata baya jin me suke faɗe, jiki a mace hiyana tace chikin harshen fullanci "babu abun da yake min Ammi sai kyautatawa" sosai suka sha hira Ammi sai kawo mata zanchen Bgs take da fullanci hiyana na kakkauchewa dan karya mata hukunci

Daya ji hiran Ammi fa ba mai karewa bane sai ya kashe Tv nasu gaba ɗaya yana jan tsaki su mata basu da wata matsala a rayuwar su idan sun haɗu dai sai suyi ta magana ba hutawa, chikin sanɗa hiyana ta miƙe tana son ta zame ta gudu dan tasan duk abun da Ammi ta faɗa yaji kuma yanzu zai iya mata wani abun akan hakan duk abun da take yana kallon ta ta wutsiyar ido sai da ya barta ta kai bakin kofar fita chikin harshen fullanci yace "waru haɗo (zonan)" turus ta tsaya zuchiyar ta na dukan uku uku dan daman tasan yaji kuma tun da yaji ba zai kyaleta ba mutun kamar wani aljani ko waye ya koya masa fullanci ohon masa ko aina ya koya oho gashi fullanci nasa ma har yafi nasu hiyana fita,

jiki a mace ta koma ta tsugunna a kasa tana faÉ—in "damin É—o (gani nan) kamar bai san da zaman ta awajen ba yayi shiru ya chigaba da latse latsen wayar sa tun hiyana na sa ran zai yi magana har ta chire rai kwatsam sai taji sexy Voice nashi ya daki dodon kunnen chikin harshen fullanci "or daman kin che wa Ammi ina miki wani abun kenan ko? To me nake miki faÉ—a min naji" girgiza kai ta farayi tana faÉ—in "aa yaya Prince wlh ba abun da kake min" wani mugun kallo ya jefa mata da manya manyan green eyes nashi nan wadda ya sanya ta haÉ—iyar yawun wahala da kyar
Chapter 44 · 0% Book details