← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 80

Sashe 69

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barci mai matukar daɗi ne ya kwashe su yana rungume da ita a jikin sa. yana tsaka da barci wayar sa ta fara kara da kyar ya iya waro idon sa waje kusan tare suka farka da shi da ita ɗauko wayar yayi daga saman drawer sunan Khalid ne ya bayya na a kan screen ɗin duba time yayi 3:55pm tsaki yaja tare da kai kallon sa kan kyakkyawar face nata dai dai lokacin ta waro blue eyes nata a kan kyakkyawar face nashi da kyar ya iya futa "are you okay? Gyaɗa masa kai tayi kafin tace "yaya Prince ya muka dawo gida? Ya baka kai ni yawo sosai ba? "Eh duk da munyi fitar sirri akoi wayan da suka bi bayan mu ne shi ya sanya muka dawo gida yanzu dai tashi mu wuche lokacin tafiya yayi" yana kai karshen maganar ya miƙe ya sauko daga gadon.
kasa tashi tayi dan yana miƙewa wani mugun sanyi ta ji ya rufe ta,har ya kai bakin kofa ya juyo yana kalle ta tana kwance kamar yadda ya barta "sister ba zakai je Nigeria bane? Shagwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka ta fara magana "yaya Prince sanyi nake ji kuma na kasa tashi" dawowa yayi chikin ɗakin ya ɗauke ta chak ya fice da ita sai rawan sanyi take har ya kai palo sai kuma ya juyo ya dawo ya ɗauki ɗan karamin trolley sa daya shirya tana kwance saman kafaɗar sa kai tsaye waje harabar gidan suka nufa.

Already su Khalid sun fito kowa ya shiga motar sa tare matar sa Hisham da Ilham suna tsaye a harabar gidan suna musu bye bye ganin Bgs É—auke da Hiyana ba karamin mamaki ya basu ba tunani Khalid ya shigayi anya Bgs ba wani abun yayiwa sister ba da ta sanya yau tun safe yake ta É—aukan ta kai da biyu wlh ba haka nan ba. Ilham kuwa matsowa tayi kusa da kunnen Hisham tace "baby wai haka ogan kunnan yake? Baya barin matar sa ta tafi da kafar ta kai gaskiya ya iya soyayya da kula da mata" harara Hisham ya watsa mata kafin yace "ki dai iya bakin ki wlh idan ya jiki ba mai iya tare miki.

da gudu Abdol ya buɗe ma Bgs mota ya sauke ta a gidan baya sanna ya juyo yana kallon Hisham ba tare da yayi magana ba chikin sauri Hisham ya tako ya kariso gaban sa hannu Bgs ya miƙa masa Hisham har jikin sa na rawa ya bawa Bgs hannu sukayi mu sabaha chikin nitsuwa Bgs ya fara magana "to Hisham ka dawo mu kuma zamu tafi amma 2 weeks zamuyi ka kula da aikin ka sai mun dawo" yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar Hisham ba ya saki hannun sa ya shige chikin mota sosai Hisham ya musu fatan alkhari da fatan adawo lfy sai murmushi yake.

Bayan tafiyar motocin su Bgs Ilham ta matso kusa da Hisham ta fara magana "baby me ya faru? Naga kana ta murmushi da baka taɓa yin irin sa ba" "my wife kin san matsayin Brigadier general kuwa? Bgs yana gaba da mu nesa ba kusa ba ina murmushi ne saboda yau na gaisa da shi hannu da hannu tare muka taso da su amma ban taɓa gaisawa da shi hannu da hannu ba ke ko baki da baki ma idan kika gaishe sa ba amsawa yake ba bare hannu da hannu shi idan kin gansa yana magana to umarni yake badawa idan za'a tafi filin yaki banaji awajen Aikin mu akoi wan da zai che miki ya san kalar voice nashi akoi manya manyan sojoji ma da basu taɓa jin voice na shiba duk yadda zan faɗa miki wanene Bgs ba zaki fahimta ba ni dai ina farinciki yau" a kule Ilham tace "to baya kula ka me ya sa zamu zo gidan su mu zauna? " "My wife ki sani nifa mun taso tare ne amma su Khalid ne abokai na ko Aryan ban kai matsayin da zanyi abota da shi ba tare Bgs ina ga baki san me kike faɗe ba ne kin san miliyoyin mutane nawa ne ke neman irin daman da na samu wasu sojojin ma nema suke ko a masu sharan gida ya ɗauke su su dai suga suna kusa da Brigadier general Safras amma ke shine kike wata magana" ajiyar zuchiya ta sauke kafin tace "tom shike nan muje mu shirya muje yawo" hannun ta ya riko suka wauce chikin gida.

A ɓangaren su Bgs kuwa lokacin da suka isa Airport an gama shirya musu komai suna isa ba tare da ɓata lokacin ba suka fito daga mota suka shiga katafaren jet ɗin Bgs mai ɗauke da tambarin sunan sa da manyan baki PRINCE SAFRAS zama yayi saman haɗaɗiyar kujerar jet ɗin hiyana ta zauna kusa da shi bawani ɓata lokacin su Khalid kowa tare da matar sa ya zauna har jirgin su ya ɗaga hiyana bata dawo dai dai ba. sanyi zazzaɓi take ji sosai chikin rawar murya da kakkarwan sanyi ta fara magana
"Yaya Prince sanyi nake ji sosai" kallon ta yayi da kyau kafin ya nuna mata saman chinyar sa da hannu ba tare da yayi magana ba da kyar ta miƙe ta dawo saman chikinyar sa ta zauna buɗe zip ɗin jaket ɗin jikin sa yayi ya kwantar da kan ta saman faffaɗar kirjin sa ya rufeta da jaket ɗin iya kan ta kawai ya bari awaje shiru ta lafe a jikin sa tana mai da numfashi. "Are you okay now? Ya tambayeta yana kallon face nata sai lokacin ta ɗago ido tana kallon kyakkyawar face nashi ɗan kwanto da kai sa yayi ta gefe yana kallon chikin idon ta girgiza mata kai yayi ya ɗaga gera ɗaya alamar lfy kike kallo na cool murmushi ta saki kafin tace "kamin kyau sosai ne shi ya sanya nake kallon ka" kawar da kansa gefe yayi yana murnushin gefen fuska.

Kallon Yusuf Khalid ke yi yayin da shima Yusuf ɗin ke kallon sa suna son yin gulma amma suna tsoro yau suna ganin ikon Allah domin idan ba ikon Allah ba ba abun da zai sauya Bgs haka wai har da kawar da fuska yana ɗan murmushi lallai sister ta chiri tuta lallai yau hakuri yayi rana daman duk wanda yayi hakuri zai yi nasara a rayuwan sa. waya Khalid ya chiro ya fara yi musu video ba tare da sanin su ba a ɓangaren Yusuf ma hakane waya ya chiro ya fara ɗaukan Romeo and Juliet ɗin nan ba tare da sanin su ba sai hira hiyana ke zuba masa shiko ya zuba mata manya manyan green eyes nashi yana kallon face nata a haka har barci ya ɗauke ta kasa ɗauke ido yayi da kallon ta gyara mata kwanciya yayi da kyau a jikin sa yana kallon face nata wani irin nishaɗi da farinciki ne ya dira a zuciyar sa lokaci guda. Shafa kan sa yayi ya furzar da iska mai zafi chikin ran sa yana tunanin "why? duk lokacin da nake kallon face ɗin yarinyar nan nake jin nishaɗi da farinciki ne why? Ko da yaushe nake son kallon face nata? why Nake jin ta har chikin raina? why Yanzu nake tunanin ta sosai?" ɗayan ɓangaren zuciyar sa ne ta bashi amsa da cewa "so mana son ta kake" da sauri ya girgiza kai yace "no so kuma ni? Ina never babu wanna wajen a rayuwata dogon tsaki yaja tare da kawar da kansa gefe ya fito da wayar sa ya fara latsawa. Mamaki ne ya kama su Khalid murmushi Khalid yayi a ransa yace "ai kaɗan ma ka gani in dai mace ce ai baka fara magana kai kaɗai bama yanzu ne zaka fara wlh inaga sai sister ta sa ka zama kamar mahaukaci muje zuwa yanzu wasan ya fara.

9:30pm jirgin su yayi landing A malam Aminu Kano International Airport Kano har lokacin hiyana barci take ga jikin ta yayi zafi sosai

Ako da yaushe Bgs shine na farko fita idan jirgin su ya sauka dan shi baya son ɓata lokacin amma awan nan karon su Khalid sun fita sun barshi yana tunanin ya zaiyi da hiyana dake barci a jikin sa baya son tashin ta dan tana jin zazzaɓi kuma bai san ɗaukan ta ya fita da ita dan sojojin da yan sanda ga manya manyan yan siyasa awaje, Airport ɗin a chike yake da jama'a so baya son kowa ya san yana tare da mace kusa da shi. Almost 30mins yana zaune ya kasa motsawa ga dubbanni jama'a na waje suna jiran fitowar sa ga taron yan jarida Aryan na zaune a cikin mota shi da jiddan sa shiru shiru Bgs bai fitoba buɗe mota Aryan yayi ya fito ya nufi cikin jet ɗin diyana na son fita ta bishi amma ya riga yayi nisa tana tsoron jibga jibgan sojojin dake kewaye awajen

Aryan na shiga chikin jet É—in Fahad ya biyo bayan sa "lfy my blood baka fito ba" yayi maganar yana karewa Bgs kallo sai lokacin ma ya lura da Hiyana dake kwance saman kirjin sa kawar da kai gefe bgs yayi ya fara magana "tamin barchi ajiki ne Aryan bana son tashin ta dan bata da lfy kuma ban san fita da ita kasan ni ba sai na sanar da kai ba akoi tarin masoya a waje kamar yadda akoi tarin makiya" Aryan na kokarin yin magana Fahad ya rigasa da cewa "ok bari to na É—auke ta tun......bai kai karshen maganar ba ya É—agata sakamakon mugun kallon da Bgs ya wurga masa chikin sauri ya fice daga jet É—in ya koma chikin motar su. murmushi Aryan ya É—an saki kafin yace "zaka iya É—aukan ta ai sai ka rufe mata face da mayafinta yanzu ma darene ai duk da akoi hasken wuta ba lallai aga face nata da kyau ba" kallon face nata yayi kafin ya chire face mark na face na shi ya sanya mata ya É—auke ta chak ya nufi waje da ita a saman kafaÉ—ar sa Aryan ya bi bayan su.
Chapter 69 · 0% Book details