← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 80

Sashe 5

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ahzan ai na ka buge wan nan kyakkyawar yarinya haka? Kuma ina iyayenta da yan uwan ta suke? "dady wan nan yarinyar fa mahauniya che bata da hankali" " aa Ahzan wan nan yarinyar ba mahaukachiya bace ka dubi jikin ta mana ka kalleta da kyau zaka gane hakan" "to dady Ni dai a yadda na ganta sai naga kamar mahaukachiya che "To mu bari ta farfaɗo tukun nan sai muji daga bakin ta ko? Yanzu dai bari naje na sanar da mom ɗin ka sai mu dawo gaba ɗaya dan ta chigaba da kula da yarinyar" to kawai Ahzan yace miƙewa dady yayi ya fice daga ɗakin, dawo da kallon sa Ahzan yayi kan yarinyar dake kwanche bata ko motsi sosai ya zuba mata ido chikin ran shi yana yaba irin kyawun yarin yar.....

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan Allah ya kaimu

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

P*💫STAR LADY💫*4

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 4*

KANO

washe gari tun karfe 7 Aunty farida Aunty salma Aunty mardiya suka shiryawa su hiyana ɗakin su da duk wani abun da mace zata buƙata an shirya musu, super market Aunty farida taje tayiwa hiyana sayayyan kanana kaya masu kyau da tsada Akwati 3 chike da kananan kayan ta kawo mata da kanta ta shirya mata a sip sosai tasake saka Hiyana a gaba tana bata shawara da kuma yadda zasuyi dan su samu su shawo kan Bgs, ba musu hiyana ta bawa Aunty farida goyan baya tare da mata alkawarin zata yi yadda tache ba karamin daɗi Aunty farida ta ji ba sosai ta sake karfafawa Hiyana guiwa tare da mata alkawarin zasu rinƙa waya kuma zata rinƙa taya ta yaki daga nata ɓangaren, Sallama sukayi dan yau zata koma Maiduguri, kuka Hiyana ta farayi dan tana ganin kamar idan Aunty farida ta tafi shike nan Yaya Prince zai kasheta, rarrshin ta Aunty farida ta shiga yi har ta hakura tayi shiru san nan Aunty farida ta tafi

Yau ta kama Monday Hiyana na zaune a ɗakin ta dan tun da aka kawota ko palo bata lekaba saboda tsoron kar ta haɗu da yaya prince, tayi light make up sanye take chikin doguwar rigar abaya baki ta yafa gyalen rigar a kanta, tayi tagumi ta zauna shiru tana tunanin ina diyana ta shiga awani hali take yanzu shin ta chi abinchi kuwa? Tayi nisa chikin tunanin da take sai taji an buga kofar ɗakin nata, wani miguwar faɗuwa gaba taji chikin sauri ta miƙe ta nufi kofar, batare da ta tambayi wanene bane ta murza key ta buɗe kofar wani dum dum taji gaban ta ya faɗi ganin Bgs a tsaye ya juyawa kofar baya ya zura hannu a aljihun kallon sa ta baya ta farayi from head to toe sanye yake chikin wando sojoji 3cuter da farin t-shirt mara nauyi zubawa gashin kan sa ido tayi ya tara ya ɗaure a baya sai sheki gashin yake sauko da blue eyes nata tayi kan wuyar sa, wani bakin lallausan gashi ne kwanche awaje har kusa da farkon bayan sa sai wani fitinannen kamshin yake zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikin sa dawo da kallon ta tayi kan ɗamtsen hannun sa dake chike kamar zasu fasa hannun rigar aranta tana faɗin idan yaya prince ya daki mutun da hannun nan tofa wlh ba zai tashi ba chikin sauri ta tsugunna kasa murya na rawa tace

"Yaya prince ina kwana shiru bai amsa ba kuma bai yi wani motsin da zai tabbatar maka da yaji gai suwar ba, tunani ta shigayi na mai mai ta gaisuwar ne ko kuma nayi shiru to idan nayi shiru kuma bai ji gaisuwar da nayi da farko bafa? Idan kuma na mai mai ta zai iya hukun tani kai bari dai nayi shiru ai ya ji fitowa ta bari naga me zai che shiru shiru Almost 5mins tana tsugunne, shi kuma yana tsaye ya bata baya yana kallon palon kasa, shiru shiru Hiyana har ta fara gajiya da tsuguno kafarta ta fara yimata zafi sai wani ash take faÉ—i, shi ko yana tsaye ko motsi bai yi ba

Juyawa yayi ya fara tafiya batare da ya kalli in da take ba sai da ya ɗan yi tafiya mai nisa ba tare da ya juyo ba yace "Abba na kiran ki a palon sa yanzu, yana kai karshen maganar ya sauka kasa ya nufi hanyar fita palon kasa cikin sauri Hiyana ta miƙe tana kallon sa sosai ta zuba masa blue eyes nata tana kallon yadda yake tafiya, sai da ya fice daga Palon san nan ta sauke ajiyar zuchiya a file ta fara magana "kai gaskiya yaya prince yana da kyau sosai Ni wlh ma gashin kan sa na burgeni ga hannun nan na sa shima burgeni yake sosai, ɗakin ta ta koma ta ɗauki hijabi babba har kasa ta sanya san nan ta fito ta sauko kasa ta fice daga palon ta nufi palon Abba

A bakin kofar shiga part ɗin Abba ta samu Bgs tsaye yana latsa waya, tunani ta shigayi to me ya tsayar da shi kuma a nan? Karisowa tayi wajen da yake ta sake sugunnawa tace "yaya prince ina kwana, ba tare da ya ɗago da fuskar sa daga kan wayar tasa ba ya daka mata wani mugun tsawa chike da izza yace "ke Ni zaki tsayar ina jiran ki!!? Chike da tsoro da karyewar zuchiya murya sai kerma yake tace "kayi hakuri yaya prince ban san Ni ka ke jira bane, dogon tsaki yaja tare da shigewa chikin part na Abba chikin sauri ta miƙe tabi bayan sa

Gaba É—aya family sun haÉ—u a table É—in chin abinchi

Abba na ganin Bgs da Hiyana sun shigo a tare ya fara murmushi yana faɗin "haka nake son ganin ku kowa ya shigomin shi da matar sa a tare shi yasa nache kuzo a tare, wani kululun ɓakin chiki Bgs yaji tazo masa har wuya jiyake kamar ya shake yarinyar nan ta mutu kowa ya huta wai ma ni ban ga abu da ya sanya Abba yake son dan gan tani da yarinyar nan ba

karisa wa wajen Table É—in su kayi kujerar kusa da Aryan Bgs yaje ya zauna tsayuwa Hiyana tayi tama kasa zama dan tsoro, sai kallon su Zahra take É—aya bayan É—aya kowache tana zaune kusa da mijin ta ba karamin kyau hakan ya mata ba ji tayi itama tana bukatar zama kusa da mijin ta

hannu Abba yasa ya mata nuni da kujerar dake gefen Bgs ɗin yana faɗin "zo ki zauna kusa da mijin ki, jiki ta har rawa yake saboda tsoro gaba ɗaya palon sunyi shiru suna kallon ta ita kuwa zulaihat kallon Bgs kawai take tana yaba kyan sa chike da ɓachin rai Bgs ya miƙe yana faɗin "Abba ka dai na min hakan bana so! No need ma na ji dalilin da ya sanya ka kiramu na fasa yin 3 month ɗin yau jirgina zai ɗaga zuwa London" tun da ya fara magana gaba ɗaya family suka nitsu suna kallon sa yana kai karshen maganar ya juya zai fita chikin sanyin murya Ammi tace "Prince dawo ka zauna a sukwane Bgs ya juyo dan Ammi bata taɓa yi masa magana da sanyin murya haka ba kuma bata taɓa kiran sunan saba sai dai tace masa kai, lallai yau dole nayi abun da kike so my Ammi nan take yaji zuchiyar sa tayi sanyi juyawa yayi ya koma kujerar da ya tashi ya zauna, shi dai Aryan duk wan nan abun da ake bai ma san ana yi ba dan kwata kwata hankali sa baya tare dasu ya sunguyar da kansa kasa da alama tunani yake

"Hiyana zo ki zauna kusa da mijin ki chewar Ammi chikin rawar murya hiyana tace "Ammi ni bana jin yinwa zan iya komawa É—aki? Gaba É—aya su Abba sai da suka tausaya mata ban da zulaihat da Aunty amarya dake ta jin daÉ—i nuni da hannu Abba yayi mata akan tazo, ba musu ta karisa kusa da shi zata tsugunna yayi saurin dakatar da ita tare da kamo hannun ta ya zaunar da ita a saman kujerar dake kusa dashi "Abba wai me yasa ka kiramu ne chewar Yusuf dake zaune kusa da Baby Lamrat nashi, gyaran murya Abba yayi san nan ya fara magana

"Daga yau idan ba nawa matan ba karwan da ya sake zuwamin palo chin abinchin kowa matar sa ta rinƙa kai masa ɗakin sa, da sauri Yaya Ahmad yace "Abba ni da Umar da Haidar fa "eh ku ma ai na kusa yin naku bikin amma kafin nan kurinka zama a ɗakin ku mai Aiki tana kawo muku" Umar yayi sauri chewa "Abba dan girman Allah karka yimana irin Auren da kayiwa su yaya prince kabari mu samo matan m.. bai karisa maganar ba yayi shiru sakama kon wani mugun kallo da Bgs ya wurga masa dariya ne yaso kub chewa Zahra Amma sai tayi saurin damme wa hakan ya haifar mata da tari, tari take sosai chikin sauri Khalid ya ɗauko ruwan dake gaban Abba ya fara bata abaki yana faɗin "sorry my wife yana ɗan bubbuga mata baya

Wani kunya Ammi taji ya lullɓeta ji take kamar ta make Khalid, shi ko Abba sai murnushi yake ba karamin daɗi yaji ba ganin yadda Khalid ke kula masa da autar sa
Chapter 5 · 0% Book details