← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 86

Sashe 74

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh haka ne nima nasan kin k'ara girma amma ni barin fad'a miki irin wanda nake nufi.."
Kallonsa taci gaba dayi tana sauraren jin me zai ce,hannunsa tajiyo k'asan cikinta yana shafa dai² mararta yake fad'in
"Da ace kin girma ina tunanin ni ne mutum na farko da zai tabbatar da haka,kuma da nan gurin ya tabbatarmin da hakan koba haka bane..?"
Sakin bakinta tayi tana kallonsa,lallaima YAYA'N nan nata ya rainata da yawa wato nufinsa har yanzun bata girmaba kenan yake nufi? Har sai ya ganta da ciki zai yarda lallai ne kuwa ta bashi mamaki kuma tabbas ta d'auki alk'awari saita nuna masa itan ta girma.
Bata sake bi takan maganarba tayi cilli da ita gefe,idanunta ta lumshe tana jin yadda yake shafa k'asan cikinta ita kam bata san wane irine YAYA'N nata ba duk wani abu da zaiyi ya jefa zuciyar mutum cikin soyayya ya iya,gani take da ada ne aka tambayeta yaya halinsa yake zata ce babu ruwansa shi en kamili ne kuma bashi da fitina,amma kam a yanzun cikin d'an tak'aitaccen lokaci ta gama fuskantarsa a nata tunanin tsaf zata zane littafi hard cover da halayensa,katse mata tunani yayi da fad'in
"JODI ki shi shiryafa cikin satin nan zaki fara zuwa makaranta"
Daga haka bai k'ara ko wasalin 'a' ba ya d'inke bakinsa ta hanyar rufe idanunsa danma kada ta dameshi da tambayoyi,hakan data ga yayi yasa ta yin murmushi cikin sanyin murya ta furta
"Allah ya kaimu,ubangiji kuma ya bamu sa'a..."
Amsawa yayi yana yadda yake tare da sakin mata kiss a porehead enta,murmushi tayi tana sake tightening hands enta dake jikinsa,kamar masu bacci haka palour'n yayi shiru baka jin maganar kowa cikinsu amma kuma a hakan hira suke da junansu,kiran daya shigo wayan KHUBRA ne yasa ta d'ago ta kalleshi,shi enma ita yake kallo mik'ewa tayi daga jikinsa inda bayan ta d'auka kiran ta shiga gaida MAMA,tambayan da MAMA tayi mata ne yasa ta kallonsa da sauri kuma ta d'auke kanta tana ci gaba da sauraron maman dake maimaita mata tambayan
"Doughter wai kam ina son tambayanki,ranan da kuka zo gida mai ya had'aki da ABBA ne kam har kika janyo ya miki fad'a...?"
Ajiyar zuciya tayi kafin cikin sanyi ta shiga bawa MAMA labari bata b'oye mata komaiba,a b'angaren MAMA kam taji dad'i sosai da yarinyar tata tayi wannan tunanin sai dai kuma dalilin da yasa ABBA ya mata fad'a shine tayi k'aranta ta fad'a masa wannan maganar kamata yayi dama a samu mutum wanda yake babba mai cikakken hankali sai ya nusar da shi cikin hikima da siyasa,kuma tabbas al'amura zasu tafi yadda ya kamata idan haka ta faru.
Nasiha tayi mata sosai akan ta kira shi ta bashi hak'uri sannan kuma kada ta sake yin maganar da kowa,haka dai har suka gama wayan ta ajiye,suka sake ci gaba da uzurin gabansu...

Kwanaki sun ci gaba da wucewa yayin da kowace rana da zata zo ta wuce take tafe da nasarori masu d'umbin yawa.A bangaren su KHUBRA da BB ma hakan ce ta kasance inda maganar makarantar ta ya kankama,makaranta mai kyau wacce kuma zata koyi karatun babu wasa ya kaita,kuma alhamdulillah! al'amura na kyau sosai,shi da kansa yake kaita school sannan idan an tashi shi yake zuwa ya d'aukota,ko da ace yana office ranar da zaran lokacin komawanta gida yayi zai tattara abunda yake yi ya tafi,sai ya maidata gida sannan zai koma office ya k'arasa aikin ranar,wata ranar kuwa idan ya dawo tofa bai komawa sai dai gobe.
Rayuwarta a makarantar wani lokacin idan ta kalli da yawan d'aliban sai taga akwai wanda ko a shekaru ya girme mata bare kuma girman jiki da wasu tsaf sai su d'auketa suyi ta gudu da ita ba tare da nuna gajiyaba,wani lokaci idan taga haka sai take tuna BB lokacin da yake mata maganar karatun,sai dai kaga tayi murmushi ita kad'ai.
Zaune take k'ark'ashin wata bishiya tana duba littafinta da suka gama lesson,tayi nisa a dubawa taji an mata sallama,d'agowa tayi dan ita a tarihin zuwanta makarantar babu da wacce suke k'awance,wata y'ar matashiyar budurwa ta gani tsaye tana mata murmushi,kyakykyawa da ita son kowa k'in wanda ya nema bai samuba,cikin dakewa ta amsa mata suka gaisa a mutunce,kallonta waccan d'ayar tayi tana fad'in
"Idan babu damuwa kuma ban takura mikiba shin zan iya zama...?"
'Dan murmushi KHUBRA tayi ganin itama da fara'a a fuskarta tayi maganar
"Babu komai bismillah! ki zauna"

"To ai kuwa na gode sosai da amsamin da kikayi.."
Matashiyar ta fad'a kafin cikin d'an yanayi na kasancewarsu sababbi a gurin ta furta
"Ni suna na AMINA UMAR FANA,nima sabuwar d'aliba ce a nan,to kuma ban san kowa ba a nan sai yau Allah yasa na ganki nayi kuma sha'awar miki magana ban sani ba ko zamu iya zama k'awaye.."

"Allah sarki ai nima da yake sabuwar zuwa ce shi yasa kika ga na zauna nan saboda babu wanda na sani,amm! ni kuma suna na KHADIJAT ABUBAKAR SA'AD amma a gida ana kirana da KHUBRA.."
Dukansu suka yi murmushi wa junansu,a hankali suka ci gaba da hira jefi-jefi kuma mafi yawanci duk akan karatunsu na ranar da suka yi ne,sosai tarayyarsu ta basu sha'awa ganin sun taimakawa juna da abunda d'aya ya gane d'aya bai ganeba,har lokacin tashinsu yayi,dai² lokacin aka zo d'aukan AMINA inda tayi ta yima KHUBRA magiyan tazo su tafi tare,hak'uri ta bata tana kuma fad'a mata itama yanzun za a zo d'aukanta,haka ta tafi wanda suna yin gaba BB yayi parking,glass en side ensa ya sauke yana kallonta,d'an murmushi tayi kafin ya fito ya bud'e mata ta shiga,sai da suka d'auki hanya ba tare da ya kalletaba yace
"Wane mota na gani ya tsaya inda kike....?"
Shiru ta masa babu amsa,shi kuma yaci gaba da fad'in
"Kina sane da cewa ke matar aure ce ko...? to ina so ki kiyaye kule-kule babu ruwanki da kowa coz bana son fitina kinji me nace...kiyi abunda ya kawoki babu ruwanki da shiga abunda ba a sakiba kinji...?"
Kanata ta d'aga alamar taji.

Kwanaki biyu tsakani take bashi labarin AMINA da suka had'u a school irin kirkinta da kuma yadda suke zaune da juna,yaji dad'in yadda ta fad'a masa abunda ya had'asu kuma shima ya tabbatar da cewa yes matarsa kam y'ar baiwa ce,yanayin yadda yake zama suna lesson kan abunda aka musu a makaranta duk bayan sallar maghreb yasan tabbas baya asara...

Tun bayan da sukayi magana da MAMA akan dalilin daya sa ya mata fad'a a wani zuwa da sukayi a can baya,MAMA bata b'oyewa ABBA'N su BB komaiba ta sanar masa cikin hikima da siyasa shi da ABBA'N KHALEEL suka sashi gaba da maganar,sosai suka kai ruwa rana da su wanda daga k'arshe kuma yaga rashin dacewar k'in amincewar da yayi tun farko,shi da kansa ya same su da maganar daga baya,cikin lokaci k'alilan aka gama magana,da taimakon MAMA da UMMI suka sata gaba itama kuma sai Allah ya taimaka basu wani sha wahala ba ta amince,an yanke d'aurin aure kad'ai za ayi sai tariya kuma babu wani taro da zasu yi bare mutane su fahimci wani abu game da sirrinsu,cikin lokaci kad'an aka d'aura auren ALHAJI ABUBAKAR SA'AD da amaryarsa HAJIYA ZUWAIRA akan sad'aki mafi inganci,anyi taro lafiya wanda y'ay'ane kad'ai suka halarta babu wata gayyata da suka yi daga iyayen sai su.
ASHNA kam lokacin bikin tana ta fama da laulayin ciki kuma sosai take shan wahala,babban dalili kenan daya sa FATAHIYYA komawa gidanta tana taimaka mata,palour suka rashe sunata hira tsakaninsu BB,KHALEEL,SADEEQ BIGGY,KHUBRA,ZUHRA dama ASHNA dake fama da kanta amma a haka ta dage itafa saita zo dan baza ayi babu itaba,FATAHIYYA kam d'akinta na gidan ta tsere dan cewa tayi bata iya zama gaban yayyen nata da ko wanne yake manne da matarsa ita a nata ganin kam wannan fitsarar da suke gwadawa bata iyawa.
Haka aka gama taro kowa ya d'auki matarsa yayi gaba,sai fatan samun zaman lafiya da sab'awar halaye.

Lokaci baya jira sai dai a jira shi kamar yadda wannan magana take haka fa abubuwa suke,bayan kimanin watanni biyar da auren ABBA'N KHUBRA,ASHNA ta haifi zankad'ed'en saurayi Yaro yaci sunan ABBA'N BIGGY wato MUHAMMAD suna kiransa da AL-MUSTAPHA,fad'in hidimar suna da suka sha a wannan family'n b'ata baki ne,yayin da a b'angaren ZUHRA da KHUBRA kuma shiru kake ji babu wacce tayi ko da b'atan wata,sam hakan bai wani dame suba dan ganin samu da rashi duka daga Allah suke lokaci kad'an yake azurta mara shi kuma hakan ma ba abun damuwa bane tunda duka yaushe akayi auren da zasu d'aga hankalinsu,a b'angaren karatunta kuwa ta dad'a maida hankali sosai k'awancen su da AMINA kuwa sai abunda yayi gaba,mutane da dama suna mamakinsu wanda bayan tsayin watannin da suka shud'e kowacce ta san y'ar uwarta nada aure,k'awance na tsakani da Allah suke duk inda kaga d'aya cikin makaranta to zaka ga d'aya,mazajensu sun san juna yanzun baya ga ziyara da sukan kaiwa junansu,sun dad'a dagewa akan harkar karatunsu abunda ya kaisu shi suke yi babu wasa,tsakaninsu da mutane gaisuwa ce suna kuma matuk'ar girmama junansu.

Yau tunda KHUBRA ta shigo skul take baza idanu taga inda aminiyar tata zata b'illo amma shiru kake ji,zaman makarantar duk ya isheta haka dai tayi manage har aka tashi,ko data koma gida bayan ta kirata a waya a kashe aka shaida mata,yinin ranar haka ta yini wani iri da ita wanda shi kansa BB sai da ya gane haka,ko da ya tambaya bata b'oye masa komaiba ta sanar masa,addu'ah ya nusar da ita tayi kan Allah yasa lafiya.
Washe gari tana shiga skul ko ta hangota har ta rigata zuwa,da saurinta ta k'arasa kusa da ita tana fad'in
"Haba CWEET SIS jiya kuma sai najiki shiru,kuma line wayanki a kashe haka naita fama da tunanin lafiya..."
Chapter 74 · 0% Book details