← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 86

Sashe 52

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da sanyin safiya aka hau shirin tafiya garin na KASHIN DILA dake cikin K'ARAMA HUKUMAR KIRIKASAMMA dake cikin HA'DEJIA a jihar JIGAWA...
Shirin tafiya ya kankama a wajen ABBA,UNCLE dama jagororin tafiyan wato BB da KHALEEL,sai sauran yaran wato ZUHRA,KHUBRA,ASHNA da FATAHIYYA da suke seat en baya,jikin KHUBRA yayi sanyi sosai tunda taga sun d'auki hanya,sai take ganin kamar yaune aka rabota da mahaifinta,kanta ta kwantar jikin ZUHRA zuciyarta babu dad'i,a haka da take kwance take matse idanunta tana hawaye...

BB da KHALEEL na gaba amma babu wata hira da suke sai dai idan KHALEEL yayi magana BB ya Amasa masa da "Eh ko A'a"....

《《》》

"Kina ina maza fito yau ba sai gobeba wollahi sai mai gari ya shiga tsakaninmu,dole ki nemomin inda y'ata take..."

Rab'e-rab'e take tana bin hanya,tana fitowa ko ABBA ya maka mata wata uwar harara da shi kad'ai ya san ma'anarta,sai kuma ita da akayi dominta

Jiki na rawa baki na b'ari take fad'in
"Dan Allah dan sonka da ma'aiki kayi min rai MALAM....... dan Allah ka k'aramin lokaci....Wallahi zan nemota duk inda take...."

"Ke rufemin baki mak'aryaciya munafuka kawai....Har tsawon wane lokaci kuma zan ci gaba da zaman jira....Wallahi yau sai na tona miki asiri ko kuma ki fitomin da inda take...."

"Wallahi MALAM naji zan nemota amma kayimin rai dan Allah"
K'afafunta zube a k'asa take wannan bayanin wanda babu abunda ke fitowa tsakaninta da MALAM BUBA sai uwar harara da yake sakar mata babu k'ak'k'autawa...

"Kin san Allah yau kam ba zan kyalekiba,sai mun dangana da gurin mai gari kuma tabbas sai kin karb'i hukunci a yau ba gobeba....."
Cakumota yayi ya mik'ar tsaye yana shirin yin hanyan k'ofar gidan da ita yana ingizata gaba
"Tsohuwar munafuka algunguma muje....."
Ko rufe bakinsa baiba tsayuwan mota ya dakatar da shi,da sauri ya nufi hanyan zaure yana son dubawa,har lokacin kuma LADIYO na chafe a hannunsa........

*~#TEAM KHUBRA.~*

*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*21/ʝųlყ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*4⃣8⃣*

*K'* atuwar motar da tayi parking a k'ofar gidan nasa yake bi da kallo game da tsantsan mamaki a zuciyarsa yake fad'in
"Wannan kam sunyi makuwa da alama gidan mai gari suke nema....."
Bai gama tunaninba mutanen ciki suka shiga fitowa d'aya bayan d'aya,har lokacin ABBA'N KHUBRA mamaki ne shimfid'e a saman fuskarsa saboda rashin sani wanda ake cewa ''yafi dare duhu''.

KHUBRA da take kusan ta k'arshen fitowa daga motan,idanunta suka sauka kan mahaifinta da ako wane lokaci shi ne farin cikinta,nan ko ta kwasa a guje bata tsaya wata-wataba ta ruk'unk'umeshi,kukantane ya bayyana inda shi kuma ABBA ganin wannan al'amari yasa shi fad'in
"Y'ar nan yi maza ki sake ni kada ki jawomin abunda za a jefeni....kina yiwa Allah ki sakeni tun kafin labari ya isa kunnen mai gari...."
Idanunta da suka gama jik'ewa da ruwan hawaye ta d'ago tana kallonsa har lokacin kuma wasu na ci gaba da sakkowa
"Alhamdulillahil-laziiy bii ni'imatihi tatimmus-salihaat!!!...."
Abunda bakin ABBA'N nata yaketa furtawa kenan har lokacin kuma ya gagara sakinta saima dad'a k'ank'ameta da yayi kamar wanda akace za a rabasu har abada.
"UWATA ke ce ko kuwa gizo kikemin kamar yadda kika saba zuwamin...?"
ABBA'N nata ya tambaya cike da rashin gasgatawa,saboda a ganinsa a ko wane irin lokaci zata iya b'acewa daga gurin.

"ABBA nice ba gizo bane..."

Godiya kawai yakewa Allah daya bayyana masa y'ar tasa kwaya d'aya tal.

ABBA'N BB ne ya matso kusa dasu hannunsa na nuna MALAM BUBA da shi sam ma bai kula ta kansuba y'arsa ce kad'ai abunda idanuwansa ke hango masa,da k'yar ABBA ya harhad'a kalmomin yana fad'in
"M.A....L..A..M......BU....BU...BUBA....."

A d'an firgice ABBA'N KHUBRA ya d'ago kansa yana kallon inda aka ambaci sunansa,kallonsa yake like no other yana son tuno inda ya sanshi,amma sam k'wak'walwarsa ta gagara tunawa da abunda yake son ganewar tattare da wannan d'an gayun mutumin.

"Nasan da wuya ka iya shaidani amma da zaka kalleni sosai tabbas zaka iya tuna fuskata..."
ABBA ya fad'a yana murmushi,aiko kamar wanda aka bawa wani gagarumin aiki ya k'ure shi da idanu duk da ya kasa tunawar hakan baisa ya hak'ura ya daina kallon ABBA'N BB ba..
"A gaskiya ALHAJI ban shaidakaba,sai dai ko kamin k'arin bayani la-Allah sai na iya tunawa"

Sai da ya saki wani k'ayataccen murmushi wanda ke bayyana kyau da kuma zallan hutu da wannan bawan Allah ke ciki sannan ya furta
"Ehhh! to ina ganin mu zauna tukun dan maganar tamu bata buk'atar muyita a haka..."

LADIYO na gefe rakub'e a zaure tana lek'e dan tun bayan da ta samu MALAM en ya saketa tayi zaraf ta shige had'eda lab'ewa tana lek'en wad'annan turawan bak'in.
Duru-duru MALAM en ya shiga yi na neman abun da zai shimfid'a musu su zauna,kafin yayi yunk'urin yin wani abu LADIYO tayi zaraf ta fito tana fad'in
"MALAM ai da ka kaisu cikin gidan ko dan nan yayi kan hanya..."
Wata uwar harara ya sake aika mata wacce take nuni da 'idan kika sakemin shishshigi zanyi maganinki,a fusace ya wuceta dan shi kam gare shi ya tsani ko da ganinta bare har wata magana ta shiga tsakaninsu.
K'atuwar tabarma ya shimfid'a musu sannan ya shiga fad'in
"Bismillah...!!!"
Gaba d'aya ko suka nemi guri suka zauna,LADIYO da MALAM ya barta tsaye da sakakken jiki ta nemi guri daga can gefe ta rakab'e,a inda kuma tayiwa kunnuwanta matsuguni a tsakiyar mutanen da takewa kallon daga wata k'asar suka zo,musamman y'an matan da har yanzu babu wacce ta shaida hatta kuwa da KHUBRA dake kusa da ABBA'NTA ta jingina dashi,idan ta kalleshi sai tayi murmushi a zuciyarta take fad'in
"Yau nima na samu y'anci gani kusa da mahaifina...."
Abu d'aya zai iya sawa kayi saurin gano b'acewar annurin dake kan fuskarta a wannan lokacin,ba komai bane kuwa face tunanin MAHAIFIYARTA da bata tab'a ganiba.
Muryoyinsu ne suka katse mata tunani inda suke ta faman gaishe-gaishe da tambayan juna iyali,bayan nan kuma gurin yayi d'an shiru na wucin gadi kafin ABBA'N KHALEEL yayi addu'ah.
Nan kuma aka koma kan ainihin maganar da ta shigo dasu,ABBA ya sake kallon MALAM BUBA da yake jiran k'arin bayani daga bakinsa,kamar yadda suma sauran jama'ar gurin suke sauraron jin me zai biyo baya.

"Nasan gaba d'ayanku kunyi mamaki musamman dana nuna nasan MALAM BUBA ko?......"

Nan suka hau amsawa da "Hakane....!"

"To Alhamdulillah! yanzun zaku ji yadda akayi na sanshi duk da dai shi bai shaidaniba..."
Kallonsu ya sake yi d'aya da d'aya,KHUBRA kuwa murna take yi jin ABBA'NSU ZUHRA yasan ABBA'NTA,fuskarta sai annuri ke fita

"Ni dai dai farko suna na SAFWAN kuma ni haifaffen garin DUTSE ne ta nan jihar JIGAWA"

Kallonsa sosai MALAM ya sakeyi jin sunan daya ambata,kamaninsa ya shiga hangowa ko tantama ba yayi shi ne dai wanda ya sani shekara da shekaru da suka gabata..

"Tabbas wallahi shi ne!....Shi ne....SAFWAN...."
Sai kuma ABBA'N KHUBRA ya fashe da kuka da alama akwai wani abu da yake damunsa wanda ya tuna a dai² lokacin.

Da k'yar suka lallasheshi yayi shiru,inda gaba d'aya sauran jama'ar gurin suke kallonsu,saboda yadda suka sasu a duhu
"Tabbas sai yanzu na shaidaka...."
Sabuwar gaisuwa suka sake da tambayar bayan rabuwa.

ABBA'N KHALEEL ya kalli ALHAJI SAFWAN yana fad'in
"To ALHAJI mu kam kun samu a duhu,bamu fahimci abunda kuke nufiba.....dama kun san juna ne kam ko yaya abun yake....?"

Kai ABBA ya girgiza masa kafin yayi magana MALAM BUBA har ya rigashi
"K'warai kuwa mun jima da sanin juna...kamar dai yadda kuka gani yanzun zan yi muku bayanin alak'ar dake tsakanina da SAFWAN....
Ni dai da farko suna na ABUBAKAR SA'ADU wanda mafi yawancin jama'a suka sani da MALAM BUBA kamar yadda na taso da wannan suna....alak'ar dake tsakaninmu kuwa ita ce.......

《《》》

Ciwo ne ya soma cin k'arfinta tun bayan zuwanta asibiti da likita ya sanar mata komai lafiya bata sake yunk'urin komawaba,jikinta duk babu kuzari a yanayin yadda take jinsa babban dalili kenan da yasa yau d'in ta shiga shiri babu ji bare gani na ganin ta koma asibitin tunda ciwon yaci k'arfinta..
Tafiya kawai take amma da tayi tayi sai ta huta,saboda rashin kuzari duba da yadda kwanakin take fama da amai da gudawa.
Layin karb'an kati tabi bayan jira da tayi na wani lokaci sannan aka sallameta,hannunta rik'e da katin ta nufi office en likitanta na wancan lokacin.

Shiganta office en ta nemi guri ta zauna kan kujera,katin ya amsa idanunsa sanye da glasses ya kalleta yana mata tambayoyin abunda ke damunta..
A hankali take motsa bakinta saboda ina ganin kamar bakin natama ya tafi yajin aiki had'e da sauran gangan jikinta..
Idanunsa na kanta har ta k'are bayaninta sannan yayi y'an rubuce-rubuce,bayan y'an mintuna kuma ya sake d'agowa yana mata bayanin za taje tayi test a yau ta kawo masa,amsa tayi ta fice daga office en kamar wancan lokacin,bata zame ko inaba sai laboratory na asibitin.Bayan an d'ibi jininta ta zauna jiran fitowan sakamako a nan.
Mintuna sun sake shud'ewa inda wata nurse ta hau kiran sunanta aiko nan MA'U ta mik'e da k'yar tana nufarta
Wani kallo nurse en ta mata sannan ta mik'o mata sakamakon gwajin tana yatsina fuska,haka ta karb'a sannan ta kamo hanyan dawowa gurin likita danjin me kuma sakamakon nata zai nuna a karo na biyu.
Chapter 52 · 0% Book details