← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 86

Sashe 60

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai KHUBRA shiru tayi mata bata tankaba sai wayan data karb'a ta ajiye gefenta ba tare da tayi tunanin d'aukaba,saima hira da take k'ok'arin sako musu.
FATAHIYYA ta kalleta lokacin da kira na uku ya shigo wayan nata
"AUNTY da kin d'auka kinji me zai ce miki...Kinga yanzun kada kisa shi tunanin ko wani abu ya faru..."

"Ke kyale shi ai yasan a gajiye nake ni kuma yanzun baran iya d'aukaba.....Dan yanzun yana ganin na amsa zai tsare ni da surutu ni kuma gaskiya bacci nake ji...."

"Aifa shi yasa naga kinyi baccin yanzun..kina nan kin wani yi gwaraf a gaban k'anwa zaku dasa surutu shi ne harda wani cewa bacci kike ji....Allah dai yana kallonki kuma sai dai ki tunasar da wani wulak'anci babu kyau.."

Ita dai FATAHIYYA tana kallonsu idan wannan yayi magana ta juya ta kalle shi idan wannan ya amsa sai ta sake juyawa,rashin d'aukan wayan da KHUBRA tayi yasa FATAHIYYA d'auka a hankali ta furta
"Hello! YAH KHALEEL ina wuni....?"

"A'a FATAHIYYA ya kike...? Ina AUNTY'NKI fa?"

"Lahh! YAH KHALEEL damafa gani nayi kana kira ita kuma tana shigowa tayi bacci.."

"Ok! to shi kenan na gode k'anwata,da safe mayi magana da ita dama kiranta nayi naji lafiyanta,amma tunda tayi bacci shi kenan kada ki tasheta,na gode sosai.."

Sallama sukayi ta ajiye wayan,sai lokacin hankalin KHUBRA ya kwanta saboda tunda ta d'auki wayan hankalinta bai kwantaba sai da taji sunyi sallama kuma duk abunda suka fad'a taji tunda wayan a handsfree ta sata.
Ajiyan heart tayi ASHNA kam shiru tayi musu amma lamarin na KHUBRA na bata mamaki musamman da auren ya dad'a gabatowa..
Bata kuma kulasuba har suka gama abunda za suyi k'arshe kuma kowacce ta kwanta.Ita dai tana kan waya suna chart da nata prince en kuma tana cikin garin ciki........

*ONE WEEK TO MARRIAGE....*

A gurguje ya fito daga mota ya nufi cikin gida dan dama a kwai abunda ya shigo dashi yanzun da yake ta sauri kada wani ya tsaida shi.
Karo suka yi da sauri ya d'ago dan ganin me ya faru haka,kallonta ya tsaya yi ganinta yake kamar cikin mafarkin daya saba a y'an kwanakin da auren nan ya matso,sam baya son abunda zai had'a shi da ita bare ya kawowa ransa wani tunanin ko yasa damuwanta a ranshi,sai daifa hakan da yake ba k'aramin azabtuwa yakeba,duba da yadda rashin ganin nata ya dad'a jefa shi cikin wani hali,ganin da ya mata a yanzunma duk da a rashin sani hakan ya faru,sosai ta dad'a yi masa kyau musamman da bai gantaba cikin y'an kwanakin da suka wuce,kamar an dasa su zuciyarsa sai sak'a masa abubuwa da dama take a kanta,cikin sauri ya d'auke kansa tare kuma da ci gaba da tafiya abunsa..
Kallonsa kawai tayi ta tab'e baki sannan ta juya tana tafiya abunta zuciyarta na fad'in
"Anya ko YAH ba wani abu ke damunsa ba?...Ko kuwa dai ni kad'ai nake ganin haka?....To amma idan har ba gizoba naga ya rame sosai ba kamar yanda na sanshiba...."
Da sauri kuma ta d'age kafad'a tana fad'in
"Kai to ni ina ruwana ma da damuwa'rsa....Shi ya sani ko wani abu na damunsa...Can ta matse masa ni banda damuwa...Allah yayi mutum sai d'an karen nunk'ufurci..."
Hanyan guarding ta nufa tana shiga ta nemi guri ta zauna,bata jima ba a gurin ko ZUHRA ta shigo gurin
"Ki ce nan kika yo yau kuma nan kika tuno bayan da kin daina zuwa"

"Ehh fa na gaji da zama cikin d'aki ne kawai shi yasa na yanke shawaran zuwa nan nasha iska....
"Wallahi dai kam nima haka nan nake jin zuwa nan yau shi yasa na fito ban kuma yi tunanin kina nanba..."

Suna cikin hiran motan KHALEEL ta kunno kai da sauri KHUBRA ta kwanta a k'asa saman grasses en tana rufe ido,dan ita kam bata son surutun KHALEEL a yanzun sam bata shiryawa jinsu ba,a nan ya tarar dasu shima ko ya zauna,mafi yawanci hiran tsakanin KHALEEL da ZUHRA ne dan dama ita ce abokiyar kuma y'ar rakiyar zance duk lokacin da yazo hira.Ita kam KHUBRA ko magana yayi mata amsanta tsaf sai mutum ya k'irga su saboda yadda take magana a tak'aice..

Labari suke sai dariya suke duka ta window ya hangosu su uku a cikin lambun,da yake lambun yafi kusa da window ensa shi yasa yake iya jiyo sautin dariyarsu.
Yanayinsu gwanin sha'awa haka nan yau kuma yaji yana sha'awar fita zuwa gurinsu ko ya rage damuwan dake ransa.
Suit en dake jikinsa ya zare ya sauya kayan dake jikinsa zuwa masu sauk'i sannan ya fice zuwa gurinsu dan a lokaci ji yayi ba zai iya fitanba.Tun kafin ya k'araso fuskarsa a sake ba kamar kwanakin da suka wuceba ya iskesu,ganin fuskarsa a sake wanda shi kansa KHALEEL ganin canji a tare da shi sai da yayi mamaki abu d'aya ya hana shi nuna hakan murnan da yake na ganin aminin nasa ya sakko yasashi jan bakinsa ya tsuke ko a fuska kuma bai nuna masa komaiba,hira sosai da suka jima basuyi ba suke wanda k'arshe suka gangaro kan maganar program's da za ayi a bikin,lokacin da KHALEEL yayi maganar sai da BB yaji wani iri kan maganar dinner da yayi,kawai dai ya danne ne,zuciyarsa na masa k'una,maganar KHUBRA ta katse masa tunani wanda har sai da ya d'ago ya kalleta

"Ni kam dan Allah wai dole ne sai anyi wad'annan bidi'o'in..."

Kallonta sukayi su duka suna mamaki
"To banda abunki CWEETY ai hakan shi zai nunawa duniya irin farin da muke ciki..."

Tab'e baki tayi tana fad'in
"Tabbb ni kam wallahi da da yadda zanyi da nayi dan kawai na hana wannan abun....Dan ni kam har ga Allah ba so nakeba"

"Saboda me zaki ce haka CWEETY...?

Sai data kalleta sannan tace
"Saboda bana son hayaniya ne kawai shi yasa,na tabbata lokacin zanyi ta fama da ciwon kai"

KHALEEL kam sam bai so hakan ba amma saboda jin abunda ta fad'a yasa yace
"To ai ina ganin hakan ba abun damuwa bane,abu ne da za ayi na k'aramin lokaci kuma ba dad'ewa za ayi ana yiba,so ina ganin babu wani abu da zai faru in sha Allah...."

BB kam bai ce komai ba game da muhawaran da suke saima waya daya ci gaba da dannawa kamar baya gurin,hiran ya koma tsakanin ZUHRA da KHALEEL dan ita ta maye matsayin BB na babban aboki da za ayi shawaran da shi itama amarya tana gefe tayi musu shiru kamar bata gurin......

Tun da suka shiga satin komai ya dad'a kachamewa musamman da kwanaki kad'ai ya rage musu a fara biki.
A lokacin duk wanda ya kalli KHUBRA babu lallai ya shaidata saboda kyau data k'ara akan nata,fita ko a cikin satin babu mai yinta tsakaninsu kullum suna d'aki daga su sai halinsu MAMA kad'ai ke da ikon ganinsu sai ko mai gyan jiki dake zuwa kullum tana gyaresu wanda gaba d'ayan su akewa sai dai na amaren yafi na sauran,a haka sauran kwanaki suka soma cimmusu.

Kamar yadda yake a tsare bayan kamu da walima ta mata zallah da za'a gudanar a shagulgulan bikin,sai d'aurin aure wanda daga shi sai dinner da za ayi bayan nan kuma za a wuce da amare gidajensu.

Duk wannan budirin da ake har lokacin BB baiyi kuskuren d'aukan invitation card enba bare ya gayyaci wani aboki ko wani mutum mai muhimmanci a rayuwarsa nasama da aka bashi tunda ya amsa ya bud'e closet ensa ya cillasu,tun daga ranar ko bai sake bi ta kansuba,hasalima duk lokacin da KHALEEL zai kirashi akan zaizo suje rabon card en sai dai ya bashi excuse akan aiki ya rik'e shi office,duk naci da magiya babu irin wanda KHALEEL bai masaba amma sam yak'i rakashi,kan dole ya hak'ura ba dan ya soba sai dan babu yadda zaiyi da shi.

Tun daga ranar da sukayi haka da shi ko ta k'arshe bai sake nemansa daya raka shinba sai dai duk inda zashi ya kama hanyansa shi d'aya,wasu daga cikin abokansu ko har tsiya suke masa idan sun ganshi shi kad'ai,sai dai ya fake musu da BB aiki ya tsare shi a office amma sun san babu yadda za ayi su ganshi shi kad'ai...
Haka har ranakun biki suka fara shigowa....

Kamar yadda aka shirya haka aka soma gudanar da events en ba tare da k'arya ko nuna su wasu bane,duk k'in KHUBRA na rashin son shiga taron jama'a abun ya gagara,kan dole take aiwatar da komai ba dan ranta na soba,duk inda ta juya jama'a ne daga ko wane sashi.A hankali saboda hayaniya da k'aran kayan kid'an wajen suka soma damunta nan ko ciwon kai yace bisimillah...
Duk yadda take ji ajikinta d'auriya kad'ai take amma sam tak'i nunawa mutane hakan.

*23/SEPTEMBER,2018.*

Rana bata k'arya akace sai dai uwar d'iya taji kunya,a yau ne dubban jama'a suka taru a babban masallacin na *UMAR BIN KATTAB* dake *ZARIA ROAD* dan shaida d'aurin auren,d'aurin aure mai cike da tarihi..

Shiga ta alfarma na hango manyan mutanen uku wanda duk ya gansu a wannan lokaci tabbas sai ya san sun bayyana a gurin,manyan ALHAZAWA da a wannan lokaci tarihinsu da labarinsu ya baza birni da k'auye cikin lokaci k'alilan,wanda dama dayawa daga cikin mutane sun san da su a wancan zamanin na baya sai a wannan lokaci labarinsu yafi yin shura...
Fuskokinsu kad'ai mutum zai kalla ya shaida tsantsan farin ciki dake shimfid'e samansu,jama'a sai gaisawa suke da su suna musu fata da kuma sanyawar alkhairi.

Da misalin k'arfe 10:30am KHALEEL na hango cikin shiga wacce take bayyana eh lallaifa wannan young man en akwai wani abu dake faruwa.
Kallo d'aya tak ya isa mutum ya gane hasken dake tare da shi a ranar wanda a dai² lokacin ya juya yana kallon BB daya koma kamar ba shiba,shigansu iri d'aya komai dake sanye jikin d'aya tabbas idan ka kalli d'aya zaka ganta ba aikin kowa bane sai BB dan shi yayi iya yinsa na ganin ta faru,kallon juna suka yi,sannan suka yima juna murmushi kafin suka fice a tare,BB ke driven inda ango KHALEEL ke gefensa
"Wai MAN lafiyarka k'alau kuwa...."

Kallonsa yayi ta cikin bak'in glass dake fuskarsa kafiin nan kuma ya furta
"Me ka gani kuma...?"
Chapter 60 · 0% Book details