← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 86

Sashe 38

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin maganar BABA ABDU yayi kamar zubar wuta a jikinsa,cikin zuciyarsa yana jinjina kalaman da zai sanar da BABA a wannan halin da yake....
Sai da BB yayi k'arfin hali sannan ya fara magana,duk wani labari daya shafesu tun daga barin garin har zuwa wannan lokacin da yake zaune a gabansa bai b'oye masaba ya sanar da BABA ABDU,amma banda labarin b'atan ASHNA...

Al'ajabi da mamakin abunda ya faru cikin labarin da BB ya sanarma da BABA ABDU yasa shi kuka yana fad'in
‘’Lallai wannan al'amari daya faru tabbas muk'addari ne daga Allah,Allah ya tsara haka sai ya faru daku a rayuwarku,babu kuma wanda ya isa ya tsallake K'ADDARA.....
To amma ina ita mahaifiyar taku da sauran y'an uwanka da kace suna nan?
A wane hali suke yanzun?kuna tare gaba d'aya a guri d'aya ko kuwa?"
Duka tambayoyin BABA ABDU ya jerowa BB ba tare da ya jira ya amsa wasu ba....

"Ehh!BABA muna tare dasu can garin kano,sai dai kuma ita mahaifiyar tamu a halin yanzun bata da cikakkiyar lafiya,wanda ta kaiga har bata iya shaida wanda yake kanta"

"Subhanallah!wannan wane irin ciwone haka ya sameta?"

"BABA muma dai gaskiya bamu san wane irin ciwo bane,tun da likita ya shaida mana suna buk'atar ganin wani babba daga zuri'ar mu dan suyi magana dasu,to mu kuma babu kowa a tare da mu,shi yasa muka yanke hukuncin nemanku mu sanar muku halin da muke ciki"....

Dattijon dake gefe ne ya mik'e tsaye cikin fushi
"Wato da can baku neme muba sai yanzu da al'amura suka gama cukurkud'e muku kuka lallab'o gurinmu....
To kuma tashi ku d'ebi tsummokaran jikinku ku k'ara gaba mu ba abunda zamu iya yi muku a halin yanzu,muma fama muke da namu mahaifin kun dai ga halin da yake ciki...
Saboda haka maza ku tashi ku koma babu abunda zamu iya yi muku a halin yanzu,ita mahaifiyar taku zata iyayi muku komai ai na rayuwa ciki kuwa harda samar muku wasu dangin uban‘’....

Jikinsu duk yayi sanyi da jin furucinsa,suna sauraron yadda yaketa fad'a..
Shi kuwa BABA ABDU yana zaune yana kallon ikon Allah yadda d'an nasa yake ta fad'a kamar zai ari baki...
Murmushi yayi ya sake kallon d'an nasa da ya kasa yin shiru har zuwa lokacin,ganin bai gane me shirun nasa yake nufiba ne yasa shi yin magana
"Ya isa haka KHALEED"

Kallon-kallo sukayi tsakanin KHALEEL da BB,sannan kuma suka juya suka kalli mutumin dake fad'a ganin yayi shiru a lokacin,suka sake kallon BABA ABDU...

"Banda abunka KHALEED ina kai ina fad'a ga wad'anda basu da laifi?ko ubangiji idan muka masa laifi yana hak'uri damu ya kuma gafarta mana....
Kuma ubangiji baya tab'a kama bawa kan laifin da ba nasaba"

"Kayi hak'uri BABA raina ne ya b'aci shi yasa‘’

'Dan murmushi yayi sannan yayi gyaran murya
"Allah sarki MURJA Allah ya bata lafiya,shi kuma SAFWAN idan yana raye Allah ya bayyana mana inda yake"
Gaba d'ayansu suka amsa da ameen...

"Da gani dai wannan da yake zaune kusa dani shu ne KHALEED ko?"
KAKA ya tambaya yana murmushi shima,duka suma suka murmusa tare da amsa masa,juyawa yayi ya kalli KHALEEL
"Shi kuma wannan abokin nawafa?
Ya tambaya yana y'ar dariya
"KHALEEL suna na KAKA"

"Ahhhh!IBRAHIM KHALEEL kenan...
To Allah ya muku albarka da kuka zo nemanmu bayan lokaci mai tsaho".....

"KHALEED kasa a kira sauran y'an uwanka da mutanen gida yanzu ina son ganinsu"
BABA ABDU ya fad'a yana kallon d'ayan dattijon dake tsaye har lokacin,da sauri ya fita don aiwatar da sak'on BABA....

Bayan wucewar wani lokaci cikin turakar ta d'inke da jama'ar gidan manya da yara kowa ya matsu yaji me BABA zai sanar musu haka mai muhimmanci da ya tarasu gaba d'aya....

Sai da yayi gyaran murya yana jingine jikin pillor sannan ya kallesu d'aya bayan d'aya ya fara da fad'in
"Alhamdulillah da Allah ya nunamin wannan rana da na jima ina sauraron zuwanta a tsayin rayuwata...
Dalilin daya sa na taraku a nan ba komai bane face sanar daku wani muhimmin al'amari game da SAFWAN da iyalinsa,wanda wasu daga cikinku sun sanshi wasu kuma basu saniba"......
Take BABA ABDU ya jaddada labarin SAFWAN da iyalinsa ya sanar dasu da duk wani abu daya faru dashi bayan barinsa garin kamar yadda BB ya sanar da shi,yana gama basu labarin turakar tasa kowa dake ciki ya d'auki salati,masu kuka nayi masu jinjina lamarin nayi...

Bayan wani lokaci aka samu kowa yayi shiru sai jimami da kowa keyi da abunda ya faru...
BABA ABDU ya kalli BB dad'an murmushi a fuskarsa yake fad'in
"Kaga wannan?" ya nuna dattijon daya rako su d'azun
"Sunan sa KHALEED shi ne babba cikin y'ay'ana,sannan wannan shi kuma sunansa SULAIMAN,sai kuma wannan AYUBA kenan,sannan sai mahaifinka,daga shi kuma sai k'anwarsu da ta rasu shekaru bak'wai da suka wuce wato FALMATA"...

Wad'annan kuma ya nuna matan dake gefensa matansu ne,haka yayita nuna masa su d'aya bayan d'aya yana gabatar dasu a gurinsa,sannan shima ya gabatar da shi a matsayin d'an uwansu da basu saniba sai wannan lokacin....

Hira sosai tsakanin mutanen parlor'n anata dad'a gaisawa,sannan BABA ABDU ya sallamesu kowa ya fice aka barsu daga shi sai su BB zaune cikin turakan nasa...
Nan da nan aka tashi girki na musamnan a gidan saboda zuwansu,tarba da karamci kam sun samu gurin mutanen gidan wanda basu tab'a tunanin samunta daga gurin mutanenba.....

*2 DAY'S LATER.*

Kwanaki biyu kenan da zuwansu garin wanda suke sa ran a washe gari za suyi haramar barin garin idan Allah ya kaimu ko dan sanin yanayin da jikin MAMA yake a halin da take ciki ko an samu ci gaba ko kuma akasin haka Allah shi ne masani...

Farin ciki kam suna cikinsa tun daga zuwansu garin har zuwa wannan lokacin,kullum cikin hira suke da KAKA da kuma su BABA KHALEED suna dad'a basu labarin zamansu da ABBANSA,wani abun idan sun fad'a sai dai suyi dariya wani ko har da k'walla saboda rashin tabbas akan ABBA'N yana raye ko akasin haka.....

Yau tun safe suke shirin komawa KANO kamar yadda suka sanar da KAKA dama kwana 3 suka zo da niyyan yi....

Sai da ya had'asu yayi musu nasiha sosai kan su rik'e zumunci...
Sunyi masa godiya tare da alk'awarin dawowa nan da wani lokaci ba mai nisaba...
Sosai yaji dad'in hakan,sannan yayi musu alk'awarin da sun koma zai turo su BABA KHALEED suzo su dubasu...

Sunji dad'i sosai da yadda aka karb'esu,sannan sukayi sallama dasu suka d'auko hanyan dawowa KANON DABO......

《《》》

Kimanin kwanaki biyu (2) KHUBRA bata samu ta fita gurin sana'ar taba kamar yadda ta saba...
Duk jikin ya takura mata da ciwo a kwanakin da yasa ta kasa fita,dalilin da ya sa BABA ZUWAIRA ta dad'a sa ido kenan kanta tana dad'a bata kulawa ta musamman saboda yadda take ganin jikin nata....

Yau ta tashi jikin da sauk'i sosai har tana iya yin komai da kanta....

Tashinta da sassafe ta share gidan ta gyara ko ina sannan ta shiga tayi wanka,ta fito kenan daga toilet en BABA ZUWAIRA itama ta shigo gidan d'auke da robber a kanta...
Sororo ta tsaya kallonta tana kuma kallon gidan,dan tana da tabbacin ita tayi wannan aiki...
K'arasowa tayi cikin gidan tana son yin magana...

"Sannu da dawowa BABA"

"Yawwa y'ar nan"
Ta fad'a tana bin KHUBRAN da kallon mamakin yadda ta ganta,bayan a kwance ta barta ta yaya kuma yanzun zata ganta ta mik'e kamar ba itaba...

"Sannu kin tashi?"

"Ehhh!wallahi BABA,ai jikin da sauk'i sosai har ina jin yauma zan iya fita"

Da sauri BABA ZUWAIRA ta katse ta tana fad'in
"Haba haba KHUBRA me zai hana ki k'ara hak'uri zuwa jikinki ya sake warwarewa,in yaso sai ki fitan ko kuwa?"

Cike da tab'ara irin ta y'ay'an fari kuma na k'arshe ta hau buga k'afa tana fad'in
"Ni wollahi a'a ban yardaba,nafa samu sauk'i sosai"

Kallonta BABA ZUWAIRA take tana sake bud'e ido tana kallon ikon Allah
"To ai shi kenan tunda kin dage Allah ya bada sa'a,kuma Allah ya k'ara sauk'i kinji"

Tsalle ta hau yi sosai tana ta murna BABA ta amince mata zata koma gurin sana'ar tata....

Cikin zumud'i ta hau shiryawa,yau da yake ita take son fitan bata b'ata lokaciba tayi ta gama shirinta,sannan tayiwa BABA ZUWAIRA sallama,dai² lokacin itama ta gama shirinta tana jiran al-majiran da zasu d'ibar mata kayan abincin zuwa bakin kasuwa....

Tafiya take cike da kuzari had'e da karsashi saboda yau kam tana jinta cikin k'oshin lafiya,sai dai d'an abunda ba a rasa ba da yake damun zuciyarta....
Har ta k'arasa bakin rafin ta d'ebo ruwa,ta kuma juyo don komawa cikin gari,tana tafe ta kare kanta da hat ta gargajiya saboda rana da ake tsulawa ga zafi.....
Yayinda wani gefen na sararin samaniya ya had'a hadari wanda yake ta gangamowa lokaci guda har garin ya had'e,da alamun yau kam za a iya dacewa da ruwan sama....

Wani iska ne ya taso mai k'arfin gaske,wanda sakamakon haka yasa wasu daga cikin mutane suketa guje-guje,bayan k'uran ya lafane kuma wani iskar cike da yanayi mai dad'i ya sake tasowa...
Cikin nutsuwarta take tafiya tana kuma ci gaba da tura kuranta ita d'aya a hanya....

Wani bak'in PRADO ne ya yanko kan kwaltan da mugun gudu sosai,dai² kafin motan ya k'araso inda take aka tsaya,tare da jan brake da k'arfi wanda ya bada wani mugun sauti ji kake KUUUUUUUUUUUU!!!...............

*_~KEEP FOLLOWING.....~_*

*~#TEAM KHUBRA.~*

*_REAL SMASHER._*
💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*2/ʝųlყ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
_Jinjina ga d'aukacin mabiya novel en *"Y'AR GARUWA"* a duk inda kuke ku en masoyanane na hak'ik'a,ina godiya sosai da k'aunar ku gareni Allah ya barmin ku a duk inda kuka kasance ina al'fahari da ku.._
*~__________________________~*
_Mun gani kuma mun yaba,danko hausawa na cewa "yaba kyauta tukuici" tabbas garemu muma hakan take,sanin masoyi sai Allah *CWEET LEEMA* muna godiya tare da jinjina gareki lallai ke d'in ta daban ce,ki jima kiyi k'arko a kullum kuma a ko ina SMASHER da HUBBEEY naki ne ke d'aya,Allah ya bar mana zumuncinmu daga nan har a Al-jannah muna fatan ci gaba da kasancewa tare.._
*~__________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*3⃣9⃣*
Chapter 38 · 0% Book details