← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 86

Sashe 56

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ABBA'N KHUBRA ya kalleshi yana murmushi yace
"Fad'i duk abunda kake so ni kuma in sha Allah idan baifi k'arfina ba zanyi maka"

Murmushin shima ABBA yayi sannan yace
"Ai nasan baifiba ma,amma dai bari mu gani.......Ba komai zan fad'a ba dama illa ina so nace maka.....tunda Allah yasa yanzun baka da kowa a garin nan mai zai hana bazaka bimu mu koma can birni tare ba,kaga kaima zakafi samun kwanciyar hankali ace kana ganin y'arka a kowane lokaci,behind ma kuma yanzun ba iyali gareka ba,sannan banajin a garin nan kana da wani d'an uwa ko kuwa me kuke gani...?"

"K'warai wannan maganar da kayi nima Allah ne yasa ban yitaba amma nima hangena kenan"
ABBA'N KHALEEL ya fad'a yana murmushi

Ga ABBA'N KHUBRA kuwa yaso musawa buk'atar tasu ganin yadda suka jajirce yasa shi amincewa..
Kowa ka kalli fuskarsa cikin mutanen gurin babu komai samanta face farin ciki da annashuwa.

Bayan wucewar wani lokaci komai ya lafa an kuma gama yanke shawara game da hukunci,shirin tafiya ya kankama in da ABBA ya kammala had'a kayansa aka sasu a mota,gaba d'aya sun mik'e da niyyar kama hanyan komawa inda suka fito..
Suna shirin fita ZUHRA ta kalli ABBA tana fad'in
"ABBA ai kunyi mantuwa..."

Duka suka juya suna kallonta da neman k'arin bayanin mantuwar da sukayi
LADIYO ta nuna musu dake cikin rumfa sai kallonsu take da fuskar munafukai musammanma KHUBRA data koma kamar baturiya dan kyau data k'ara,sai lokacin LADIYO ke nadama game da dana sanin bata aikata abunda tayiba duba da yadda KHUBRA'N ta koma,lokaci guda ta bayyanar mata a matsayin y'ar dangi mai cikakken asali,komawa tayi wata kalar tausayi ganin irin kallon da mutanen gurin ke mata.

A fusace ABBA'N KHUBRA yayo kanta yana fad'in
"Bak'ar munafuka al-gunguma kinzo kin ficemin a gida ko kuwa saina raunataki"
Wani ice ya rarumo faskare guda ya dumfarota da shi,da sauri ABBA'N BB ya rik'e shi yana murmushi had'e da girgiza masa kai
"Haba MALAM BUBA me zai kaika aikata abunda ko a baya baka aikataba,kana so ne ka k'arasa gawar da ba taka bane?...."
Da sauri kuma ya tsaya harara ya aika mata sannan ya jefeta da icen,aiko nan ta juya da niyyar guduwa d'aki icen ya sauka a tsakiyar bayanta ji kake timmm,wani ihu ta kurma su ko su ZUHRA,ASHNA,FATAHIYYA me za suyi inba dariyaba,tsabar mugunta harda rik'e ciki,BB ya kallesu yana fad'in
"Dillah ku rufawa mutane baki,ko meye abun dariya a nan kuma ohooo...."
Kyal-kyalewa KHUBRA tayi da dariya dan ita sai a lokacin da yayi magana tata dariyar tazo,nan ta shiga dariya saboda mugunta irinta KHUBRA baya ga hawaye harda durk'usawa a k'asa tasa hannu ta dafe gefen cikinta..
Kallonta yayi yana dad'a d'aure fuska,lallaima yarinyar nan ta raina shi,banda iskanci shi zai musu magana ta tsaya tana masa dariya,lallai ko zata bawa mutanen garinsu labari idan suka had'u..
Lower lip nasa ya cije yana kallonta k'asa-k'asa fuskar nan a had'e kamar bai tab'a dariyaba,ZUHRA data kalli yanayinsa da sauri ta dunguri KHUBRA tana nuna mata BB,d'an bakinta ta murgud'a k'asa-k'asa tayi magana
"Ina ruwana to da shi....."

Abunda KHUBRA bata saniba tsaf BB yaga abunda sukayi kuma yaji maganar da tayi,kwafa yayi had'e da girgiza kansa..

"Kinzo kin fice ko kuwa sai na danganaki da gaban mai gari?..."

"Wollahi MALAM ban san ina zaniba bani da kowa sai MA'U ita kuma ban san ina takeba a fad'in duniyar nan,dan Allah ka rufamin asiri dan sonka da manzon rahama kada ka koreni,idan ka koreni ina zani.....?"

"Ke dallah dakata ina ruwana da inda zaki?? ni yanzu bani da alak'a ta kusa ko ta nesa dake,tun wuri kuma ki zo ki fice kafin na fusata jikinki ya kuma gaya miki ina fatan kinji dai abunda na fad'a miki....."
Kuka wiiwii take tana bashi hak'uri amma bai biya ta kantaba,nan suka fice daga gidan,haka LADIYO ta k'ullo y'an kayanta ta fito tana kallo MALAM ya sawa gidan pad lock ya rufe gidan,sannan suka d'au hanyan komawa....

Maimakon su d'auki hanyan KANO sai gani suka yi BB dake driving ya yanke hanya,cikin garin DUTSE ya nufa,babu wanda yayi magana cikin iyayen da suke zaune,a tunaninsu a kwai abunda zaiyi a garin,basu tsinci kansu a ko inaba sai k'ofar gidan KAKA,parking yayi sannan suka fita gaba d'aya da masu son tambaya duk sun yi shiru,jikin ABBA'N BB da kuma ABBA'N KHUBRA duk yayi sanyi saboda su kam ko daga mafarki suka tashi aka kawo su nan sun gane ko ina ne,su kuma y'an matan babu wacce tayi tunanin wani abu game da gidan da suka zo.
BB da KHALEEL na gaba,basu tsaya shawara ba suka shiga gidan su KHUBRA na bayansu har cikin gidan,su ABBA na waje suna shawaran yadda zasu fuskanci KAKA dan dukansu masu laifi ne a gare shi,har basu sanma y'ay'an nasu sun shigeba.

Da sallama suka shiga kamar zuwansu na farko haka tsakar gidan yake cike da mutane sunata aikace-aikacensu game da hirarraki irin na mutanen k'auye,bayan sun gaisa da matan gidan kai tsaye suka nufi turakar KAKA dan sun san kam yana nan kamar yadda take a wancan lokacin,da shigarsu cikin turakar suka tarar da KAKA na karatun AL-QUR'AN saboda hadda gare shi,sai da ya kai aya sannan ya amsa musu sallama'n da sukayi,nan BB da tsokana yace
"Sadak'allahul-aziiym tsoho mai ran k'arfe,ashe a kwai tsohuwar hadda bata guduba..."
Dariya KAKA yayi sannan yace
"Yo an fad'a muku haddar da mukayi irin taku ce ta yanzu,mu gwagwarmayar da mukayi ai ko rabi baza kuyiba....Idan kuma ka musa to mu gwada mu gani waye zai nasara..."

Gaba d'aya suka sa dariya har y'an matan sannan suka gaisa,kallon y'an matan yayi yana murmushi kafin yayi magana su ABBA suka shigo da yake ABBA'NSU BB ne a gaba hakan yasa KAKA baiga na can bayaba,kallon ABBA yayi yana murmushi sannan ya fara magana
"Idonka kenan ko SAFWAN..."

Sunkuyar da kai ABBA yayi k'asa ba tare da yayi maganaba

"Kayi hak'uri BABA ka kuma yafemin dan Allah,komai daya faru nima ba a son raina ya faruba...."

"Ai shi kenan Allah ya yafe mana baki d'aya...."

Gaisuwa ta musamman akayi ga kaka,nan KAKA ya sake kallon BB yana fad'in
"ABOKINA wad'annan y'an matan kumafa ?"

Dariya BB yayi dan yasan da shi yake
"Baka sansuba ko...?"

"To banda abunka da na sansu zan tambaya ne.....?"

Gabatar masa da su yayi a matsayin jikokinsa da bai saniba sai yanzun....
Dariya KAKA yana kallonsu duka,ABBA ya kalleshi yaga yana kallon KHUBRA,d'an murmushi yayi yace
"BABA ka santa ne....?"

"Gidanku SAFWAN ni kuma na zama abun tsokana ne kam a gurinka?"

"A'a BABA naga kana kallonta ne kamar ka santa..."

'Dan murmushi ABBA yayi sannan ya kalli KHUBRA dake murmushi ya kuma kalli KAKA yace
"To tunda ka santa fad'i wace ce....?"

Bud'ar bakin KAKA yace
"Yo wannan kam duk wanda ya kalleta ya ganka ai yasan y'arka ce ba sai an tambayaba....kuma har mene abun wahala anan da zaku sani gaba kai da d'anka daga zuwanku,ce muku akai bazan ganeba ne...?"

Dariya suka sa mishi saboda paul daya buga gurin fad'in ko wace ce
"Haba BABA ka dai sake kallonta sosai dawa take maka kama"

Sake kallonta BABA yayi sannan ya kalli ABBA yace
"Nifa bana son shegantaka yo to dawa take kama idan ba da kaiba...."

Sai da suka gama wana shi sannan ABBA yayi gyaran murya,duka suka juya suna kallonsa
"BABA dan Allah duk abunda zaka ji a yanzu ina so ka maida shi ba komaiba,kayi hak'uri ka yafewa wad'anda suka maka laifi,nasan kasani sai dai tunatarwa dan Allah BABA..."

Murmushi KAKA yayi masa ba tare da yayi maganaba,kallon KAKA ABBA yayi sannan ya kalli KHUBRA a hankali yace
"BABA wannan da kake gani tabbas y'ata ce amma bani na haifeta ba.....jikarka ce ta wajen y'arka FALMATA....."

KAKA dake kwance idan zai tashi sai an taimaka masa jin an ambaci FALMATA bai san lokacin daya mik'e zauneba da kansa.

"Ka ce me SAFWAN...? Shin kam yaushe na fara wasa da kai kamar haka?..."

"BABA sam cikin maganar da nayi babu wasa a ciki,jikarka ce y'ar wajen FALMATA..."
Chapter 56 · 0% Book details