← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 86

Sashe 45

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sosaima kuwa sam tunanina bai kawomin haka ba shi yasama ban maka maganar ba"

Sai da suka jima a gurin suna shawaran yadda zasu fuskanci ABBAN KHALEEL idan ya diro k'asar tun bayan da ya bar k'asar shima akan wani project da yaje k'asar Singapore na tsawon shekaru uku wanda ya rage masa y'an watanni ya kammala.

"To amma MAN baka ganin gara tun yanzun mu tuntub'eshi da maganar,kaga idan suna tare nema zai iya convincing nasa su dawo tare ko kuwa me kace?"
BB yayi maganar had'e da kallon KHALEEL yana jiran jin me zai ce masa
"Ehh!kumafa shawaran da ka bayarma idan muka bishi hakan zaifi mana"

Sai da suka kammala shawaran sannan KHALEEL ya fiddo phone ensa yana dannawa alaman neman wani abu...

《《》》

Shigowarsa gidan zuciyarsa ta sake yin k'unci saboda tunawa da abunda ya faru kwanaki biyar da suka wuce,duk asuba anayin kiran sallah idan ya fice baya tab'a shigowa gidan sai bayan dare ya gama tsalawa alamar babu wanda zai san da zuwansa kenan yake shigowa.
Shigowarsa kenan kamar kullum yana k'ok'arin wucewa yaji an rik'o gefen rigarsa,da mugun fushi ya juyo dan ganin waye zai aikata masa haka.
LADIYO ce ta rik'e shi sai girgiza take alamar dake nuni da yau ba zaman lafiya kenan,fisgewa yayi tare da nunata da hannu,ba tare da yayi magana ba ya juya zai bar wajen,sake rik'oshi tayi cikin b'acin rai wanda yafi na farko yana juyowa ya d'auketa da mari.

Dafe kuncinta tayi tana kuma kallonsa,cikin kaushin murya had'e da sake nunata da hannu
"Ke dabbar wace duniyar ce da har zaki rik'e ni? ko kuwa kina tunanin nima baho ne irinki da zaki aikata abu kiyi tsammanin ban saniba
To bari kiji duk abunda kike aikatawa ina sane da halin da kike ciki,sai dai abu biyu zuwa uku zan fad'a miki
Na farko dai zan fara miki da Allah ya isa da har kike cin amanata kuma a haka kike tunanin ban saniba,kin munafurce ni sannan kin ci amanar hakkin aure to kije ke da Allah,kuma da sannu zaki ga sakamakon tozarta aure da kikayi.
Abu na biyu da zan fad'a miki shi ne,tun wuri kuma muna shaida juna duk inda yarinyata take kiyi gaggawar nemo min ita tare da damk'ata a hannuna,idan ba hakaba zan sauya miki hallita sa'annan in damk'aki a hannun hukuma.
Abu na uku da zan shaida miki kuma na k'arshe shine daga rana irin ta yau ni MALAM BUBA SA'ADU na sake ki saki uku babu ni babu ke,zaki bar gidannan daga ranar da yarinyata ta dawo hannuna ina fatan kin gane ko?"

"Wayyooo Allah ni LADIYO wallahi MALAM baka isa ka sake niba na rantse sai ka zauna dani"

"Ke dakata da Allah idan kin manta abunda ya faru shekaru sha tara da suka wuce ni ban manta ba kin gane ko,ni bani da lokacin b'atawa bare har na tuna miki d'anyen hukuncin da kika sani aikatawa saboda sharri da kuma kaidi irin naki"
Yana kaiwa nan a zancensa ya fisge rigarsa tare da wucewa ya barta a nan tsaye tana faman taraddadin da tasani bata aikata masa abunda tayi ba tun farko yau ga shi abunda hakan ya jawo,tunani ta lula kan maganarsa....

《《》》

Sabuwar kulawa KHUBRA ke samu daga gurin MAMA dan yanzun kam ta mai data kamar y'arta data haifa tsakaninta da su ASHNA yanzun babu wata k'iyayya,sai dai kuma har yanzun ta kasa sakin jiki da su kamar yadda su en suke mata shishshigin ganin ta sake da su.

Ihu suke tayi suna murnan zuwan UMMI da tazo yanzun babu jimawa,bayan sun gaisheta kowannensu suka fashe daga parlor,hira sosai suke tsakaninsu irin ta k'awaye kamar ba sune da suka jima basa tare ba.
"Nikuwa MAMA'N yara da wata alfarma nazo nema gurinki"
UMMI ta fad'a tana kallon MAMA dake zaune tana ta faman sakin murmushi kamar ba ita tayi jinya ba
"Haba UMMI'N yara wace irin al'farma kuma,ai tsakaninmu ya wuce haka,ki fad'i ko me kike so ni kuma in sha Allah babu abunda zaki nema ki rasa a gurina"

"To shi kenan tunda kince haka,dama ba wani abu bane illa ina so ki bani KHUBRA na tafi da ita gidana kinga tunda Allah yasa mukayi aure d'a d'aya kad'ai muka mallaka,ke kuma kina da y'ay'a da yawa,dan Allah ki taimakamin ki bani ita kada kuma kice a'a,saboda ina son y'a mace sai dai Allah bai azurtamu da samun hakan ba"
Shiru UMMI tayi tana sauraren MAMA da itanma dai shirun tayi,ko me take tunani ohoo,sai da ta sauke wani dogon ajiyar zuciya sannan ta fara magana
"To UMMI ni me zance a kan wannan maganar,ina ganin yaran nan ko da bana raye na tabbatar ke kad'ai ce zaki rik'emin yarana saboda haka ko dukansu kike so a halin yanzu ni babu abunda zance miki"

Dad'i sosai UMMI taji dan yadda MAMA tayi maganar ba k'aramin farin ciki tajiba

Suna cikin firan ne driver'n gidan yayi sallama had'e da sunkuyawa

"HAJIYA dama wani ne yace a fad'a muku kuna da bak'o idan kun bada izini zai shigo"

Kallon-kallo akayi tsakanin MAMA da UMMI cikin wani yanayi kuma suka furta
"Bak'o kuma daga ina haka?"....................

*Ku canki waye a waje yake neman izinin shigowa.....* ☺☺☺

_Kuyi hak'uri da wannan wollah mura ke damuna jikina duk a mace yake shi yasa na kasa yin typing en yadda ya kamata...Luv u oll._ ❤

*~#TEAM KHUBRA.~*

*_#REAL SMASHER._*
💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*12/ʝųlყ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~__________________________~*
_A kullum kuma a ko wane lokaci ina alfahari daku dan kun rigada kun zame min jinin jiki wanda idan babu ku to lallaine SMASHER bata tab'a moruwa,ina godiya sosai da addu'o'inku gareni,Allah ya bar k'auna.....#1❤ MY PEPs._
*~__________________________~*
_Fan's muna baran addu'anku akwai sister enmu da aka nema aka rasa dan Allah ku tayamu addu'a Allah ya bayyana mana ita.._
*~__________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*4⃣3⃣*

*K* allon UMMI MAMA tayi kafin ta had'iyi wani irin yahun wahala saboda gaba d'aya tunanin MAMA ya tafi wani nahiya daban.
UMMI ce ta kalli driver'n da yake jiran umarni har lokacin tace
"Kaje kace masa Bismillah! zai iya shigowa"
Da sauri ya fita don isar da sak'on da aka bashi.
Har bayan fitansa MAMA bata koma dai² ba saboda firgicin da take ciki wanda ya hanata magana.

Da sallama ya shigo cikin shiga ta kamala wanda idan har wanda ya sanshi ya ganshi a cikin wannan kayan zai iya tsammanin ba shi bane wani ne daban,sosai kyaunsa ya dad'a bayyana ga wani classy da ya k'ara,har k'asa ya sunkuya ya gaidasu sannan ya zauna a kan rug,k'afafunsa a tank'washe kamar mai d'aukan darasi,wanda bai sanshiba idan ya kalleshi a wannan shigan zai iya tsammanin dama can haka yake.
Shiru cikin parlor'n na wani lokaci,su kuma suna masa kallon rashin sani dan babu wanda ya tab'a ganinsa cikinsu bare ya shaida shi.
MAMA ce taga shirun yayi yawa ta fara magana da fad'in
"Samari daga ina haka mu nan babu wanda ya shaidaka cikinmu"

Kansa ya d'an sosa yana d'an inda-inda dan bai san ta ina zai fara maganaba,kansa a k'asa yana shirin yin magana su BB suka shigo shi da KHALEEL
"Da farko dai HAJIYA ni suna na *SADEEQ* wanda wasu daga cikin mutane ke kirana da *BIGGY* na zone domin baku hak'uri tare kuma da neman gafararku bisa abubuwan da suka faru a y'an watanni sannan kuma zuwa wasu satittika da suka shud'e"

Kallon mamaki duka suka bishi da shi,inda su KHALEEL suka nemi guri suka zauna don jin abunda zai biyo bayan zancen da yake yi.

"A da HAJIYA ni ban kasance cikin mutane masu tausayiba bare imani....."

"Subhanallah!" UMMI ta furta
"Kai kuwa wane irin mutum ne da har kake furta baka da imani,ka san kuwa ma'anar wanda aka ce bashi da imani?
A duk lokacin da aka cewa mutum bashi da imani to tabbas wannan mutumin baya cikin jerin mutane masu imani,saboda ko me ka aikata ka rok'i yafiya daga gurin mahaliccinmu sannan ka nemi yafiyar wad'anda ka zalunta,tabbas ubangiji zai gafarta maka dukkan zunubanka,ina fatan ka gane ko?"

Kai ya kad'a mata sannan idanunsa na fidda hawaye kamar mace yace
"HAJIYA sam abunda na aikata ba shi da alak'a da abunda kike magana,kamar dai yadda kikaji na ambata ni na kasance ina yin aiki na marasa imani,kamar kuma yadda na kasance cikin marasa tausayi had'e kuma da aiki ga mutane marasa imani"

Wani kallo gaba d'aya mutane hud'un dake cikin parlor'n ke masa mai wuyar fassara,gaba d'aya hankulansu na kansa basu da burin daya wuce jin cikakken labarin wannan SARK'AK'IYA.

Dad'a duk'ar da kansa yayi k'asa ya goge fuskarsa sannan yaci gaba
"HAJIYA ni da kuke gani a da na kasance cikin mutanen da suke yin *GARKUWA* da mutane domin neman wani abu ko kuma asasu sace wasu sannan mutane su yasar wani yanki daban
Idan baku mantaba a watannin baya kun nemi y'arku kun rasa wacce kuka jima kuna nema ba tare da kun gantaba
Sannan a weeks da suka shud'e kuka sake neman wata kuka rasa,wanda ita kuma ta dawo gida kimanin sati kenan da samunta"

"Kaii da Allah dakata kada dai kace mana kai ne k'asurgumin b'arawon da ka sacesu duka"

Ba tare da ya kallesuba ya kad'a kai,yin hakan babu b'ata lokaci KHALEEL ya kalli BB daya ke kallon wannan bawan Allah mai matuk'ar k'arfin hali.
"Ammafa kayi k'ok'ari kuma ya zama wajibi a jinjina maka saboda bajintar da kayi,a saboda haka ni kuma nayi tunanin karramaka ta hanyar baka lambar yabo..."

Da sauri KHALEEL ya kalli BB cikin fad'a yana fad'in
"Haba MAN wane irin bajinta kuma?.........wane irin kuma karramawa kake magana ga azzulumi irin wannan?wanda makomarsa bata wuce gidan sark'aba,irin wad'annan mutanen makomarsu ma yaci ace tafi haka muni saboda ayyukansu......"
Chapter 45 · 0% Book details