← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 86

Sashe 46

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya isa haka SON,me yasa zaka katse shi daga bayanin da yake yi bayan d'umbin nadama da yayi wanda har ya masa jagora akan yazo neman afuwarmu,ina ganin idan har ba dagaske yake ba babu abunda zai kawo shi gurinmu,mu bashi dama muji dame yazo tukuna kafin a yanke masa hukunci....."
Maganar da UMMI tayi ita tasa su yin shiru kowanne sai huci yake burinsu bai wuce a kyalesu su sab'a masa halittaba ko samu sassauci,idanun BB sun gama rinewa da b'acin rai ga tarin bak'in cikin dakatar da shi da akayi gurin hukunta wannan k'asurgumin mai laifin dake gabansa,kunnuwansa yasa hannu ya toshe duk dan kada yaji abunda ake fad'a idanunsa a lumshe kamar mai bacci haka ya jingina bayansa a jikin sofa...

Kallon matasan samarin BIGGY yayi da suke cike da zafin kai wanda a ganinsu idan har aka barsu da BIGGY to babu abunda zai yi saura a jikinsa..
Sai daya sake kallon mutanen parlor'n sannan yaci gaba
"Bisa wannan kuskure dana aikata a rayuwata kuma bisa ga dalilin had'uwata da d'aya daga cikin y'an matan dana sata zuciyata ta kasa nutsuwa wanda har tayi min jagora zuwa alkhairi,itace ta kawo haske cikin rayuwata wanda yayi sanadiyyar dana yanke shawarar dena aikata duk wani laifi dana ke tawa akan hakane na yanke shawarar dawo da ita gida....."
Daga nan ya kwashe duk yanda suka yi da ASHNA tun bayan daya sace ta da irin damuwar da ta shiga,har kuma yanda yayi nadama kan aikin nasa ya kuma dawo da ita a ranar da sukaje asibiti shi ne lokacin da suka tarar da MAMA'N ta samu sauk'i,sannan ya k'ara da yadda ya tafi ya bar asibitin wanda a ranar babu wanda ya kula dashi
acikin d'akin saboda yadda hankalinsu ya koma kan MAMA...
Shiru yayi bayan ya kai nan a zancensa yana jiran ganin matakin da zasu d'auka akansa.

"Alhamdulillah!da har haka ya faru kuma muna godiya ga Allah daya sa ka shiryu daga mugun aikin da kake aikatawa,abun farin cikine ace wani ya shiryu ta sanadinmu,wannanma kad'ai ya ishemu alfahari da har haka ta faru
Y'anzun shin kana da wata sana'a ne da za kayi bayan dena waccan mummunar sana'ar taka?"

"A'a HAJIYA amma dai zan ci gaba da k'ok'arin nema ko dan ganin ban koma wancan sana'ar dana bariba"

"To Alhamdulillah da haka ya kasance lallai wannan ya tabbatar mana da cewa da gaske kake yi ka tuba daga wannan d'anyen aiki,abunda zan maka albishir da shi shine idan har ka dena abunda kake gaba d'aya ka kuma yi min alk'awarin bazaka sakeba
Ni kuma in sha Allah nayi alk'awarin nema maka aiki,amma abunda nake son ji daga gareka.....shin kayi makaranta ne?"

Sai da yayi murmushin jin dad'i sannan ya furta
"Ehhhh!HAJIYA nayi karatu rashin aiki ne tun farko da kuma sharrin matar mahaifina ta d'orani a wannan hanyan tun bayan dana rasa mahaifana"

"Asshha! Allah ya kiyaye ashema ba hakanan ka fara wannan mummunar sana'ar ba,Allah ya tseratar damu daga sharrin masu sharri amma abu baiyi kyauba
Abun da nake so da kai yanzu shine ina so ka kawo min copy na takardunka nan da sati guda kaji ko,sannan kuma kasa a ranka gaba d'ayanmu mun yafe maka abunda kayi mana,Allah kuma ya yafe mana baki d'ayanmu...."

"Haba UMMI ta yaya zaki saurin amincewa da maganarsa daga fad'an magana har kin yarda,irin wad'annan mutanen wallahi munafukai ne akwai wani mugun nufi da suke zuwa da shi a zuk'atansu,sai su fake da neman yafiya nan ko wani abu suka hango shi yasa suka lallab'o da sun samu nasara zaki neme su ki rasa...."
KHALEEL ya k'are maganar had'e da zabga masa wata uwar harara,wacce shi kam BIGGY baima san yana yiba dan ko kansa a k'asa yake.

Hararar shima ya samu daga gurin UMMI sannan ta masa dak'uwa tana fad'in
"Ungo naka SON wato kai gaka sarkin fitsararru ko?da nace a bar maganar kai ne bazaka iya yin shiru ba kenan,kana gani d'an uwanka yayi shiru amma kai saboda futsara shi ne zaka ci gaba da magana ko?to Allah yasa na sake jin ka furta wata magana wallahi saina sab'a maka kaji dai na fad'a maka..."

Kame bakinsa yayi bai sake yin maganaba duk maganar da UMMI ke yi da BIGGY babu wanda ya kuma ko da tari a cikinsu,har suka kammala maganar da suke,godiya sosai BIGGY yayi musu sannan ya mik'e yayi musu sallama da niyyan komawa,babu wanda ya kulashi tsakanin BB da KHALEEL duk kuwa da yanda ya mik'a musu hannu da zai fita,haka ya fice jiki a salub'e dan sam bai ji dad'in yadda KHALEEL en yake aika masa da kallon tsanaba.....

Dai² bakin parlor yana shirin fitowa ta taho a guje tana waiwaye tana ihu da alama akwai wanda ta tsokano karo tayi dashi da sauri ta maida kanta dan ganin mene ta buga haka,idanunsa na kanta duk da lokacin da ya fito zuciyarsa babu dad'i amma yanzun kam da ya ganta yaji dad'i sosai wanda baya misaltuwa,a hankali ya furta
"BEAUTY......."
Saurin kallonsa tayi dan tunanin inda tasan mai wannan kamannin take sai dai ta kasa ganewa yanzun kam da yayi magana ta rigada ta gama gane ko waye shi en,da sauri ta mik'e daga jikinsa tana fad'in
"Kaiii ne?.......me kuma ya kawoka gidanmu?"

Dariyama tambayanta ta bashi a hankali kuma ya karkatar da kansa gefe cikin wani irin yanayi yake fad'in
"Neman yafiya nazo gurin family enki dama ke kanki"

Idanunta ta sake bud'ewa tana k'are masa kallo saboda yadda ya mata kwarjini a yau,kallon sama ba sosai take iyawaba,kanta a kasa zuciyanta na skipping,ga wani feelings da take ji tattare da shi a lokacin,maganar daya mata ne wancan ranar ya fad'o mata a zuciyanta ta furta
"Kenan dama maganar dayamin kan zai daina abunda yake yi gaske ne?........To amma wane azzalumi ne yasa shi aikata mana wannan rashin imanin.......?"

Duk maganar da ASHNA ke yi batayi tsammanin a fili take yintaba sai da taji ya bata amsa
"K'warai kuwa BEAUTY da gaske ne babu k'arya a ciki....Kina son ki san wanda yasani aikata hakan ne?"
Yayi tambayan yana kallonta
"A'a kawai dai nayi maganar ne amma ba haka nake nufiba"

'Dan murmushi ya sake yi sannan ya furta a hankali
"Noo!BEAUTY nasan kina son sani kawai dai kinamin alkunyane ko?"

Bata ce komaiba taci gaba da murza ring en dake yatsanta,shi dai BIGGY (SADEEQ) yana ta kallonta duk wani abu da za tayi ji yake tana k'ara burgeshi,musammama wannan y'ar kunya da take nuna masa.

"Shin kin san wata mata mai suna HAJIYA LAURA?"
Tambayar ta daki kunnen ASHNA wacce bata yi tsammanin jin hakanba,a firgice ta d'ago kanta tana kallonsa,idanunta ne suka cicciko da hawaye cikin rud'ewa tana inda-inda take shirin tambayarsa,ko kafin tayi magana har ya rigata ta hanyar fad'in
"To itace bak'ar azzalumar data sa muka sace y'ar uwarki wacce muka yar a k'auyen garin ZAKIRAI,sannan kuma ita ce wacce tasa muka sace ki akan wani buri nata da mu bamu saniba....."
Kafin ya kai k'arshen maganarsa tuni ASHNA har tayi fitar burgu ta fad'a cikin parlor tana rusa kuka mai ban tausayi.
Shi ko BIGGY dake tsaye ganin hakan da tayi yasa jikinsa dad'a yin sanyi,a hankali ya juya ya bar gidan,yana tafe yana tunanin halin da BEAUTY ke ciki...

Fad'awa'nta parlor tana gunjin kuka shi yasa BB bud'e idonsa d'aya yana kallonta,ko kafin yayi magana har sun tsinto maganar ASHNA cikin kuka tana bada labarin abunda BIGGY ya shaida mata yanzun.
Da sauri MAMA ta mik'e tana zunduma wani gawurtaccen zagi wanda gaba d'ayansu basu tab'a tsammanin jinsa daga bakinta ba,jikinta sai karkarwa yake kamar wacce ake kad'awa mazari haka ta hau sababi
"Lallai HAJIYA LAURA yau kam kin riga da kin gama janyowa kanki k'arshen bala'i,yau ni HAJIYA MURJA zan nuna miki k'arshen colour ena,saina bar miki darasi a rayuwa wanda ko sunana kika ji an ambata zai sa ki dinga gudu dan neman mafaka......ba dai ni kika tab'a ba shi kenan mu zuba mu gani shege ka fasa yau zaki tabbatar da kin tab'o ......... dodo
Maza ki shirya yau ga maza nan bisa kanki"

Gaba d'aya mutanen parlor'n sun shiga shock idan aka d'auke BB da ya sake maida eyes yayi closing,mamakinsu ya kasa b'oyuwa saboda kowa yasan yadda suke da HAJIYA LAURA duk wani tak'ama da take yi da bazar HAJIYA MURJA take taka rawa,lallai ko yau kam HAJIYA LAURA kin d'ebo ruwan dafa kanki......

《《》》

Tun bayan da MALAM BUBA ya gama kora mata jawabi take tsaye a nan inda ya barta k'afafunta duk sun mata nauyi wanda ta gagara d'agasu,a gurin ta zube hannunta a ka ta shiga rera kuka babu ji bare gani...

Haka MALAM BUBA ya shige d'akinsa nan ko ya shiga jero nafilfili yana dad'a rok'on Allah yafiya bisa kuskuren da ya tafka a baya,sai da dare yayi nisa sosai sannan yayi addu'a ya kuma kwanta yana mai dad'a yin tasbihi ga ubangijin sammai da k'assai.

Kwanaki sun dad'a jaa inda a kullum tashin hankalin LADIYO yake dad'a k'aruwa daga lokacin da aka ce mata dare ya kawo kai,zuwa yau kuma babu wani labari dangane da MA'U bare ita kanta KHUBRA da ABBA'NTA yasa LADIYO ta dawo masa da d'iyarsa kamar yadda ya bata umarni.

《《》》

Tun daga ranar da BIGGY yazo gidan har zuwa yau bai sake dawowa ba,wanda zuwa yau an kwashi kwanaki da dama ba tare da ya sake waiwayar gidan ba.

A b'angaren ASHNA kuwa ko wane dare da tunani da kuma mafarkin BIGGY take kwana kuma take tashi,ko wane motsawar second ji take kamar za tayi hauka saboda yanda zuciyarta ta damu da shi fiye da tunaninta,tun bata yarda da cewa sonsa take ba har ya kaiga yanzun ta amincewa zuciyarta da son da take masa..
Chapter 46 · 0% Book details