← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 86

Sashe 50

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune a guarding hannunsa rik'e da magazine,sanye da fara kar en singlet mai hannu sai farin 3quater,kamar wanda aka ce ya d'ago jin shigowan mota,bin motan yayi da ido,daga inda yake zaune yana hango duk wani abu da yake faruwa tsakaninsu,kallonsu yake zuciyarsa kamar zata fad'o dan tsaban tashin hankalin da yake ciki.
Idanunsa har sun soma chanja colour baya ga jinsu da yake suna masa zafi kamar an zuba masa chili a ciki,kansa ya kwantar a baya ganin hakan bai masa ba ya fice daga lambun yana nufan hanyan d'akin da KHUBRA ta zauna kafin b'acewanta,a hankali yasa hannu cikin aljihunsa ya fito da key en sannan ya bud'e k'ofan kamar wanda bashi da kuzari haka ya shiga had'e sa rufe k'ofan,d'akin yake bi da kallo duk tsayin lokacin nan d'akin bai yi k'uraba kamar dama can da mutum a ciki,komai tsaf a d'akin da alama dai BB na kula da d'akin,kwanciya yayi k'asa kan carfet kansa kuma ya d'orashi saman katifan,idanunsa da suka canja launi ya kulle har lokacin jinsa yake kamar ba shiba a fili ya furta
"Ya zama dole na d'auki mataki,idan ba hakaba komai zai iya faruwa....."

Kamar wacce aka cillo haka ta fad'o cikin parlor'n ko sallama bata iya yiba,akan BABA ZUWAIRA idanunta suka fara sauka da gudu ko ta fad'a jikinta,gaba d'aya kallon mamaki suka bita da shi ita ko kulawa da hakan bata yiba saboda yadda take a firgice sannan ga d'okin ganin BABA ZUWAIRA da suka had'e mata.
Dariya suka sa mata wanda ya jawo hankalinta garesu kallonsu tayi tana tsuke fuska kamar mai shirin yin kuka,MAMA dake zaune tana murmushi ta furta
"Ya isa haka nan kunga kada kusamin ita kuka kunsan dai hali ko?"
Like serious tayi maganan,dalili kenan sa yasa duka suka k'unshe baki amma duk da haka ba wai dainawa sukayi ba..
'Dan sakin fuska tayi sannan ta gaida MAMA da BABA ZUWAIRA dake ta faman shafa kanta tana murmushi..
Wuni guda cikin gidan amma sam basu ga BB ba,har suka tashi tafiya dan KHALEEL ma daya kawosu bai wani jimaba ya tafi sai yanzun da ya dawo d'aukansu,haka suka tafi basu sashi a idanun suba kuma cikinsu babu wanda ya tambaya yana ina..

********

Shiri sosai BB ya shiga yi cikin kwanakin ba tare da sanin kowaba dan ganin ya nemama kansa mafita kan abunda ke shirin faruwa da shi,a ganinsa hanya d'aya ce maganin wannan damuwan nasa.
Shigowarsa gidan kenan ya zube keys en a saman side drower had'e da wasu takardu,gefe kuma envelop ne sannan luggage daya gama zuba kaya cikinsu.
Tsayawa yayi yana kallon room en a hankali ya furta
"3 days to go...."

《《》》

Damuwa kam KHALEEL ya shigeta saboda rashin ganin aminin nasa duk kuma lokacin da zai je gidan sam baya ganinsa ko da ko zai wuni a gidan ba zai tab'a ganinsa ba,tun abun bai wani damunsa sosai har yazo abun na matuk'ar damunsa,waya kuwa ko da zai kwana yana kiransa bazai d'aukaba tun yana tura masa text har ya daina.
Yanzu'nma da yake zaune cikin parlor kiransa ya gama amma har ta k'araci kukanta ba'a d'aukaba,hak'uri ya bama kansa dan yasan ba d'aukan zaiyiba.
Yayi nisa cikin tunani UMMI da fitowarta kenan zata d'auka ruwa a fridge en k'asa ta ganshi zaune,kusa da shi ta isa sannan ta dafa shoulder ensa da yasa ya d'ago.
A hankali ya kalleta sannan ya k'irk'iro murmushi da bai kai har zuciba
"Lafiya kuwa SON kake....kwana biyu ina yawan ganinka cikin damuwa,kawai dai na kyaleka ne ko zaka yi hankalin sanarmin,amma shiru baka ce min komaiba na zuba maka ido naga iya gudun ruwanka ne kawai,me yasa kake sha'awar sama kanka damuwa?ko kuwa kana sha'awar wani ciwon ya kamaka ne?"
Kai ya girgiza mata,ajiyan zuciya yayi sannan a hankali ya furta
"Wallahi UMMI ni da KHALEED ne kwanakin nan sam na kasa gane inda ya dosa,idan na kirashi baya d'auka haka ko text na masa ma babu amsa,idan kuma naje gida nemansa bana samunsa,na rasa me yake damunsa da har ya kawo wannan chanjin a tsakanunmu cikin wad'annan kwanakin,na tambaya ko baya nan an cemin babu inda yaje yana garin, na rasa me yasa UMMI...."
Yanayin da yake magana ya nuna tabbas abun sosai yake damunsa.

"Tun tsahon wane lokaci hakan yake faruwa tsakaninku?"
UMMI ta tambaya idanunta kuma na kansa

'Dan d'age kansa yayi alaman tunani
"Ammmm!UMMI ina ganin kamar tun ranar dana miki tuni kan neman aurena da KHUBRA ne"

Shiru tayi tana tuna ranar da abunda ya faru tsawon watanni biyu kenan da faruwar hakan ai,yanayin da ya nuna har zuwa ficewarsa daga gidan,ita sai yanzunma ta sake yin wani hasashe kan hakan,d'an murmushi tayi sannan ta furta
"To Allah ya kyauta amma dai SON kabi komai a hankali kaji ko?Sannan ka tsananta addu'a kan abunda kake nema idan babu alkhairi a tsakaninka da abun cikin sauk'i ubangiji zai maka chanji mafi alkhairi kaji ko?...."

"To UMMINA na gode sosai,Allah ya barmin ke"

Kansa ta shafa tana murmushi
"Maza kaje ka kwanta kaji ko dare yayi,sannan kayi kuma addu'a kafin ka kwanta"

"To UMMI sai da safe"
Ya fad'a yana bin hanyan bedroom ensa,har ya b'acewa ganinta sannan ta juya tana girgiza kai alamar tausayi dan ta fuskanci abubuwa da dama na shirin faruwa
"Lallai ya zama dole na dage da addu'ah kan wannan rikitaccen al'amarin,Allah ya zab'a muku abunda yafi alkhairi baki d'ayanku......"

*2 DAY'S LEAP.*

Cab en ta parker a k'ofar gidan,cikin shiga ta alfarma kamar baturen daya fito daga k'asar amuruka jikin nan a murje kamar mai rayuwa cikin k'ank'ara,k'afarsa ya sako waje ko kafin ya k'arasa fitowa har cab driver'n ya gama fito masa da luggage's ensa dake bayan booth.
Sallamansa yayi sannan yaja luggage's en yana nufan get en gidan,kasancewar safiya ce sosai yasa ya tsaya a dai-dai k'aramar k'ofan knocking ya shiga yi saboda babu lallai ace mutanen gidan sun tashi a wannan lokacin..
Ya d'an jima tsaye kafin aka bud'e k'ofan,kallon tsoro game da mamaki BABA MAI GADI yake binsa da shi wanda yasa shi jaa da baya,murmushi mutumin yayi sannan ya shiga yana jaye da luggage's ensa,shi dai BABA gani yake kamar gamo yayi da wannan sanyin safiyar shi yasa ya kasa motsawa daga inda yake,wucewar mutumin kawai ya gani,faruwar hakan ke da wuya BABA ya shige d'akinsa,cikin seconds da basu fi 3-5 ba ya fito hannunsa d'auke da buta aiko da sauri ya fad'a toilet dake jikin d'akin nasa ta baya...

Kallon cikin gidan yake komai yana nan kamar yadda ya barshi sai dai gyara da gidan yake samu wanda ya hana shi tsufa,amma kam kamar yadda yake a wancan lokacin haka ya tarar da komai a mazauninsa..

Fitowansa kenan sanye da train suit da alama zai fita motsa jiki ne,shigowan mutumin yasa shi binsa da kallo tun daga nesa har ya dad'a matsowa kusa da shi kallonsa BB yake jikinsa duk ya saki saboda mutumin da yake gani gaba gare shi gani yake kamar mafarkin da ya saba ne yauma,murmushin da yayi masa ne yasa a hankali ya bud'e baki ya furta
"ABBA.............."

*~TEAM KHUBRA.~*

*_REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*19/ʝųlყ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*4⃣7⃣*

*M* urmushi ya sake yi masa da sauri kuma BB ya isa inda yake tsaye,hannu ABBA yasa ya jawo BB jikinsa,wani feeling's ne suka dinga sauka a cikin jikinsa wanda ya kasa bambance na mene ne a wannan lokacin,da k'yar BB ya iya komawa gefe sannan ya amshi luggage's dake hannun ABBA ya nufi hanyan komawa cikin gida.

A dai² lokacin MAMA,BABA ZUWAIRA,ASHNA da FATAHIYYA na kitchen kamar ko yaushe suna had'a break fast daya zama al'ada tun bayan barin su ZUHRA a gidan,duk safiya musamman idan akace weekends to tare suke shiga kitchen.
Karafniyarsu a kitchen en ne yasa BB yayi hanyan da sauri bayan ya ajiye luggage's en ABBA a gefe cikin parlor.

"MAMA zo kiga wani abun al'ajabi...."
Abunda ya fad'a kenan fuskarsa da matsanancin farin ciki,kamar zata tambayeshi kuma ta fasa,hannunta ta wanke sannan ta goge da duster dake saman k'ofa.
Fitowa tayi batayi maganaba,ba dan komaiba sai dan yadda taga fuskarsa a sake ba kamar sauran lokaciba da sam basa ganin sakin fuska daga gareshi baya ga haka kuma tasan abunda yake son nuna mata mai girma ne shi yasa tak'i yin maganar..

Tsaye yake ya juya baya hankalinsa nakan wani frame dake d'auke da photo'nsu dukansu sai dai babu HANEEF ajiki,a lokacin KHALEEFA ne k'arami.
Yanayin yadda yake tsaye ya juya baya ta kalla ita kam tasan ko daga mafarki ta tashi ba zata kasa gane shiba,jikinta a matuk'ar sanyaye taci gaba da matsowa,kaf jikinta rawa yake saboda bata gama gasgata zatontaba,ita kad'ai take fad'in
"Anya kuwa shi ne da gaske ko kuwa gizon da ya sabamin ne yauma.....to amma taya haka zai faru?.......idan har da gizo ne me yasa KHALEED zai kirani.....?"
Cikin wani salo ya juyo fuskarsa har lokacin cike da annuri daya gagara b'acewa daga samanta.
Still tayi a gurin bakinta bud'e saboda ganin mutumin da batayi tsammaniba a dai-dai lokacin da kuma bata tab'a tunanin faruwar hakan ba.
Chapter 50 · 0% Book details