← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 86

Sashe 48

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali KHALEEL ya juya yana girgiza kai,BB ya kalla ya wani basar kamar baya gurin,fuskar nan ya dad'a d'aureta kamar ba shiba ko lokacin da suka fito a mota dariya ya gama yi yana tsokanar KHLEEL amma yanzun ya wani had'e girar sama da ta k'asa.
Ci gaba da tafiya sukayi har lokacin kuma bai wani saki ransaba,cikin parlor'n babu kowa sai TV dake ta faman b'ab'atu ita d'aya,zama sukayi babu wanda ya kula wani a ciki,UMMI ta fito daga corridor en da zai sada ka da stairs en data sakko
"A'a SON ashe kuna nan..."

"Eh UMMI muna nan amma bamu jima muma da shigowaba"

"To yayi kyau kam Allah ya taimaka..."

"Ameen.......Ammmmm! UMMI gurinki muka zofa"
KHALEEL yayi maganar yana kallon BB da har lokacin bai yi maganaba tun bayan gaisuwa da sukayi da UMMI.
"Toh! ina saurarenku ai...Maganar mene kukayi shiru?"

Inda-inda KHALEEL ya fara ya kasa magana,kallonsa UMMI ta tsaya yi ganin ya kasa cewa komai ne tayi magana
"Lafiya k'alau kuwa kake ta faman inda-inda ka kasa magana?"

Kansa ya shiga sosawa wani kallo BB yayi masa mai wuyar fassara kafin ya sake d'auke kansa ya shiga danna phone dake hannusa kamar mai neman wani abu,sai dai maganar da KHALEEL yayi a dai² lokacin ta kusa tarwatsa masa lissafi a burkice ya kalleshi dan son tabbatar da abunda yake fitowa daga bakin KHALEEL en

"UMMI damafa kan maganarmu da KHUBRA ne nake son yi miki tuni,tunda ALLAH yasa an ganta UMMI mai zai hana ki sake tuntub'ar MAMA da maganar,kinga idan ABBA ya dawo sai ayi maganar auren ko?"

Dariya tayi na jin dad'in maganar da yayi mata cike da farin ciki ta furta
"SON kenan banda abunka wannan maganar itace zata sa ka tsaya kana min magana kamar wani mara gaskiya,ka kwantar da hankalinka indai wannan ne,ina so ka sa a ranka kamar nayi mata maganar kuma kamar anyi an gama kaji koh?"

"Yawwa UMMINAH shi yasa nake ji dake wollahi,ni iya hakama yau kam kin gama min komai,na gode sosai UMMINAH"

Hankalin BB idan ya kai million a wannan lokacin to ya kai k'ololuwa gurin tashi,shi kad'ai lokaci guda har ya nemi farin cikinsa ya rasa,zuciyarsa tayi duhun da baya iya gane me suke cewa a lokacin dan gaba d'aya kunnuwansa suka tafi yajin aiki na wucin gadi,bai san lokacin da ya mik'eba ya shiga neman hanyan fita daga parlor'n,duk maganar da suke masa babu wanda ya iya kulawa haka ya fice motansa ya shiga ya fisgeta fiye da lokacin da yazo gidan,tuk'i kawai yake wanda baimasan inda yake nufaba ikon Allah ne kad'ai ya kaishi gida,MAMA dake parlor taga shigowarsa tana masa magana bai san me take cewa ba bare ya bata amsa,ido itama ta zuba masa har ya wuceta yabi corridor en da zai sada shi da bedroom,da k'arfi yayi banging door en.
A saman bed en ya zube zuciyarsa ta gama yin duhun da baya gane komai,da k'arfi yake sauke ajiyan zuciya wanda daga ji kasan bana lafiya bane,idanunsa ya runtse hango lokacin da KHUBRA ta rik'e hannun KHALEEL yayi da yadda take narke masa fuska tana shagwab'a wani b'acin rai ne ya dad'a kawo masa ziyara da ya dad'a hasala shi take ko ya bud'e idanunsa da k'arfi,gaba d'aya d'akin sai juya masa yake yi.......

《《》》

"Ina kika shiga munafuka maza fito dan yau kam ko ani ko ake,imma dai ki nemomin y'ata ko kuma yau na tona miki asirin abunda kikayimin sannan kuma na kaiki gurin mai gari a gaban dubban jama'a nasa a yanke miki hukuncin da bakiyi tsammaniba"..

LADIYO da ta b'uya a d'akinta jin shigowar MALAM en ne dama yasa ta zurawa a guje tayi cikin d'aki sannan ta k'ara da rufe k'ofar d'akin nata duk a ganainta ta gujewa had'uwa da MALAM en kan wannan maganar ta al'janar y'ar tasa..
A hankali ta bud'e k'ofar ta fito jikinta a salub'e kamar kazar da kwai ya fashewa sai sink'e kai take yi.

"Munafuka algunguma kuma kina jin tsoro ne dama?
Da kina tsoro ai da baki aikata duk wani tuggu da kika shiryaba amma kije ke da Allah,sannan ki sani nan da sati guda na baki duk inda KHUBRA take ki gaggauta nemomin ita idan ba hakaba kuma......"
Yayi k'wafa kad'ai tare da shigewa d'akinsa ya banko k'ofar

Jiki babu k'wari ta mik'e ta koma d'aki,tagumi ta buga da hannayenta duka biyu tana jimamin halin da MA'U ta jefata da kuma irin halin da ita kanta ta jefa kanta,kuka sosai LADIYO take yi tana kuma tsinewa MA'U duk kan damuwar da ta haifar musu,yanzun gashi ta barta a ciki.....

_Niko da nake gefe nace kad'anma kika gani,ki jira zuwa nan gaba...._

《《》》

Tun bayan fitarsa da suketa magana bai saurare suba duk k'ok'arin UMMI bai wuce sanin dalilin canjin da ta gani a tattare da shiba,amma ganin yadda yake tafiya da irin yadda ya fisge daga rik'on da KHALEEL yayi masa a k'ok'arinsa na dakatar da shi daga nufinsa,ta tabbatar ba k'alauba amma sai bata kawo komai a rantaba duba da yanayin da yake ciki kenan lokacin da suka shigo,sai tayi tunanin ko wani abu ke damunsa daban..
FItowansa daga parlor KHALEEL en ya biyoshi duk dan ya dakatar da shi amma inaaa lokacin harya manne motansa,a k'ok'arinsa na yin reverse har round about en dake farfajiyan gidan ya daka da bayan motan amma sam bai kula da hakanba saima ficewa da yayi a 360...

Da gudu KHALEEL en shima ya hau motansa ya biyo bayansa ba shi ya kyaleshiba sai bayan da yaga shigarsa gida sannan KHALEEL en ya juya yana kuma jimamin abunda ke damun aminin nasa da ya zame masa kamar wani mai shafar jinnu...

《《》》

Duniyar ta masa k'unci yahuma da k'yar yake iya had'iyansa wanda yake jinsa kamar judar k'asa yake taunawa..
Wayoyinsa dake gefe ne d'aya ciki ta hau kuka,kamar bazai dubaba haka ya banzatar da ita,zuwa wani lokaci daya ji an ci gaba da kiran ya bud'e idanunsa da suka matuk'ar firgitar dani ganin jini kwance cikinsu kamar dama can idanun nasa babu komai cikinsu sai jini..
Ko dubawa baiba ya danna bottom en da baima san me ya dannaba gefen kunnensa ya ajiyeta sannan ya sake maida idonsa ya kulle.
Maganar da ya jiyo ne ta cikin wayan yasa shi saurin laluben wayan ba tare da ya kuma bud'e idanunba ya karata a kunnensa.

"Hello SON kuna lafiya dai ko?"

Sai da yayi k'ok'ari ya saita nutsuwarsa sannan ya iya amsawa
"Ehh UNCLE muna lafiya ya k'asar Singapore da aiki?"

"Alhamdulillah!kam zamu ce"

Shiru sukayi na d'an lokaci kafin UNCLE yace
"SON are u there.....?"

"Ehhh UNCLE..."

"Ok akwai wani abune najika kamar kana cikin damuwa hope dai komai lafiya?"

Shiru BB yayi yana dad'a hasaso abunda ya faru d'azun bada jimawaba sannan ya dake
"Ehhh to Lafiya dai ba lafiyaba UNCLE"

Da sauri UNCLE en yake fad'in
"Maza sanar dani abunda yake faruwa son kaji ko kada ka b'oyemin,komai kake ciki ka sanar min nima mahaifine a gurinka kaji ko?"

Damuwansa a lokacin ya dad'a kaiwa mak'ura,idanunsa babu abunda suke hasko masa face hotonsu suna rik'e da hannun juna sai dariya suke,da k'yar ya iya furta
"ABBA......................."

*~#TEAM KHUBRA.~*

*_#REAL SMASHER._*
💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*15/ʝųlყ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
_As'alullahal aziiym rabbal arshil aziiym an-yasfiyaki ×7...._
_Cweet sis *SAFIYYA BALA (MOM HANAN)* ina miki fatan samun lafiya mai d'orewa kuma ingantacciya,abunda muka rasa kuma Allah yasa mai ceto ne ranar gone k'iyama,Allah ya bamu hak'uri da juriyan rashinsa..._
*~________________________~*
_ALHAMDULILLAH!family nd friends addu'anku a ko wane lokaci garemu tana zama karb'ab'b'iya muna godiya sosai da addu'o'inku,SISTER kuma Allah ya bayyana mana ita,sai dai bata cikin hayyacinta,muna fatan zaku sake taimaka mana da addu'ah akan Allah ya daidaita mata tunaninta...REALLY HEART U MY PEP's 💔..._
*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*4⃣5⃣*

*"SON* me ya faru maza sanar dani,wane ABBA'N kake nufi???"
Sai da ya saita kansa zuciyansa kuma na ambaton
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un
Allahumma inniy a'uzhubika minal hammi wal-huzn,wal-ajazi wal-kasali,wal-bukhli wal-jubni,wa-dal'iddaini wa-galabatir-rijaal"
Take ya d'an fara samun nutsuwa duk da idanunsa na kulle har lokacin,kamar yadda har lokacin bai daina ajiyan zuciyan da yake yi da sauri-sauriba.
"UNCLE please dan Allah ka taimakemu idan kasan inda ABBA yake ka sanar damu please........"

Daga b'angaren UNCLE en yayi shiru yana sauraron BB,yanayin da ya jishi ya tabbatar da matsala,amma da yake yana sone BB en ya sanar masa ko akwai wata damuwa da zai iya maganceta sai ya sauya salon maganar tasa.
"SON nace ka sanarmin da damuwarka idan akwai abunda zan iya to"

"Noo!UNCLE babu komai kawai dai muna da buk'atarsa ne kusa damu....behind these ma babu yanda za ayi mu rayu ba tare da shiba,rashinsa tare damu zai haifar mana da matsala a rayuwarmu ko ta b'angaren neman aure,sannan mutane da dama a yanzun sun rigada sun san cewa ABBA ba wai mutuwa yayiba....UNCLE duk duniya a yanzun na tabbata kuma duk inda ABBA'NMU yake ya sanar maka,kuma tabbas kaima UNCLE kasan inda yake....."
Yanayin yanda yake magana kad'ai UNCLE ya karanta,shiru duka sukayima juna har na tsawon wani lokaci,jin shirun yayi yawa yasa BB jiki a sanyaye ya furta
"Shi kenan UNCLE zamu hak'ura daga nan har zuwa lokacin da ABBA zai ji son ya dawo gida garemu,za kuma muci gaba da addu'ah Allah ya juyo mana da hankalinsa kanmu"
Hawaye ne suka ziraro masa ta gefen idanunsa,kasa jurewa ci gaba da magana yayi saboda yadda zuciyarsa ta dad'a yin rauni da sauri ya kashe wayan,saitin zuciyansa yasa hannunsa biyu ya danne bakinsa na ci gaba da motsawa da alama yana addu'ah ne a lokacin...
Chapter 48 · 0% Book details