← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 86

Sashe 13

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin babu sarki sai Allah ta rarrashi zuciyarta,ta wuce zuwa d'akin ASHNAR,tattara kayan tayi kaf closet enta babu wani kaya da ba a b'ata ba,haka taita jido su tana fito da su har ta kammala...
A washing machine taita sawa tana wankewa,da yake tana taya ZUHRA wani lokacin,kuma itama takan wanke nata,haka ta b'ata lokaci mai tsawo tana fama da kayan...
Tana cikin wanki ta jiyo muryan ZUHRA na kiranta,tana daga cikin toilet en ta amsata,aiko ta shigo...
Da mamaki ta kalleta tana fad'in
''Me kuma ya had'oki da wanki yau?''

Murmushi kad'ai tayi,bata iya cewa komaiba,haka taita fama da wankin ita kuma ZUHRAN na tayata matse kayan,tsaf ta gama lokacin ana kiran sallan isha..

Sai da sukayi sallah tukun sannan suka shanya kayan,suka ci gaba da fira a d'akin KHUBRAN haka suka raba dare suna fira,sannan ZUHRA tayi mata sallama ta tafi d'aki,itama ko nan ta kulle k'ofa ta kwanta zuciyarta fal tunanin makomar zamanta a gidan....

《《》》

Sai da suka raba dare suna abu d'aya dukansu babu wanda yayi tunanin yin sallah,suna ta faman aikata masha'arsu...

Dan kansu kuma suka hak'ura da juna badon sun gajiba,don dukkaninsu gwanaye ne a harkar,kuma kowa nunawa d'an uwansa yake yafi d'ayan,sai da suka raba dare a haka,sannan kuma bacci yayi gaba dasu suna hakan,ba tare da sun tsarkake jikinsu ba bare gaida mahalicci...

《《》》

Shigowarsa gidan yaji kansa yana sara masa,take ko ya dafe kansa yana mai nufar d'akinsa ya kwanta ba tare da addu'ah ba bayan a da ya saba baya tab'a kwanciya bai yi addu'ar ba...

Tayi nisa cikin baccinta ta ji ana shafata,cikin magagi take magana,amma bai kulata ba yaci gaba da abunda yake jin abun yayi nisa kuma babu halin a daina yasa ta bud'e ido,wa zata gani??

Cikin firgici ta furta ''B...O....BO....K.A.....''

Bakinta har sark'ewa yake gurin maganar,shiko ya d'ora hannunsa a baki yana mata alamar tayi shiru..

Babu shiri ko ta ja baki ta tsuke,bata kuma furta ko a ba,haka ya rabata da ilahirin kayan da ke jikinta ya shiga amfani da ita,duk ilahirin jikinta ya mutu saboda tun da ya zo ya shafata,jikintan ya idasa mutuwa ta gagara tab'uka komai,har ya gama biyan buk'atarsa wanda ba shi ya k'yaleta ba sai gabanin b'illowar alfijr...

Kallonta yayi yana dariya wacce ta cika d'akin
''Kiyi maza kije d'akin mai gidanki,kisan yadda za kiyi ku samu wata alak'a ta shiga tsakaninki da shi a yanzun kafin b'illowar alfijir idan kikayi haka,duka buk'atunki sun gama biya kenan''......

Yana gama maganar ko ya b'ace,ta neme shi ta rasa,take ko ta ja zani tayi waje,tana shiga d'akin MALAM BUBA ta yi karo da shi kwance yana bacci,ai bata jira komai ba,ta sa k'arfi ta mirginashi ta ko hau shafa shi kamar yadda boka ya mata...

Da yake bai da magagi ya bud'e ido,suna yin arba da juna tayi cilli da zanin jikinta...

Wani sara masa kansa yayi,yayi saurin runtse idanunsa yana damk'e kansa,ganin haka LADIYO ta birkice tana fad'in
''Sannu MALAM ciwo kan ke maka?''

Kai ya kad'a mata bai ce komaiba,ita kuma ta fice tana nemo garin magani zata jik'a masa dan burinta bai wuce aiwatar da bayanin boka ba...

Kaf sai da ta hargitse d'akinta kan binciken magani amma bata ganshi ba..
Wani uban tsaki ta doka tana ficewa zuwa d'akin MALAM en...

Shiko tana fita wani bacci ya sake d'aukarsa,duk budirin da take bai sani ba...

Dai² zata shiga d'akinsan taji masallacin dake unguwan ladanin ya fara kiran sallah na biyu,alfijirya keto kenan,tuni LADIYO ta buga wani wawan tsalle tayi cikin d'akin MALAM en....

《《》》

Cikin daren ko a b'angaren KHUBRA haka ta tashi tayi alwala tahau jero nafilfili tana dad'a kai kukanta ga rabbis-samawat..
Har aka kira sallah tana kan abun sallanta,sai da tayi sallah sannan ta d'an kwanta,aiko take bacci mai dad'i ya sake d'aukanta...

A furgice ta farka tana kallon yadda gari ya soma haske,cikin sauri ta watsa ruwa ta fita tayi kitchen,abinci ta d'ora mai sauk'in dahuwa,cikin lokaci k'ank'ani ta kammala komai har girkinsu HANEEF da yake su biyu ne ke tafiya da abinci,ta gama had'a musu a lunch-box ensu..
Sai lokacin nutsuwa tazo mata,ganin ta kammala cikin lokaci k'alilan,tayiwa Allah godiya,sannan ta fita ta shirya musu dinning..
A cikin kitchen en ta ci nata abincin,tana gamawa ta hau wanke²..
Dai² lokacin ZUHRA ta shigo,sad'af² ta biyo ta bayanta ta rufe mata ido...
Murmushi tayi tace
''Habaaa ZUHRA kinma mai dani wata abar tsokanar ki kenan,kina tsammanin bazan gane bane?''

Tayi murmushi itama suka gaisa,a gurguje ta mata sallama ta fice daga kitchen en...

Suna fita ba jimawa itama ta fito ta tafi d'aki,ta kwanta tana tsaka da tunani bacci ya d'auketa dan kuwa dama baccin take ji.......

*_~#TEAM KHUBRA~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘

💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*3/mąყ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._

*~________________________~*
_Masoyana a ko ina kuka kasance bazan iya mantawa da k'auna,halacci tare kuma da kyatatawarku gare niba,tabbas kun nunamin karamci wanda ba zai tab'a gogewa a cikin raina ba har sai bayan bana numfashi,Allah ya bar k'auna tare da zumunci.._
N
A
G
O
D
E
_Sosai da sosai,Allah ya barmin ku,duk inda kuke ina tare da ku da izinin Allah... *#1 luv my peps..*_
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*

_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._

*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*2⃣0⃣*

*K'*afafunta saboda tsabar kid'imewa da tayi har neman kasa d'aukarta suke,kamar an cillota ta fad'o d'akin aiko bata jiraba ta afka kan MALAM dake ta sharara bacci abunsa...
Shafa shi ta shiga yi shi ko maimakon ya farka kamar yadda yayi d'azun saima dad'a gyara kwanciya da yayi,yana sakin numfashi abunsa...

Haushi duk yabi ya cika mata zuciya,haushin rashin farkawarsa yasa ta kirb'a masa wani naushi aiko take ya bud'e ido,murmushi ya mata ya sake kulle idonsa yana mai dad'a gyara kwanciyarsa......

Kamar mahaukaciya ta fice tana sosa jikinta........

《《》》

Tsaf suka gama shek'e ayarsu a daren,har safiya suna mak'ale da juna...
Yanayin kwanciyar da suka yi kai da gani kasan ba shiryawa baccin suka yiba,dan kam da gani kasan suna tsaka da harka baccin yayi awon gaba da su.....

Ko da ta farka lokacin har gari ya gama haske,sannan ta bud'e idanunta da suka mata nauyi...
Jiki ba k'wari ta fita tayi wanka,bata tashe shiba dan kansa ya tashi yayi wanka,lokacin ko a takure ya ganta wanda ita kad'ai tasan halin da take ciki...
Sai da ya gama shirin ficewa tukun ya dawo
''Yahhh!d'an kawo wani abu mana''

Da rinannun idanuwanta ta kalleshi tana neman k'arin bayani...
''Ko zaki cemin oga bai sallamekiba?''

''Ohhh!kuma nufinka ni zan baka wani abu cikin kud'in ne?wato baya ga biyan da na maka har wani sabon tukuicin kake nema?''

Dariya yayi irin tasu ta y'an duniya,kafin ya juya yana nufar hanya yasan kam duk inda ya kai da son duniya MA'U ta fishi,haka ya fice yana fad'in
''Sai kin ganni''
Bata ko d'aga ido ta kalleshi ba bare ta bashi amsa.........

《《》》

Ko da ta farka bata wani b'ata lokaci ba ta koma bakin aikinta,har ta kammala ta fito da niyyan komawa b'angarenta..
A parlor ta tarar da ita tayi shirim cikin sofa,har zata fita ta kwad'a mata wata tsawa,ba shiri KHUBRAN ta dawo dan ita kam a yanzun baza ta so abunda zai rabata da gidan ba,dan ko shi ne rufin asirinta a wannan halin da take ciki...

''Wanki yana nan ya taru,saboda haka kiyi maza ki soma''

Shiru tayi ta kasa magana,zuwa wani lokaci kuma ta mik'e uwa kazar da kwai ya fashewa a ciki.Haka ta jido kayan masu uban yawa sai wari suke uwa masu kayan basu san wani abu mai kama da turare ba,ko da ta kaisu bakin washing machine en gani tayi kayan sam ba zata iya wanke su iya yau ba,dan ko kaya ne har na mutum biyar,bata b'atawa kanta lokaci gurin tunani ba ta hau abunda tasan shi zai fishsheta,tun tana na marmari har ta gaji.A haka su ZAHRA suka dawo suka tarar da ita,ko kallon arzik'i bata samu daga gurin ASHNA da FATAHIYYA ba..
ZAHRA kam dama tuni ta riga kowa shigowa,nan tai ta mata sannu,haka suka shiga ciki...
Ko cikakken mintuna talatin batayi ba ta fito ta dawo gurinta aiko tare suka ci gaba da aikin shanya,har malaminsu na islamiyya ya zo,a nan ne ta barta ta tafi,har suka dawo bata kammala ba,k'arshe dai yinin ranar haka ya shud'e mata tana abu d'aya..
Wajen k'arfe goma na dare ta tattara ta ajiye su akan ta k'arasa idan Allah ya kaimu washe gari........

Rayuwa ta mik'awa KHUBRA cikin wannan gida,wanda iya wannan lokacin babu wani abu dake shiga tsakaninta da y'ay'an gidan,ta kame kanta had'e da rik'e matsayinta na y'ar takala,duk wani aikinta tana gama shi take barin cikinsu ta koma guarding tai zamanta,mafi yawancin lokaci nan ne gurin da ke d'ebe mata kewa,musamman idan ta tuna ABBANTA ko MAMANTA da bata tashi tayi rayuwa da ita ba...

Cikin sauri² ta fito zata shiga cikin gidan,karo suka kusa yi da ZAHRA,da saurinta kuma ta tsaya tana kallonta duk sai murna take uwa wacce akama wata gagarumar kyauta,kallonta ta tsaya yi...
Da sauri ZAHRA ta rik'eta tana jan hannunta suka nufi kitchen,aikinta ta fara suna ta hira,duka yau tana kula da yanayin ZAHRA wani murna take tayi ita kuma tak'i tambayan dalilin,suna ta aikin su,can ZAHRA ta d'ago tana kallon KHUBRA...
''Wai kam sis kin san wani abu?''
Kai kad'ai ta kad'a mata kafin ta bud'e baki tayi magana ZAHRA ta katse ta da fad 'in
''Cikin month ennan YAYANMU zai dawo fa''
''Eeyyahh!Allah dawo da shi lafiya,yasa ya samo abunda yaje nema''
''Ameen dear,aiko zai sha labarinki duk ranan da mukayi waya''
Ita dai KHUBRA bata sake magana ba,ta ci gaba da aikinta,ZAHRA kuwa nan taita bata labarin YAYAN nasu,wanda har zuwa yau bata tab'a tsintar sunansa ba..
Chapter 13 · 0% Book details