← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 86

Sashe 18

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take ko zuciyar HAJIYA MURJA ta soma skipping,ranta duk ya b'aci da wannan maganar,daga jin wannan zancen babu alkhairi cikinsa,dan ko bata raba d'ayan biyu wannan shegiyar y'ar mai kama da aljanu yake so...
Zuciyarta ta danne kafin cikin kissa ta furta
''Aiihhhooo!KHUBRA yake nufi ba...........Ai ko tabbas gidana take,sai dai wani hanzari ba guduba,gaskiya HAJIYA kiyi hak'uri da abunda za kiji yanzun..
Ita dai wannan yarinya da ake magana kanta babu wata alak'a tsakaninmu da ita face matsayinta na 'YAR AIKI,inama laifin ya duba cikin k'annen nasa ko Allah zai sa a dace''

Ita dai HAJIYA FATEE shiru tayi tana mamakin lamarin,a zuciyarta ko fad'i take
''Aiko bari SON en ya dawo,sam baza ta sab'uba(wai akace bindiga a ruwa)''........

Haka sukayi sallama,take bata jiraba ta dokawa KHALEEL waya,katsewa yayi ya kirata coz dama al'adarsa ce hakan...
Bata jira tajima me zai ceba ta hau fad'in
''Maza kazo ina son ganinka''
Tana gama fad'in uzurinta ta katse kiran,sai safa da marwa take a parlor ita kad'ai....

Shigowansa parlorn ya tarar da ita a tsaye,hankalinsa har ya soma tashi ganin yanayinta...
''UMMI lafiya naga hankalinki a tashe?''

''Dakata SON'' ta d'aga masa hannu
''Dama yarinyar da ka dameni akanta *HOUSEMAID* ce?''

''UMMI amma fa''...........

''Bana buk'atar jin komai daga bakinka,magana d'aya zan fad'a maka ka shafe babin wannan maganar a rayuwarka,ko dai cikin k'annenka ka duba wata ko kuma ka nemo wata,amma banda wannan''

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN
Yake maimaitawa,kafin ya kalli mahaifiyar tasa
''UMMI mene laifinta,yanzun ita ba mutum bace da baza a sota ba,kuma tana da iyaye......Ni gaskiya da in auri wannan yarinyar Allah gara na k'are rayuwata babu aure''.........

Kafin ya k'arasa ta wanke shi da mari tana nuna shi da hannu
''Wallahi SON baza ka kunya tani ba ASHNA ce baka so,to ka sa aranka kai da ita anyi an gama sha³''.......

Dafe da kumatunsa yake kallonta,tsawon tasowansa bata tab'a masa fad'a ba,amma yau har da mari,shi kam a ransa a k'udurce shi da ASHNA sai dai kallo,me zaiyi da wannan ballagazar?
Jin kalamanta na k'arshe ya tsorata,take hawaye ya shiga biyo kumatunsa,yasa hannu ya goge kallon UMMIN nasa kawai yayi ya fice....

Hawayen da ta gani a fuskarsa shi ya bata tsoro,da girmansa yake mata kuka,tabbas tasan bai tab'a ce mata ga wata mace da yake soba,lallai ko wannan yarinya duk inda ta fito ta daban ce.....
Tunani duk ya addabeta,haka ta zauna duk kuma sai taji babu dad'i,tasan gaskiya ya fad'a,to wai kam ita ya za tayi ne????

Yana fita daga parlorn direct gidan ya bari dan yasan hakan kad'ai shi ne solution,idan ta nemeshi ta rasa a gidan zata sakko....

Shi kad'ai yayi wani murmushin takaici,lokaci guda kuma wata tsanar ASHNA ta diro masa,aiko nan ya lashi takobin wallahi ko me za ayi bazai tab'a aurenta ba,da haka ya d'auki hanya wanda baima san inda zai nufa ba.....

《《》》

Tsawon kwanaki uku kenan bai sake sata a idonsa ba,duk inda ya so da ya ganta kamar wacce tasha sab'ani haka suke ta bugawa,da zaran ta shigo shi kuma yana d'aki,lokacin kuma da ta fita zai fito....

Yana kwance kamar wanda aka tsikara da allura ya mik'e parlor ya fito ya kwanta babu kowa cikin parlorn...
K'amshin da yake jiyowa daga kitchen shi ya sa ya mik'e fuskarsa ta dad'a kyau saboda yanda tayi fayau uwa wanda yayi jinya,a bakin k'ofan ya tsaya ya jima yana kallonta,sam bata san da mutum a bayanta ba,ya jima a haka hannayensa a hard'e kan k'irjinsa.....

MAMA ce ta fito cikin shirin fita da yake gidan ba kowa duk suna skul,kallon hanyan kitchen en tayi saboda ta ga kamar da mutum a tsaye,mamaki fal zuciyarta yanda ta ganshi yayi a gurin....

''SON zan fita''
Tayi maganar cike da k'ulewa,aiko ya juyo a d'an firgice yana kame² ya dawo cikin parlorn,sam ya rasa wace kalma zaiyi amfani da ita gurin kare kansa,kansa ya d'an kawar gefe

''Allah ya kiyaye hanya''
Ya furta a hankali,da harara ta rakashi ta fice,nan ya kwanta yana d'an murmushi,duk wani shige da ficenta akan idonsa take yinsa,zuciyansa fal far in ciki....

*********

''Tabbbb tun kafin wannan al'amarin ya afku gara nayiwa tufkar hanci''
Fad'in HAJIYA MURJA kenan da suke tafiya cikin motor
''Taya ma za ayi da raina maza biyu su nuna suna son wannan kuchakar yarinyar,ni kuma nawa suna zaune,ai sam haka ba zai tab'a faruwa ba,duk cikin su babu rabonki yarinya''

Wata k'awarta ta tuno take ko ta hau binciken number enta a wayanta...............

*_~TEAM KHUBRA~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*8/ʍɑվ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*

_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*2⃣4⃣*

*D*a k'yar ta iya lalubo number matar,wata dariya tayi ita kad'ai tana sak'a abubuwa da dama cikin ranta,bata jira ta b'ata lokaci ba ta danna mata kira....
Ta jima tana ring ba a d'aukaba,haka ta ci gaba da mai²ta kiran kusan sau uku tana kira wayan na katsewa,har wata zuciyar ta bata shawaran kar ta sake kiran ta ji ba zata iya hak'uri ba,kiran ta sake yi,cikin sa'a wannan karon aka d'auka,zuciyarta tayi kar saboda murna,sai dai me tana d'auka taji an ce
''Hello! wa ke magana,naga an dameni da kira tun d'azun''

Baki ta sake tana mamakin lamarin dama akwai ranar da HAJIYA LAURA zata manta da ita haka,matar da tun k'uruciya suke tare...
Zuciyarta ta danne tana fad'in
''HAJIYA LAURA amma alk'awari baice haka ba,yanzu a kwai ranar da zaki manta da ni k'awarki da muka tashi tun yarinta?''

''Laaaa!HAJIYA MURJA kin san Allah wannan kalaman naki su suka sa nayi saurin ganewa,da yake sim card en nawa ya sha welcome back ne,saboda ana yawan sacemin waya ko na yar,to ke kuma ba gwanar kiran mutum ba bare na samu numbrki''

''Eyyahh!Allah ya maida alkhairi''

''Ameen''...........

Nan suka gaisa,kafin HAJIYA MURJA ta soko mak'asudin kiran da tayiwa ita HAJIYA LAURAN,bata b'oye mata ko da wasali ba kan abunda ke shirin faruwa.....

Dogon numfashi ta sauke,kafin ta cema da HAJIYAN
''Gaskiya HAJIYA yanzun bana so muyi saurin yanke hukunci,amma abunda ya kamata muyi shi KHALEED tunda gida d'aya kuke da shi da kanki zaki sa masa ido kan al'amuransa,tunda kinga har yanzun bamu gane sonta yake ko kuwa,shi kuma wancan KHALEEL kika ce sunan sa ko?''

''Ehh!haka ne''

''Yawwa to abunda za kiyi shi ne duk hanyar da zai ganta idan ya zo gidanki ki tosheta,sam kada ki ba shi wannan damar,idan yaso sai ki dinga tura su ASHNAR ko ita ZUHRA,idan kuma ya tambayi yarinyar kawai kice ai ta koma gidansu aure za su mata,fak'attt magana ta k'are kinga an yiwa tufkar hanci''

Shiru tayi tana sauraren k'awar tata,take ko tayi na'am da shawarar tata,sun jima suna magana kafin suka yi sallama kan sai kuma sun had'u ko ta sake kiranta.....

《《》》

Da ihuu su HANEEF suka shigo kamar kullum,sai dai suna shigowa parlor suka yi d'iff saboda ganin OGA a kwance,babu wanda yayiwa magana suka b'ace kowa yayi hanyan d'akinsa....

Allah sarki ZUHRA ko da ta shigo cikin parlorn waige² tai tayi coz sai da ta biya d'akin KHUBRAN bata ganta ba,hanyan kitchen tayi nan ta hangota ta juya baya,hakan yasa ta lallab'a bata sani ba sai ji tayi an rufe mata ido,y'ar dariya tayi mai sauti,itama ZUHRAN dariyan tayi kafin kuma ta zare hannunta daga fuskan KHUBRA,juyowa tayi ta kalleta
''Har kun dawo?''

''Lallaima wai har,ina fa har,kina gani tun safe fa muka futa bamu dawo ba sai yanzun''

''Ai kuwa dai kam,Allah ya bada sa'a''

''Ameen kam,barin shiga na fito''

''Toh!a fito lafiya''

Ta juya tana tafiya had'e da murmushi,har ta fice ita kuma ta ci gaba da aikinta.....

Dai² ta zo giftawa ta parlor BB dake kwance ya d'an bud'e ido saboda yaji maganarta a kitchen
''My SIS idan kin fito ki zo ina nemanki''

''To BBNAH''
Da sauri tayi ciki,cikin sauri² tayi wanka ta shirya,a parlorn ta tarar da shi,kusa da shi ta nemi guri ta zauna,parlorn daga ita sai shi
''Aaamm!MY SIS kin san me zan tambayeki?''

''A'a YAYANAH''

''Yawwa dama kan wannan k'awar taki ce,me kika sani dangane da ita?''

Yanayin tambayar ya d'an d'aure mata kai,ganin bata gane ba yasa ya mata bayani,y'ar dariya tayi kafin ta sake maimaita masa abunda ta sani game da KHUBRAN kamar lokacin farko da ta tab'a bashi labarinta......

''Ok ba komai jeki na gode''
Yana gama fad'in hakan ta mik'e ta nufi kitchen,kasancewar ZUHRA yarinyace amma akwai basira ta harbo inda maganar BB ta dosa,dan tafi kowa sanin halayyarsa ta rashin shiga abunda babu ruwansa,idan ko har kaga yayi magana kan abu to da walakin (Goro a cikin miya).......

Kitchen en ta koma ta tarar har ta gama abunda take,da murnanta ko ta hau tsokanarta
''Matar YAYA har kin kammala ne,dan nifa da yunwa na dawo''

Da sauri KHUBRA ta kalleta tana mata alamar neman k'arin bayani
''Wane YAYA kuma?''

''Nawa mana ko zan fad'i wani ne ba shiba?''

''Uhmmm!rufamin asiri matsayina bai je nanba''.....

''Tabbb ai wollah har kin wuce nanma,ke wollah da izinin Allah ke rabon YAYANA ce dan ko naga alama''.......

Maganar ce ta mak'ale saboda shigowar ASHNA cikin kitchen,kallon da ta yiwa ZUHRAN da ita kanta KHUBRAN shi ya tabbatar musu ta ji abunda suke magana akai....
Sai da ta gama d'aukan abunda ta zo nema sannan ta kalli ZUHRA
''Ke kam koi banza,ta ina ma zaki had'a YAYA da wannan matsiyaciyar,wacce iyayenta basu damu da sanin inda take ba,sun turota aikatau saboda neman abun duniya,ki rasa da wacce zaki had'a shi sai wannan,to wallahi yafi k'arfinta,banza sha³ kawai''

''Eeehh!an fad'a en naga itama ai mutum ce,ke har kina da bakin magana,wannan en da kike gani kina rainawa naga dai ta fiki duk wani abu da kike tak'ama da shi,k'ark'ari ki nuna mata gidanku suna da wadata, bayan wannan babu abunda zaki gwada mata''......

Bata k'arasa ba ASHNA ta kwasheta da mari da yasa tayi shiru tana binta da kallon mamaki
''Ni kika mara kan na baki amsa?''
Chapter 18 · 0% Book details