← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 86

Sashe 21

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

''Nasan da haka BIGGY ai shi yasa bana wasa da lamarinka,zan turo maka address na inda gidan yake''

''An gama,sai na jiki''
Da haka ya sa kai ya fice....

Yana tafiya ko ta tura masa komai,take kuma ta kira HAJIYA MURJA
''Toh na gama nawa sauran aiki yana hannunki,duk yanda za ayi anjima bayan Maghreb ki aiketa,zan miki bayani bayan kinyi hakan''

Tana gama fad'in haka ta kashe wayan,tana wani makirin murmushi........

*7:30pm*
KHUBRA ta shigo parlorn HAJIYA MURJA ita kad'ai ta tarar a parlorn,wani leder bak'i ta mik'o mata k'unshe da wani abu da ni kaina ban san mene a ciki ba,amsa tayi kafin HAJIYA ta soma magana

''Maza karb'i wannan kije waje zaki ga wani a bak'in mota ki kai masa injini''

Cike da ladabi ta amsa,har ta mik'e ZUHRA ta fito daga corridor en bed room nasu,kallon KHUBRAN tayi itama tana kallonta tana d'an murmushi kamar wanda basu saba ganin junaba suka k'urawa juna ido,fitowan BB ta waiga ta kalle shi,rana ta farko kenan da ta k'ure shi da kallo a iya zamanta a gidan,tsananin fad'uwa taji gabanta yanayi,a hankali ta waiwaya za ta fita,haka kawai taji idanunta sun kawo ruwa,da sauri ta sa hannu ta goge...

''SIS tsaya na rakaki''
Bata jira amsanta ba ta biyo bayanta,da sauri ta rik'e hannunta har suka fita daga gidan,KHUBRAN ce ta k'arasa kusa da window en motern tayi knocking,ZUHRA kuma tana jikin get,k'ofan aka zuge....

Gaisheshi tayi duk bashi da kad'ai ne a motanba,amma ita kam shi ta gani ta mik'o masa abunda ke hannunta aiko take ya mik'a hannu kamar zai amsa kawai ya fizgota cikin motan take ya datse k'ofan suka figi motan a 360...............................

*_~TEAM KHUBRA~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*11/ʍɑվ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*

_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
_Ga masu buk'atar son kasancewa da group na *Y'AR GARUWA* za ku iya yin joining ta hanyar amfani da wannan link en,saboda gujewa had'uwa da maza,mata zallah dan Allah👏..._
👇
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EvdAvnFbBaX2BBMAwCCH4E
*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*2⃣6⃣*

*B*akinta da hancinta ya danne da wani handkeey take ko ta sulale uwa matacciya....
Ganin abunda ya faru yasa ZUHRA dake tsaye matsowa da gudu kuma ta hau natsowa kusa da motan...
Cikin wani razanannen murya ZUHRA ta shiga k'wala kiran sunan KHUBRA wadda tuni motarsu har ta b'ace daga line en.....

Faruwar hakan ke da wuya ta dawo da gudu ta shiga gidan babu kowa cikin parlor sai BB dake shirin barin gurin shima,a rud'e ta k'arasa kusa da shi fuskanta duk ya gama yin kacha² da hawaye,chakumoshi tayi tana kuka take fad'in
''Sun tafi da ita dan Allah YAYA karka bari su tafi da ita''

Gaba d'aya kalamanta sun gama rud'ashi,ya rasa ganema inda ta dosa,a hankali ya shiga girgizata dan kam ya gama fuskantar a kwai matsala
''Su waye ne kam,kuma waye suka tafi da ita?''

''YAYA KHUBRA sun tafi da ita,YAYA za su cutar da ita,please karka bari su gudu da ita''

Sunan KHUBRA da ta ambata shi ya masifar d'aga masa hankali,take ko ya sake ta yayi hanyan fita daga gidan,da gudu ta biyo bayanshi,sai dai ko da ya fita babu ko da k'urar motan bare yasa ran ganin ita kanta motan,tsayawa yayi ya dafe kansa baya ga *''INNALILLAHI WA-INNA ILAIHI RAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNIY FIY MUSIBATIY WA-AKLIFNIY KHAIRAN MINHA''* babu abunda yake fitowa daga bakinsa sai wannan,wani sabon yanayi ya tsinci kansa a ciki,sam ya kasa magana fuskarsa lokaci guda har ta sauya kammani....
ZUHRA dake tsaye kusa da shi ko har yanzun banda gunjin kuka babu abunda take,kallonta kad'ai ya iya yi,kusa da ita ya matso yana son tambayanta sai dai kalmomin sun mak'ale a iya mak'oshinsa.....

Matsawa yaga ZUHRA na yi har dai² gurin da motan su BIGGY ta bari,takalman KHUBRA ta d'ebo wanda garin kokawar sata a motan suka watse a kasa,rik'esu tayi k'am ta rungume tana ta faman kuka,gwanin tausayi haka take kukan babu mai rarrashi....

Kusa da ita ya dawo hannayensa yasa akan sholders enta
''Pleasee!ya isa haka sisnah waye ya sa ku fito a daren nan?''

''MAMA ce ta aikomu''

Katseta yayi dan ko sunan kad'ai da ta ambata sai da gabansa yayi mugun fad'uwa,a zuciyarsa ya furta
''Ko me ya sameki tabbas da sa hannun MAMA a ciki,amma me yasa za ta aikata mata haka?",rashin amsa ya sashi dakatar sa tunanin,dan ko ba lokacin tunani bane,gefe suka sake komawa cikin low voice yake mata magana,ammafa hankalinsa baya tare da shi

''SIS abunda nake so dake ki dena kukan nan haka,kuma koda mun koma gida kada ki nuna damuwa kan abunda ya faru,har sai mun gano gaskiyar wanda ya aikata hakan''

''YAYA ai babu wanda ya aikata komai face MAMA''

Duk da ya sani da sauri ya dakatar da ita
''A'a SIS ba a saurin yanke hukunci,mu jira mu gama bincike tukun kin ji ko?''

Kai ta kad'a masa,hannunta ya ja suka kama hanyar komawa cikin gidan suna tafe yana bata baki kan kada ta kuskura ta nuna damuwa ko da anzo ana maganar a ganta....
A hanyan suka rabu shi ya nufi corridor da zai sada shi da bedroom ensa,suna tafe kowa zuciya babu dad'i kamar majinyata haka kowa ya shiga bed room ensa.....
Daren ranar kam a b'angaren ZUHRA da BB babu wanda ya iya cikakken bacci,gani suke kamar an had'e musu darare arba'in dan ko har fatan wayewar gari suke.....

《《》》

Tun bayan barinsu line en basu tsaya ko inaba sai k'auyen ZAKIRAI dake cikin garin kanon dabo,da yake dare ya soma yi sosai kuma suna son komawa dan ko hanya suke shirin d'auka zuwa garin kaduna,dai² kasuwarsu dake gefen hanya suka perker,sai da suka duba suka tabbatar babu kowa da yake ganinsu kafin suka kinkimota daga cikin motan,k'asan wata rumfa suka shimfid'eta tare da sanya mata ledan da ta fito da ita a tsakanin hannayenta,juyawa suka yi da mugun gudu suka bar gurin,yayinda KHUBRA ke baccinta peacefully,ko sanin inda kanta yake bata yi ba.....

Sai da gari ya gama haske mutane nata hada-hadar kasuwanci sannan ta farka,nan ta shiga k'arewa ko ina kallo,can ta kalli kanta sai a lokacin ta iya tuna abunda ya faru da ita a jiya da dare,take ko wasu zafafan hawaye masu k'una suka shiga sakko mata,ta jima tana kuka uwa baza ta dena ba,da k'yar ta mik'e ta nausa cikin kasuwar k'afarta ko takalmi babu,ita dai har yanzun tana rungume da wannan ledar.....
Yunwa ce ta fara damunta take ko ta sake sakin wani sabon kukan,tuna yadda rayuwarta ke garawa bisa doron K'ADDARA,zuciyarta fal addu'ah ta neman agaji daga mahaliccin sammai da k'assai,a hankali ta ware ledan dan duba abunda ke ciki dan kam ita tunanin yasarwa take,kud'i tayi arba da shi y'an one thousand sababbi,take ko tayiwa Allah godiya....
Guda ta zaro ta shiga bulayin neman abunda za ta karya,mai k'osai kad'ai ta samu aiko take ta tsaya sai dai gurin akwai yalwar mutane dake faman bin layi....
Kallo ne ya koma sama (wai akace shaho ya d'auko giwa) duk inda ta gifta sai dai kaga idanun mutane a kanta,bama kamar gurin mai k'osan da take tsaye uwa wacce aka dasa,har lokacin k'afafunta babu takalmi,tana nan tsaye har layi ya zo kanta mik'a kud'in tayi tana jiran a bata ba tare da ta fad'i adadin na yanda za a bata ba,kanta a k'asa ta kasa kallon kowa zuciyarta ko tarin k'unci ne a cikinta bama kamar yadda take fama da tunanin ZUHRA sahibarta,k'awarta,take ko wasu sabbin hawayen suka sake sakko mata....

Mai k'osai tana tambayarta amma sam bata sanma me take yiba,ganin haka yasa kawai ta auna mata,kafin tasa aka tab'ata,a d'an tsorace ta d'ago hannu tasa ta amsa tare da juyawa za ta bar gurin,chanjin da ta juyo da niyyar bata taga har ta yi gaba da sauri tasa wani yaro ya bi bayanta,d'an murmushi ta masa duk da tarin k'uncin dake cunkushe a zuciyarta ta amsa wash hawayen na dad'a sakko mata taci gaba da tafiya....
K'asan wata bishiya ta zauna jama'a nata kallonta amma sam hakan bai wani d'aga mata hankali ba,sai da ta tabbatar ta k'oshi kafin tunanin neman mafita ya fad'o mata....

''Ina ya kamata na dosa ni da ba ko ina na sani ba?''

Babu inda ta sani bare ta ce ga hanyar gidansu,ko da canma ba fita take ba bare daga baya da ta dawo wani gari na daban,tana zaune ta had'a kai da gwuiwa tana tunani,wani mai kuran ruwa ya d'an tsaya a kanta
''Yarinya sannu ko''

Kallonsa kad'ai ta iya ba tare da ta iya magana ba,kamar mai nazarin wani abu take kallon gurin da take zuwa wani lokaci kuma ta sake kallon mutumin ji tayi ta aminta da shi take kuwa ta bud'e baki da niyyar yin magana.......

《《》》

Haka gari ya waye musu babu wanda yayi isashshen bacci idanunsu a soye,kasa fitowa suka yi su duka biyu....

Lokacin break yayi y'ay'an HAJIYA suka fito da niyyan break,sai dai suna zuwa suka tarar da gurin wayam babu komai,kowa sai tura baki yake gaba uwa shantu,suka nufi d'akin MAMA da niyyar yi mata k'orafi....

''MAMA kinga fa ba a had'a break ba har yanzun''
Abunda ya fito daga bakin FATAHIYYA kenan da take kan gaba gurin shiga d'akin

K'wak'walwar MAMA ta tafi yajin aikin ina kuma KHUBRAN ta shiga (ni da nake gefe nace kajimin y'ar cin).........

Ta jima d'age da kai tana tunani,kafin ta soma tunanin me ya faru da ta aiketa jiya?

''Kuyi hak'uri kunji,maza kuje ku sha ko tea ne kafin na fito''
Fita suka yi suna tura mata baki,sai k'unk'uni suke,suka nufi dinning area,flask en suka kinkimo a tunaninsu a kwai wani abu cikinsa nan ko suka tarar da shi wayam shima,kuka kad'ai su HANEEF suka sa,wanda sanadin haka yasa BB fitowa fuskarsa uwa wanda bai tab'a dariya ba,wani kallo ya watso musu wanda yasa suka shiga hankalinsu ba tare da ya furta komai ba...
Chapter 21 · 0% Book details