← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 86

Sashe 63

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ohhh! abunda za kacema kenan...wato ka mai dani wani tamkar ban san abunda nakeba shi ne harda cemin na gama fad'an....?
To ban gamaba kuma Allah ka ji na rantse babu abunda zai hanani tafiya,idan ka gama ka dawo ka tarar da babu kowa...."
Yana kaiwa nan ya datse wayan ko sauraron me KHALEEL en zai fad'a baiba kuma har lokacin yana tsaye sai huci yake.

KHALEEL jin da yayi BB ya kashe wayan yasa shi saurin yin tunanin ya kamata ya tura masa wani evidence da zai zauna cikin gidan kada ya bar yarinyar mutane ita d'aya a gidan,da saurinsa ko ya tura masa sak'o ta email,sannan ya jaa motansa ya k'ara gaba.

Dai² lokacin da yake sintiri tsakiyan parlor hannunsa d'aya a dunk'ule yana naushin iska sak'on ya shigo,da sauri ya isa kusa da phone en yana dubawa,email nasa ya shiga cikin sauri saboda ganin sak'on ta email yake,nan ko ya tarar da sak'on audio da kuma na video's wanda da gani babu tambaya kasan a gurin d'aurin aure ne.
Cikin hanzari ya shiga playing nasu d'aya bayan d'aya yana kuma sauraro har dai² lokacin da aka soma sanar da d'aurin auren kamar haka
_An d'aura auren *IBRAHIM KHALEEL* da amaryarsa *KHADIJATUL-KHUBRA* akan sadaki naira na gugan naira har naira dubu d'ari biyar..._

Wani uban tsaki BB yayi a dai² nan yana fad'in
"Banda d'an iska ni zai rainawa hankali kamar ba a gabana aka fad'i hakaba...."
Kafin ya sake magana yaji mai sanarwar yana fad'in
_"Afwan..! Afwan..!! Afwan..!!!_
_Y'an uwa a gafarceni nayi makuwa gurin sanar da wannan d'aurin auren,ina fatan kuma za amin afuwa dan kuwa ba *KHALEEL* zan ambataba gurin fad'amin ne aka samu sab'ani sai yanzun aka sanar dani gyaran dake cikin wannan maganar tawa,a maimakon KHALEEL dana ambata *KHALEED* ne angon,wannan auren na *KHALEED* ne da amaryarsa *KHADIJATUL-KHUBRA*_
_Sai kuma auren *IBRAHIM-KHALEEL* da amaryarsa *FATIMA-ZUHRA* akan sadaki dai-dai dana y'ar uwarta,aure na uku kuma shi ne na *ABUBAKAR-SADEEQ* da amaryarsa *ASHNA* sadakinta kwatankwacin na y'an uwanta lakadan ba ajalanba...._
Dafe baki BB yayi yana fad'in
"Ta yaya akayi haka ya faru? kenan bayan na bar gurin akayi haka ko kuwa yaushe ne hakan ya faru...?"
'Daya bayan d'aya ya dinga binsu yana playing har yazo na k'arshe,again bai hak'ura ba ya sake kiran KHALEEL,shima cikin isa ya d'auka yana fad'in
"MAN! lafiya kake kirana kuma dai² lokacin da zan shiga gidana? ko kuma har yanzun shaidan basu gama gamsar da kai bane...?"

Murmushi kawai yayi yana fad'in
"Noo! kawai dai na kasa yarda ne...!"

"To tunda baka yarda ba ai shi kenan ka jira gobe sai su ABBA su maka bayanin yadda akayi haka,ni nayi iya nawa sauran nasu..."
Yana kaiwa nan ko ya kashe wayan gaba d'aya dan yasan idan ya barta haka BB zaita damunsa da kira,dai² ya shigo parlor aiko ya juya ya kulle k'ofofi tare da addu'an neman kariya daga mahalicci...

**********

B'angaren amarya KHUBRA kuwa tun bayan da suka futo daga parlor lokacin za a sasu mota ta rik'o ZUHRA akan itafa lallai sai dai k'afarta k'afar ZUHRA zasu tafi,ganin zata jik'a musu aiki da dabara aka sata cikin mota sannan aka ce to ta matsa ZUHRA ta shigo,da yake babu wayo nan ko ta matsa aiko tana yin haka aka rufe k'ofan sannan driver'n yaja yayi gaba.
Kuka babu irin wanda bata yiba dan an taho da ita babu ZUHRA dama kuma ba wani cikakkiyar lafiya gareta ba,haka ko bayan da aka kawota da d'aya da d'aya duka suka zare jikinsu suka gudu,aka barta daga ita sai halinta,kukanta ta shak'a bayan taji gidan shiru a nan inda ta gama kukan take kwance jikinta duk ya dad'a yin zafi tana saman bed jikin ta ya ko dad'a rikicewa ....

Nan parlor yaci gaba da zama ya kasa yanke shawaran abunda ya kamata yayi,har 12am yana nan shi bai bar gurinba kuma bai daina kiran number KHALEEL ba duk kuwa da yadda wayan ke sanar masa a rufe take,wani zuciyan ne ya bashi shawaran kiran UMMI baiyi tunanin komaiba ko yaddana mata kira ba tare da yayi tunanin dare yayi ko akasin hakaba...
Cikin magana irinta mai bacci UMMI ta d'auka tana fad'in
"KHALEED SON lafiya kuwa ka kirani cikin wannan lokacin.....ina ita KHUBRA'N ko kuwa jikin nata ne ya sake rikicewa...?"

Murmushi yayi mai k'ayatarwa ko tantama babu yanzun kam ya soma gasgata maganar KHALEEL,sai dai tambayan da yake ta damun kansa shi ne *TA YAYA HAKA YA FARU?*.
Murmushi yayi ta saki abunsa kamar ba wanda yake jinya ba d'azun,kan cuition ya kwanta had'eda kashe wayan ba tare da yayi magana ba,yana juya lamarin a ransa,lallai a yanzun kam ya tabbatar da komai hukuncin rabbi ne ba tare da dabara ko k'arfinsa ba ya bashi abunda ya jima a ransa a kuma lokacin da babu zato bare tsammani, ai kam ya tabbatar a yanzun yafi kowane d'a namiji sa'a,a duniyarsa gani yake babu wanda zaiyi dace kamar nasa.
Tunawa yayi da maganar KHALEEL ta d'azu da abokansu suke tambayan basu ganshi gurin d'aurin aureba,sannan kuma maganar UMMI ta sake fad'o masa inda take cewa
_"KHALEED SON lafiya kuwa ka kirani cikin wannan lokacin.....ina ita KHUBRA'N ko kuwa jikin nata ne ya sake rikicewa...?"_
Cikin hanzari ko ya mik'e yana bin hanyan da zai sadashi da d'akunan baccinsu cikin damuwa coz bai san halin da take cikiba a fili ya furta
"Is she ill...? Amma tun yaushe ne hakan ya faru...?"
Dai² lokacin ya iso kallon gefe da gefensa yayi coz bai san a wane room take ba,kallon doors yayi ya d'an tsaya tunani can kuma sai ya kalli wanda yake bud'e a hankali ya d'aga k'afafunsa ya nufeshi...

*GIDAN KHALEEL...*

Bayan ya gama tura masa abunda zai tura daya kashe phone ensa ya kulle k'ofifi,hanyan bedrooms en ya nufa yana fad'in
"HABIIBTIIY!!!.....Ina kika shige ne..?"

Shiru yaji babu amsa nanko ya nufi cikin bedroom enta,zaune saman bed ya hangota sai dad'a jan vail enta take tana dad'a rufe jikinta,da alama da ba gurin take zauneba,dariya yayi yana fad'in
"Ohh! kunyana kuma ake ji yau..? i think yau kam babu wannan a tsakaninmu tunda burin da muka jima da shi yanzun Allah ya nuna mana ranar da muketa jira...So ina ganin kamata yayi ace munyi godiya ga Allah daya nuna mana hakan cikin rai da lafiya gami kuma da kwanciyar hankali..."

A hankali ta d'an motsa kamar zata janye vail en sai kuma yaga sab'anin haka
"Ohhh! wato sai kin bani wahala dai kenan ko..?"

Har lokacin ZUHRA ta kasa masa magana,ta kuma k'i d'agowa ta kalleshi,saman bed en ya isa yana ajiye ledan dake hannunsa,a kusa da ita yayima kansa masauki,fuskanta ya shiga lek'awa yana fad'in
"Haba mana duk kalaman da nake GAM DA KATAR (ZEEY BUGAJE) dasu a kullum kuma yauda nake tsammanin ganinsu a zahiri bayan tsawon lokacin da muka d'auka bama tare,sai naga sab'anin haka,shi kenan tunda baki son ganina bari na koma inda na fito...Dama na had'u da wata d'azun so kinga saina tafi zance gurinta ko?"
Yana gama fad'in haka ko ya shiga k'ok'arin mik'ewa da niyyan zai fice,a zahiri kuma yana kallonta yaga wane reactions zata bayar da jin maganar tasa,alama yayi kamar zai fice,aiko nan ZUHRA ta dire k'afafu tana bugasu k'asa cikin tab'ara tana fad'in
"Ni wallahi a'a,kuma idan ka fita nima saina bika duk inda zaka..."
Dariya ya kwashe mata da,sai da yayi son ransa,ita kuma ganin yana mata dariya gashi dama tunda ta mik'e tayi cilli da mayafin,tsayawa tayi kallonsa yadda yake dariya take kallo sai taga ya k'ara mata kyau fiye da yadda ta sanshi.Tsayawa tayi tana kallonsa bata k'i su dawwama a hakaba.
Ankara yayi da irin kallon da take masa,nan ya matsa kusa da ita,waist enta ya rik'o yana matso da ita jikinsa,da sauri ta kalleshi coz batama san ya akayi yazo kusa da itaba,jinta da tayi a jikinsa shiya farkar da ita,duk'owa yayi dai² kunnenta yake fad'in
"MADAM wannan kallonfa haka,bayan gani kusa da ke,ko mafarki kike yine wata ta k'wace miki ni...?"

Kai ta sake d'agawa ta kalleshi jin abunda ya fad'a,a hankali ta tab'e d'an bakinta ta sake kauda kanta,mutsu-mutsu ta shiga yi saboda tana son ya saketa,shi kuma hakan da tayi yasa shi dad'a rik'eta sosai
"Please YAH ka sakeni..."
Maganar yayi escaping daga bakinta ba tare da ta shiryama hakan ba.

"Nak'i...Ina son jina jikinki ne yasa..it's been long da nake son mu kasance tare sai dai aikin UMMI ya hana mu kasancewa kusa da juna....Buh Al-hamdulillah alaa kulli haliin...Yau kam komai ya zama tarihi,tunda gamu yanzun a matsayin abu guda.."
'Dan murmushi ta sake yi tana sauke kanta k'asa dan ita kam yanzun tunda ya fara mata wannan maganar take jin kunyarsa...

《《》》
Chapter 63 · 0% Book details