← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 86

Sashe 6

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da k'yar ta mik'e daga gurin tana d'ingishi,haka ta koma d'aki tana duba jikinta...
Hannayenta ta k'urje su,ga d'an yatsanta na k'afa da yake mata rad'ad'i....
MENTHOLATOM ta hau gogawa gurin...
Azabar da yake mata ce ta sata bari babu shiri...
Haka ta kafawa d'an yatsan nata ido,ganin ya soma kumbura ta tabbatar ta samu targad'e...
Dafe kai tayi tana jin rad'ad'in da yatsan ke mata har tsakiyar kanta...

Lallai wannan yarinya koi ja'ira,amma babu komai ta ciji lips enta,
''Zanyi maganinki''
Ta furta ciki².....

*************

Haka ta shige d'aki ko tunanin sallah batayi ba,tana shiga kuwa ta turo k'ofar d'akin nata...
Kwanciyarta tayi take kuwa bacci yayi awon gaba da ita....

K'arfe 9:15pm MALAM BUBA ya nufo gidan nasa,da tunanin ko LADIYO ta ga dama ta dawo?
Tun da ya tunkaro gidan gabansa ke faman fad'uwa...
Bai kawo komai a ransa ba,haka ya shigo gidan,k'ofar dake jingine ya d'aga ya karata a saitin k'ofan...
Juyawa yayi ya shiga da sallamarsa...

Da yake yasan ma koda tana nan ba amsawa za tayi ba,hakan ya sashi wucewa d'akinsa.....

Jiri ne ya fara neman kada shi,da sauri ya dafa wall en d'akin,ya daddafa ya shiga ciki,tun da ya shiga d'akin bai sake sanin inda kansa yake ba......

***********

Lek'owa tayi tana daga soron,jin shiru da tayi,shi ya bata tabbacin bata gurin...
Da sand'a ta shigo ta lallab'a ta kwashe kayanta daga gurin....

Kan wall en toilet en gidan ta kai ta shanya,ta dawo ta nemi guri ta zauna tana jiran gawon shanu,nan ta sake lulawa duniyar tunani...

'Daga labule taga anyi,ai kuwa karaf akan idonta...
zaraf tayi ta mik'e tsaye,tana rab'ewa gefe....

Harara MA'U ta aika mata,ta wuce ta shiga toilet,kamar ko wane lokaci,kafin cikar mintuna biyar har ta fito....

Kallon KHUBRA tayi kafin cikin wata irin murya ta hau fad'in
''Uban meye kike jira a nan?
Ki zo ki wuce ki samo ruwa sannan ki tabbata kin sharemin gidan nan''...

Sum² ta zo ta wuce,haka ta d'auki k'aton bocket en da MA'U ta ajiye,ta jaa silifanta tayi waje...

Lokacin da ta fita rasa ina zata nufa tayi,coz tun da tazo yau ne rana ta farko da ta fara fitowa...
Ta jima tsaye tana tunanin in da ya kamata ta nufa....

Tambaya ta yanke shawaran tayi,amma wa zata tambaya? unguwan shiru,babu kuma masu wucewa....
Haka tayi ta tsaiwa a gurin....

Gajiya tayi da tsaiwan,zuwa wani lokaci har ra fara gumi,haka kan dole tabi ra'ayin zuciyanta..

Gidan dake gefensu ta nufa,sallama tayi ta shiga...
Babu kowa a tsakar gidan,sai wata mata da ta gani tana fitowa daga d'aki...

Da d'an murmushi akan fuskanta ta amsa mata,tana fad'in
''Maraba,k'araso daga ciki''..

Murmushin itama KHUBRAN tayi tana fad'in
''Laa da kin barni ma daga nan''...
Gaidata KHUBRA tayi,kafin ta shiga tambayanta inda zata sami ruwa....

''Laaa kinga ai ba nisa ma,kina fita akwai gida da yake kallon nan,suna da rijiya''-....

Godiya tayiwa matar ta kama hanya ta fice,matar na binta da kallo....

Haka ta shiga gidan,suka gaisa da matar mai kirki,sai jan KHUBRA take da fira,ita kam ta kasa sakin jiki da ita,haka taita kaiwa da kawowa,har ta kammala d'iban ruwan.....
Bayan ta kammala haka ta duk'ufa kan shara,zuwa wanke²...

Lokacin da ta gama tana murna za ta huta,har ta nemi guri ta zauna,MA'U ta lek'o tana fad'in
''To hakima ba zama za kiyi ba,maza duba wancan d'akin akwai kwanuka maza ki tattarosu ki wanke su,idan kin gama kimin magana....

Haka ta shiga tattaro kayan wasuma har sun fara fungi,wani kuwa cikinsa yayi bak'i kamar an shafa kwalta...

da k'yar ta gama wankewa,ko da ta gama haka ta kwashi k'afafunta ta je k'ofar d'akin
''Na gama'' abunda ta iya fad'a kenan...

''To jirani'' MA'U dake d'aki ta fad'a....
Fitowa tayi da uban kaya a hannunta,haka ta watso mata su,ta sake komawa ta d'ebo wasu...
''Ga shinan maza ki tabbatar kin wanke su sun fita tas,dan idanma basu fitaba,zaki sake ne''...

Juyawa tayi tana k'arewa kayan kallo,gasu da uban yawa,ga kuma daud'a,wanda ko kayan d'an goye ba zai nuna musu daud'aba....

Har ta kai bakin k'ofa KHUBRA ta furta ''Sabulun wankin''....
Shigewarta tayi,sai da ta gama b'ata lokaci,sannan ta cillo mata...
Haka tayita gurzarsu,babu iyaka,har dai ta samu ta kammala,lokacin ana kiran sallan ISHAA.....

Ranar gaba d'aya KHUBRA haka ta yini aiki daga wannan sai wancan...

Haka ta tashi jikinta sai kyarma yake,ga ciwo da yake mata,ga tsananin yunwa,ga uban ciwo da kanta yake tamkar zai rabe...

Tashi tayi da k'yar ta tattara kayan da tayi amfani dasu,ta shiga d'akin shirgin nan ta gyara shi,duk da tana cikin wannan halin haka ta share shi...
Ruwa ta d'iba ta shiga ta wanke jikinta,sannan ta d'auro alwala,ta fara jera sallolin da ake binta bashi,dan kuwa MA'U hanata tayi ta motsa ko nan da can...
Tana yi tana ZUBAR HAWAYE,tana rok'on Allah gafara da kuma neman d'auki daga gare shi.....

Ta jima acikin sujudah tana rok'on Allah,kafin ta d'ago tayi tahiya,ta sallame....
Da k'yar ta iya motsawa daga gurin,ta lallab'a ta fito daga d'akin...

'Dakin MA'U ta shiga sai tare kanta take da hannu wanda ke mata barazanar fashewa...

''Dan Allah BABA ki taimakamin da abunda zan ci,wallahi ina tsananin jin yunwa,kuma kaina ciwo yakemun''
Ta fad'a kamar zata fad'i....

''Ke dallah dakata,karki fad'o kaina,dan kina jin yunwa shi ne me?
Malalaciyar kawai,d'an wannan aikin da kikayi kinzo kina min raki''.....
Haka MA'U ta koroto ba tare da ta tausaya mataba...

Kuka ta fashe da ta nemi guri abakin d'akin ta shiga rerawa...

Ashar en da MA'U ta k'unduma ne ya sata tsagaitawa...
Kamar daga sama ta ga MA'U da jakar kayanta a hannu,cillo mata tayi tana fad'in
''Idan zaki iya tafiya bismillah,abincine banga dama ba,kina iya ki nema da k'arfinki sai ki ci......

*_~#TEAM KHUBRA.~_*

*_REAL SMASHER._* 🤞🏻😘
💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*30/mąrcɧ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_

🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._

*~__________________________~*

*ADDU'AR SHIGA BAN'DAKI.*

_BIMILLAHI!!! ALLAHUMMA INNIY A'UZHUBIKA MINAL-KHUBSI WAL-KABA'ISI.._

*ADDU'AR FITOWA DAGA BAN'DAKI.*

_GHUFRANAKA...._

*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*

_The hole page goes to masoyana kuma masoya novels en *RAYUWAR WANI* da *Y'AR GARUWA* ,iya wuya ina k'aunarku nima kamar yadda kuke k'aunata Allah ya barmin ku aduk in da kuke..._

*_~#REALLY HEART U GUYS..~_* 💔💔💔
*~_________________________~*

*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*

_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._

*~__________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*1⃣1⃣*

*T*ana gama fad'an haka ta juya ta shige d'aki,ba tare da damuwan komai a rantaba...

Sai da ta gama cin kukanta sannan ta tashi,ta tattare kayanta da suka zube,ta mai da su ciki..
'Dakin da ta gama gyarawa ta shiga ta sa kayanta daga gefe...
Nan ta takure guri guda tana mai had'a kai da k'afa,tana tunanin wannan rayuwar da ta tsinci kanta a ciki...

Cizon sauro shi yafi takurata,a d'akin haka suke kawo mata farmaki,ga zafi....
Zaman dirshan ta yi bacci ya gagareta,banda koran sauraye babu abunda take,wanda shima da k'yar take iya d'aga hannunta,daga k'arshe ma kasawa tayi,haka ta bar su tanaji tana gani,suke kawo mata farmaki...

Tana daga zaune ta jingina kanta a wall en d'akin,abun tausayi ga jikinta sai faman ciwo yake,ta rasa inda zata sa kanta,saboda azaba kanta kamar zai fad'o haka take jinsa,yanda take ji yasa ta fara cire tsammani da rayuwar duniyar...
Bakinta banda motsi babu abunda yake,da kallo kasan ba abunda take da ya wuce addu'a...

Idanunta a rufe haka hawaye ke layi ta gefen face enta,kukan ya gagareta.....

Da k'yar ta tashi lokacin da taji kiran sallah da asuba tana bin bango haka tayi alwala,ta sake komawa d'akin...
A daddafe tayi sallah daga zaune,ko addu'ah bata samu daman yi ba,wani wahalallen bacci yayi gaba da ita...

**********

Ba shi ya farka ba sai da gari ya gama yin haske,rana harta faso a garin...
Cikin wani irin yanayi na mutuwar jiki haka ya mik'e ya fita,yayo alwala ya dawo,a d'aki yayi sallah ya idar,haka ya zauna yana tunani amma ya rasa mai zai tuna...
A ganinsa akwai wani abu mai muhimmanci da yake son tunawa da shi,amma ya kasa tuna wannan abun...
Badan ya soba haka ya k'yale kansa,yana mai mik'ewa yayi hanyar fita daga gidan....

***********

Har gari ya gama haske rana ta gama haske garin,MA'U bata farka ba,haka itama KHUBRA,Bacci take a wahale...

Sai wajen k'arfe 12:30pm KHUBRA ta farka...
Idanunta take bud'ewa a hankali,duk sun kumbure saboda bata wani samu isashshen bacciba...
Sai da ta gama bud'esu tar,sannan ta mik'e ta zauna,sai da ta zauna ta huta...
Jikinta ba kamar da dare ba,yanzun har tana iya mik'ewa sosai,kantan kuma ta d'anji sauk'insa...

Kayanta ta tattare tana had'asu guri d'aya...

Tunawa tayi da abunda MA'U ta mata jiya kan dole ta mik'e ko dan kar a maimaita irin jiyan,ta d'auka tsintsiya tayi tsakar gida...

Tsaf ta share gidan ta,d'ebi ruwa tayi wanka,haka ta zauna a tsakar gidan,rana sai sake matsowa inda take.....

MA'U ce ta fito daga d'aki tana mik'a,ta nufi band'aki kamar wacce ake tunkud'awa,haka ta fad'a band'akin kamar an cillata,ko addu'ah babu...
Kamar sakkowar ruwan sama haka ta saki fitsarin da shigarta...

Tab'e baki KHUBRA tayi tana daga wajen,fuskarta duk maik'o...
A ranta take fad'in
''Wama ya sani ko ta fara a kwance ne?''...

***********

Tun fitowar ABBAN KHUBRA daga gida bai koma ba,haka ya yaci gaba da rayuwarsa a waje....

LADIYO an shanya baki sai bacci ake,ba ita ta tashiba sai azhur,ba don ta so tashin ba,sai dan cikinta dake ihun yunwa,fun da ta San babu wanda zai bata tana kwance...
Ba tare da tunanin gaida mahaliccinta ba ta shiga neman abunda za taci, rashin komai a gidan, yasata bazama neman MALAM BUBA haka take cilla fasassun k'afafuwanta...
Kitchen ta sake lek'awa neman duniya tayi aciki babu komai cikinsa sai busashshen k'anzon tuwo ta tsinto...
Haka bbau komai ciki bare mahad'i tayi ta garzarsa kamar akuya har ta cinye,sannan ta fito daga ita sai d'aurin zani iya k'irjinta....
Chapter 6 · 0% Book details