← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 86

Sashe 16

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kulle ta ga k'ofan har zata koma,sai kuma ta juyo a bakin k'ofan ta tsaya ta d'ora hannunta akan k'ofan ta shiga knocking....

KHUBRA dake zaune ta tallafe kumatu da hannayenta duka biyu tana faman sana'ar tunani taji ana knocking,da uwa bara ta bud'e ba,sai kuma ta tashi tana bud'ewa sukayi arba da ZUHRA,kallonta kad'ai tayi kafin ta shigo ciki....

Kanta a k'asa ta k'i yarda su had'a ido da ZUHRA,ita kuma ta kasa magana tun da ta shigo sai bin KHUBRAN take da kallo,da k'yar dai ZUHRA tayi k'ok'arin dakatar da shirun nasu...
''To meye na wani guduwa,kina gani ma na je k'ofan nasa anyi locking enta ta ciki''
Cike da jin haushi take yin maganar,sai cuno baki take yi gaba...

Ajiyan heart KHUBRA tayi nan ko ta soma kame²n abunda za tace,ZUHRAN ta katseta da fad'in
''Maybe ko akwai abunda yake amma gaskiya BB baya kulle k'ofa hakanan''

Fira suka soma kamar kowane lokaci sunata dariya abunsu,tuni sukayi fatali da wancan zancen...
Suna tsaka da dariyan ne HANEEF ya fad'o d'akin ba tare da Sallama ba yana haki ya hau fad'in
''YAH ZUHRA wai ki zo inji YAYA''

''Ok!muje gani nan zuwa yanzun''

Ficewa yayi a guje,tun kafin ta juyo KHUBRA tayi tsalle tana nufan hanyan toilet,juyowa tayi tana kallonta
''Ina kuma zaki yanzu,ki zo muje sai mu dawo tare''

''Eyyahhh!sis yi gaba zan biyoki kinga wanka zanyi,Allah yau zafi nake ji''
Duk ta wani marairaice fuska uwa za tayi kuka take maganar

Y'ar dariya ZUHRA tayi kafin ta mik'e tana tafiya
''Ke dai kya fad'i gaskiya dan kam tsaf na harbo jirginki,YAYANAH ne baki son gaisawa da shi,ai shi kenan ba komai dama duniya ta gaji haka''
Tana gama fad'in maganar tata tayi waje da d'an gudunta ta bar gurin...

Kafad'a KHUBRA ta d'age sama,alaman ko a jikina sannan ta shige toilet en.....

Tana shiga parlorn ta tarar da shi ya shirya tsaf cikin wasu k'ananan kaya sun matuk'ar amsar fatarsa,da sauri ta isa kusa da shi ta zauna
''BB nah gani''

''Waye yaje yanamin knocking k'ofa d'azun?''

''Laaaa! BB nice fa''

''Ok!nayi tunanin ko wad'ancan fitsararrun ne''

''Uhmmm!a'a,dama k'awata na kawo maka ku gaisa,wacce na fad'a maka ennan to ita cefa,kuma ko da baka nan tana yi maka add'uah idan ina bata labarinka''

Murmushi kad'ai ya mata kafin ya furta
''Ok na gode sosai''

''Yawwa BB ga breakfast enka can,amma koh sai ka canki mene mukayi''

''Uhmmm!ZUHRA Allah ya shiryamin ke kin cika shirme,muje ni kam''
Har sun nufi dinning area en wayansa ya fara ring da yake cikin parlor ya barosu,ZUHRA ce ta koma ta d'auko masa,aiko ta mik'o masa dai² time en wayan ya yanke...
Yana shirin dubawa wani kiran ya sake shigowa,d'an murmushi yayi kafin ya dai²ta fuskansa uwa ba shi yayi murmushinba,yana d'aukan kiran....
''Hello!yane da wannan safiyan zaka kirani?''

Banji me aka fad'a daga d'ayan side enba,kawai dai naji ya furta

''Ok!sai ka shigo en''
Tuni yayi hanging kiran sai kace shi ya kira...

'Dan juyawa yayi ya kalli ZUHRA da take tsaye har lokacin tana raba eyes uwa mara gaskiya
''UHUMMM!ke kuma tsaiwan mene kike haka ?''
Murya k'asa² yake maganar kamar baison magana,ko da yake na fuskanci haka d'abi'arsace....

Kujera ta janyo tana daga tsaye ta shiga serving ensa,yana can yana pressing phone baima san me take ba har ta kammala,ta zauna tana k'ok'arin soma cin nata,ya d'ago yana bin plates en da kallo....
Wani arnen smile ya saki lokacin da yayi arba da plate nasa,ko uffan bai ce ba sai da ya tabbatar ya k'oshi,tukun ya kalleta....
''Kai sis gaskiya ko wace ce tayi girkin nan ta burgeni coz ta gama sanin favourite nawa''

''Aaaaaa!BB mun iya dai''

''A'a fa ita dai ke ai aikin surutu kad'ai kike yi,bayan na gani da idona''

''Uhmmm!kawai dai BB santi kake yi,laaaaa!na manta k'awar nan tawace fa da na gama baka labari yanzun''
''Uhmmm!wai kam Sis a ina take ne,da har ta iya baro nasu gidan da safiyar nan tazo taya ki aiki?''

Sai da tayi dariya son ranta sannan ta iya magana
''BB a nan gidanfa take da zama''

Da sauri ya kalleta,coz bai gane inda maganarta ta dosa ba
''Ehh pha!a nan gidan take''
Nan ta kwashe komai na alak'arta da KHUBRAN ta sanar masa...
Ajiyan heart yayi,a ransa ko fad'i yake
''Tabbbb gaskiya tunda nake ban tab'a ganin housemaid kamar ta ba,gaskiya wannan ta daban ce''

''BB barin je gurinta na barota ita kad'ai''
Tun kafin ya bata amsa har ta fice daga parlorn,bayanta yabi da kallo yana jinjina al'amarin a zuciyansa,ko me ya tuna ya d'age kafad'ansa yana fad'in
''To ni mene ma na damuwa,da zan tsaya tunani''.....

Dafe kai yayi yana fad'in
''Ohh!God na manta ban sanarma Sisnah ba zanyi bak'o''

Dai² lokacin ASHNA ta shigo parlorn taci wasu k'ananan kaya duk sun d'ameta,wani kallo ya mata cike da harara,take ko zuciyarsa ta dad'a tunziro shi aiko ya hauta da fad'a
''Ke don kin raina mutane,uban waye ya sa kike irin wannan shigan a gidan nan,saboda kinga bana nan koh?to wallahi ki maida hankalinki jikinki in ba haka ba ina mai b'allaki,wawuya kawai kina girma kina dad'a cin k'asa,Allah ya sa na k'ara ganinki da irin wad'annan kayan kiga yadda zanyi da ke...........Kin b'ace min anan ko sai jikinki ya gaya miki?''
Yi yayi uwa zai tashi,aiko ba shiri ASHNAR ta kwasa a guje sai bedroom nata,bata sake fitowa ba,ta ci gaba da zama ciki....

FATAHIYYA ce ta fito idonta uwa na aljanu duk ya sha hauka,shi da ya kalletama dariya taso bashi,amma ya doje yak'i yi
''Ke je ki kiramun AUNTYNKI''

''YAYA wacce AUNTYN?''

kanta a k'asa uwa munafuka tayi tambayar,d'agowa yayi ya kalleta
''Wacce kika san ina nufi''

Ya bata amsa a d'an hasale,ba shiri ta fice dan tasan bata cikin gidan kam,d'akin KHUBRA ta nufa direct,sun rashe saman katifa sunata faman dariya ta shigo ,ko kallon arzik'i bata musuba su duka ta furta
''Ki zo inji YAYA''
Daga haka ta juya,ba tare da ta jira amsar ta ba...

"To barin je inji me kuma BB zai ce yanzun,yaukam ina shan kira gurinsa''

Kai KHUBRA ta sunkuyar k'asa dan yanzun kam bata san me zata yiba wanda zai ceceta don ma kada ZUHRA tace ta zo su tafi tare.....
Cikin ikon Allah da sauri ZUHRAN ta fita bata ko neme ta kan su tafi tare ba....
Godiya tayiwa Allah da hakan ta faru,aiko ta d'auko littafinta na da take rubutu cikinsa,nan ta shiga (bahas) kan girkin da za tayi yau.....
ZUHRA ce ta shigo tana tsalle,a hankali ta janye littafin daga kan fuskanta tana kallonta...

''Maza ta so sis,yau akwai aiki a gabanmu,dan BB ya sanarmin zaiyi bak'o yau kam,so yanzun ya kamata musan abun yi''

''Tohh!muje kada mu b'ata lokaci''
Da sauri ta zari hijab enta,ita kuma ZUHRA ta kama hannunta suka fice suna rufe d'akin....

A kitchen suka yada zango,nan kuwa suka kachame a kitchen en sai aiki suke suna hirarsu duk da mafi yawanci surutun na ZUHRA ne....
Misalin k'arfe 1:30 suka jiyo maganansu k'asa²,da yake lokacin sun kusa kammalawa,aiko nan suka dad'a bada himma......

Sun d'an jima da shigowa sannan HAJIYA MURJA da muk'arrabanta suka fito,ASHNA tana ganin bak'on aka chanza tafiya sai kwarkwasa take,aiko FATAHIYYA ma na ganin haka itama ta shiga gyara tafiyarta,ko wajen magana ma sai ta sirance murya tana gaida shi.....

A hankali ya d'ago yana kallonsu,gaye ajin farko a kyau,iya kwaliyya,tsafta,gayu,ya had'e cikin wasu k'ananan kaya sam banyi tunanin yana jin yaren da suka masa ba,take ko ya musu wani kallon k'asan ido yana amsawa da k'yar....
Duk bidirin da ake babu ZUHRA a gurin,suna can suna fama a kitchen....
Sun kammala komai setting teble kad'ai ya rage musu,aiko nan ZUHRA ta hau tsokanar KHUBRA kan sai dai ta fita da kayan,dan ta san da wuya ta fitan,coz ta fuskanci tun da YAYAN nata ya dawo bata tab'a gigin barin sun had'uba,ko mene hakan ke nufi ohhoo???....

Da kyar ZUHRAN ta soma kwasar kayan tana fita da shi dan tasan kam KHUBRAN ba zataba,tun da ta jiyo muryansu ASHNA da MAMA....
Drink en da take had'awa ne kad'ai ya rage basu fita da shiba,jin parlorn shiru yasa KHUBRAN zura hijab enta ta nufi hanyan fita a tunaninta tana ajiyewa sai tayi waje ba tare da sun had'u da kowa ba....

Sam bata yi tsammaniba,kanta a k'asa take tafiya har dinning arean,k'asa² taji magana wanda yasa ta d'ago a d'an tsorace,suna zaune dukansu a gurin wata harara HAJIYAN ta aiko mata da yasa ta dad'a sadda kanta k'asa still tayi a gurin har sai da HAJIYAN tayi magana....
''Me kike jira a nan gurin,kina b'atawa mutane lokaci''

A hankali ta ci gaba da tafiya har dinning en,sai dad'a janyo hijab enta take tana rufe fuskanta....
Ajiyewa tayi zata bar gurin,HAJIYAN ta sake dakatar da ita
''Waye zaiyi servings da kike k'ok'arin barin gurin?''
Dawowa tayi jikinta a sanyaye jikinta sai rawa yake,plate na farko da tayi serving ta mik'a gaban HAJIYAN saboda tafi kusa da HAJIYAN...

Duk su biyun sun tsaya kallonta yanda ta wani k'udundune kanta cikin hijab...

Shi dai BB tab'e baki yayi yana pressing wayansa,shima dai abokin nasa bakin ya tab'e ya koma yana duba wrist watch en sa....

Ta side ensu ta zagayo ta shiga serving nasu,tsaf ta kammala ta janyo cup's ta zuba drink ciki....

Hannu ya mik'a zai d'auka,ita kuma tana k'ok'arin ajiye d'ayan na hannunta,hannunsa ne ya tankwab'e nata aiko take suka zube masa a jiki,cikin sauri ya furta
''Ya salaam!''

Da saurin itama ta soma bashi hak'uri,still hijab enta na a yanda ta sashi,sweetest voice nata shi ya dokesu su biyun suka bita da kallo,ko kafin suyi aune tuni suka tsinkayo muryan HAJIYA MURJA tana fad'a cikin kaushin murya....

''Amma wannan kwoi sha³ kin rufe fuska dama uwa wata munafuka taya zaki san me kike?''

Dukkansu basu ji dad'in abunda tayi ba,hayaniyan da ZUHRA ta jiyo ne yasa ta fito da sauri daga kitchen,lokacin da ta k'araso gurin a lokacin ita kuma KHUBRA ta juya tana kuka ta nufi hanyan fita ko gabanta bata iya gani sosai....
Chapter 16 · 0% Book details