Sashe 55
Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuga kuwa da hud'uba kullum cikinsu take musamman idan ta fita tofa babu inda take zuwa sai gidan TABAWA,haka itama kullum cikin sintiri take a gidan nan,haka har suka k'ulla abunda suka k'ulla.
Wata rana da asuba lokacin bayan iya ta koma gida KHUBRA nada watanni biyu a duniya,bayan mun idar da sallah a masallaci na kamo hanyan dawowa gida,abunda ya faru a wannan ranar idan na tuno ina jin b'acin rai da nadamar abunda na aikata a wannan lokacin,a ranar ba d'akin FALMATA nakeba bayan shigowata saina tuna ai ranar ban tashetaba da zan fita kasancewar ina sauri zani masallaci,tuna hakan da nayi yasa na nufi d'akinta da sauri kasancewar gari har yayi haske sosai,da zuwana d'akin abunda ya d'agamin hankali shine na tarar da ita kwance tasa KHUBRA a gaba,daga bayanta kuma wani k'ato ne jikinsa ko riga babu ya rungumeta suna bacci a haka,ganin wannan abu ya d'agamin hankali sosai ban tsaya jiraba na shiga jibgar k'aton ihunsa shi ya farkar da ita dama jaririyarmu,dukan daya isheshi yasa shi ficewa a guje,idanuna sun rufe da tsantsan b'acin rai nan babu jira na fice daga d'akin.Faruwar hakan babu jimawa na sake dawowa a lokacin har tayi sallah jikinta duk a sanyaye,tana rungume da y'arta tana bata abincinta,na shigo babu b'ata lokaci nace ta shirya zamuje gidansu,ita dai har lokacin batayi maganaba kuma jikiinta yayi mugun sanyi fiye da farko dana tarar da ita a d'akin mayafinta kawai ta d'auka ta goya KHUBRA a baya muka kama hanya ni da ita haka har muka isa gidansu,da zuwa nace ta shiga ciki idan BABA na nan tamin sallama da shi,ta shige ta barni nan a k'ofar gida.
Bayan fitowar BABA muka gaisa a mutunce sannan na shiga koro masa bayanin abunda ya faru,shi dai yayi shiru yana saurarona har na k'are labari,sannan ya kalleni da mamaki shimfid'e a saman fuskarsa ya shiga fad'in
"Nayi mamaki daka zomin da wannan rikitaccen labarin naka mai kama da k'anzon kurege,kuma tabbas kaima ka bani mamaki da wani yazomin da wannan maganar wallahi da sai nayi k'ararsa amma da yake kaine mun barka da Allah,amma zan tambayeka wani abu game da y'ata,shin lokacin da kazo neman aurenta ka tarar da ita tana tara samari ne ko kuwa? sannan bayan ka aureta ka sameta a cikakkiyar budurwa ko a'a? tana da kamun kai ko a'a a bayan aurenku?"
Duka amsoshin d'aya ne A'a,tabbas ba haka halayenta suke ba,amma a lokacin da yake abunka sa sharrin zuciya sai nake ganin kamar fa ta aikata,nan na k'ek'asa k'asa na kuma dube shi nace
"Nifa BABA duka nasan ba haka bane amma na sani ko ta sauya hali ne bayan nan"
Sosai maganata ta b'ata masa rai amma sai ya danne ya ce
"To yanzu daka dawo da ita kuma me yake faruwa?
Nan ko na furta "Na dawo muku da ita ne,sannan kuma tunda Allah yasa haka halinta yake na saketa saki d'aya idan ta samu miji tayi aure..."
Ba sakin ne ya b'ata masa raiba illa cin mutuncin da nayi musu na saida na kawota har gida sannan kuma nace na saketa a gaban idonsa,nan ya ce
"To BUBA munji abunda ya faru mun kuma gode amma ka jirani na fito maka da y'arka,kamar yadda ka dawomin da tawa y'ar nima ina son tabbatar maka da bazan rik'e maka taka y'arba,saboda haka saika nema mata wata uwar"
Yana gama fad'in haka ya shiga gida ya fito hannunsa d'auke da jaririyar,nan ya mik'omin ita nako sa hannu na karb'a na mik'e zan tafi,maimakon na tafi sai na bud'e bakina na kuma kalli tsabar idonsa nace
"Kamar yadda ka bani y'ata in sha Allah zan rik'eta da yardar Allah kuma babu abunda zai samemu,kamar yadda zan tafi da ita yanzu to ko ku tabbatar na tafi da ita kenan bazaku sake ganintaba haka nima na tafi kenan ni da ku har abada...."
Ina gama fad'a masa ban jira ya sake maganaba nayi gaba abuna..
"Tun daga wannan rana rainonta ya dawo hannun IYA mahaifiyata saboda LADIYO ko kallo bata isheta ba,KHUBRA nada wata uku a duniya mahaifina ya rasu daga nan ne kuma IYA ta dawo gidanmu da zama a d'akin da FALMATA ta zauna,tana kuma ci gaba da kula da ita.
Kimanin watanni biyu da rasuwar mahaifina,IYA ta fara rashin lafiya a lokacin annoba ce ta shigo garin nan na amai da gudawa wanda kwanaki biyar da fara jinyar tata itama tace ga garinku nan,a wannan lokacin naji mutuwar nan da akamin a tsakanin watanni biyar na samu k'aruwa na samun y'a na kuma rasa mahaifana biyu..
Da farko na damu sosai bayan mutuwar IYA amma daga baya sai na dangana na koma ga Allah,sannan naci gaba da kula da KHUBRA duk wani abu da uwa za tayi mata ni nake mata shi dan LADIYO dai-dai da sau d'aya bata tab'a d'aukanta ba saboda tsanar da tayi mata.
Lokacin da bakinta ya fara bud'ewa na shiga koyar da ita karatun addini,a haka muka ci gaba da rayuwa duk inda zani ina tare da ita,bacci ma tare mukeyi a haka har Allah yasa ta fara wayo sosai ta fara gane wasu abubuwa.
Rana ta farko datamin wata magana na shiga damuwa amma sai dai na dake a lokacin data ke tambayeta ina UMMA'NTA? amsa d'aya na bata kamar yadda nayi alk'awarin bazan kaita gurin mahaifiyartaba shi ne nace mata ta mutu tun bayan data haifeta,ranar data ji haka yini tayi kamar mara lafiya,daga baya kuma ta ware kamar sauran lokaci.
Lokacin data k'ara girma shekarunta sun kai ta fara aikace-aikace gudun kada a zageni da kuma k'ananan maganganu dake tasowa yasa na fara barinta a gida sannan muka daina kwana tare,a lokacin ne kuma aikin gidan nan ya dawo kanta komai ita keyi tun bata iyaba har ta gama k'warewa,idan zani d'ibo ruwa ita ke karb'a ta tafi ta hanani zuwa,ina kallo tana wahala amma sam idan nayi magana sai ta nunamin babu komai..
Haka muka dunga rayuwa da dad'i babu cikin hukuncin Allah,har kuma ta zama budurwa,wanda nanma kyau irin nata data gado a wajen mahaifiyarta dan kam babu abunda ta bari na mahaifiyarta yasa hassada ta sake kunno kai ta b'angaren wannan dai shaid'aniya inda bata kyalemuba har sai da tayi nasarar rabamu..."
Nan ya kuma kwashe abunda ya faru tun daga barin KHUBRA a gidan har zuwa yau da suka zo ya sanar da su...
Al-ajabi kam sunyi shi,tasbihi kawai suke suna kuma jinjina abun,kan KHUBRA na cinyan ABBA'NTA banda kuka babu abunda take jin labarin mahaifiyarta da abunda ya faru,Allah ya isa kam LADIYO ta shata koma ince tana kan sha a gurin KHUBRA da sauran mutanen gurin musamman BB da ZUHRA da suke ganin kamar su hakan ya faru da su,kowa a zuciyarsa yake fad'in albarkacin bakinsa da kuma irin hukuncin da zai yanke mata saboda su a ganinsu hukuncin da ABBA ya yanke matama yayi kad'an...
Muryan ABBA'N KHUBRA tasa su maida hankulansu kanshi inda yaci gaba da fad'in
"Bayan faruwar wannan abun ne kuma wata rana ina zaune akayi sallama dani dana fita sai naga mutum tsaye ganin ban sanshiba na daure muka gaisa,sannan nace masa ban shaida shiba,shi ne ya kwashemin komai ya sanar dani,dama shi ne wanda na kama tare da matata,jin haka raina ya sake b'aci sosai amma sai ya shiga bani hak'uri sannan ya sanarmin shima sashi akayi kuma ba kowa ya turo shi ba sai LADIYO da taimakon k'awarta TABAWA,nan ya nemi gafarata na yafe masa sannan na sanar masa yaje ya nemi yafiyar wacce ya aikatawa laifin,na masa kwatancen gidansu saboda ni kam a lokacin bazan iya zuwa gidanba saboda a ganina da wane ido zan kalli wannan baiwar Allah ita da mahaifinta nace ina neman yafiyarsu? to kuma ana haka ne bayan wannan mutumin ya tafi,na shigo gida kwana biyu tsakani nayi MUGUN GAMO........"
Labarin mugun kamun da yayiwa LADIYO da wannan k'asurgumin tsohon banzan ya basu,nan kowa ya shiga fito da abunda ke bakinsa suna fad'in
"Sakayya ce Allah ya nuna mata,Allah ya wadaran hali irin wannan.."
LADIYO dai tana gefe babu baki sai ido tayi k'us da ita kanta a k'asa saboda kunya data lullub'eta ji take inama k'asar gurin ta bud'e ta shige,da tasan abunda zai biyo baya kenan da bata zaunaba,da tasan ta felle k'afafunta tun lokacin da MALAM BUBA'N ya saketa amma yanzun kam inaa lokaci ya k'ure mata...
*SOME MINUTE'S LEFT......*
Bayan wucewar wasu mintuna,an gama jimami da alhini,ABBA'N KHALEEL yake shaida ma ABBA'N KHUBRA cewa
"Ya kamata ka daure kaje gidansu domin neman yafiyar abunda ya wuce saboda idan babu rayuwa akwai mutuwa..."
"In sha Allah zanje na nemi gafarar BABA dama ita kanta FALMATAN..............."
😱😱😱😱😱😱😱.
*Huhhh!!! kunji fa fan's abunda ABBA'N KHUBRA yace kenan bai san MAMA'N KHUBRA ta jima da rasuwa bama ko me yake nufi???*
*~#TEAM KHUBRA.~*
*_#®EAL $MASHER._*
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*22/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣0⃣
*B* ayan k'ura ta lafa komai kuma ya dai-daita an gama jimamin abubuwa da suka gabata sannan kuma an shaidawa ABBA'N KHUBRA labarin yadda ta rayu a gurinsu a matsayin y'ar aiki da kuma matsayinta yanzun a gurinsu,daga nan kuma suka gangara kan mak'asudin zancen daya kawosu garin.
Sosai yayi farin cikin abunda suka sanar masa,daga nan ya shaida ma ABBA'N BB cewa
"Duk abunda kaga ya dace ka aikata SAFWAN ba sai ka neme niba idan ya so daga baya naji hukuncin daka yanke,saboda KHUBRA y'arka ce kuma bayan haka kuma kuna da hak'k'i akanta a matsayinku na iyayenta kuma dangin mahaifiyarta..."
Wannan karramawa da ABBA'N KHUBRA yayi masa yaji dad'inta,take kuwa shima ya yanke nasa hukuncin inda yace
"To Alhamdulillah! da Allah yasa al'amura suka kasance haka,gaskiya nafi kowa farin cikin faruwar hakan,amma magana biyu gareni zan fad'a yanzun kuma ba ga kowa ba sai kai MALAM BUBA"
Nan suka sake maida hankali gurin ABBA don jin me kuma zai fad'a
"Ina ganin a yanzu tunda abubuwa da dama sun faru zan nemi wata alfarma a gurinka..."