← Book details Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 86

Sashe 22

Yar Garuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin parlor ya kwanta idanunsa a rufe jijiyoyin kansa sun gama bayyana a fili,shi kad'ai yasan abunda yake ji a zuciyarsa,yanzun kam ko magana baya jin zai iya yi
''To amma ai bai kamata na ci gaba da zama ba yanzun,,,,,,,,me ya kamata nayi?''
Yayiwa kansa tambayar,saurin mik'ewa yayi ya koma bed room ensa,cikin abunda bai fi mintuna biyar ba ya fice daga gidan gaba d'aya.....

ZUHRA kam kasa fitowa ma tayi tana d'akinta,kuka take sosai tamkar wacce uwarta ta mutu,idanunta duk sun kumbure sun canja launi kan kukan da tayi,sai da ta ji cikinta tamkar babu komai ta fito da k'yar tana tafe tana bin bango har ta shiga kitchen...
Kallonta suka yi ganin yadda take bin bango,da ka suka tambayi juna sai dai babu amsa...

Kitchen ta shiga kallon gurin da KHUBRA ta saba tsaiwa tana aiki ta shiga yi,take wasu hawayen suka k'ara b'alle mata ganin babu KHUBRA cikin gurin da suka saba zama tare,sai da tayi kukan mai isarta da k'yar kuma ta iya dafa indomie a plate ta juye ta d'auka tayi bed room enta.....

Kallonta suka sake yi,coz tun tana cikin kitchen en suke jiyo k'amshi na tashi,gaba d'aya sun rashe suna jiran ta gama ta basu,aiko tana barin gurin suka shiga da sauri suna dubawa...
Wayam babu komai ciki haka suka janyo tsummokaran k'afafunsu suka fito,guiwoyinsu a sake....

《《》》

Fitarsu daga d'akin ta sauke wani gwauron numfashi,wayarta ta janyo ta shiga kiran HAJIYA LAURA...
Bata wani jima tana ringing ba ta d'auka cike da izza da k'asaita kamar d'iyar sarauta....

''Aiki yayi kyau mutuniyata,yanzun kam yaranmu sai yanda mukayi da su''...

''Ban fuskanci me kike nufi ba''
HAJIYA MURJA ta tambaya cike da zak'uwa da son jin labarin...

Take ko ta zayyane mata sawa tayi aka d'auke KHUBRAN daga garin,ta k'arashe zancen da fad'in
''Nasan yanzu kam tayi nisa da mu''
Wata dariya ta saki ta makiran mutane....

Sai lokacin hankalin HAJIYA MURJA ya kwanta tana fad'in
''Mun rabu da alak'ak'ai,jarababbiya aje can a k'arata''....

Tana sakin dariya itama,sun jima suna shirya makircinsu kafin suka yi sallama....

*_~TEAM KHUBRA~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠

*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹

*©®2018*
*14/ʍɑվ,2018*

*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*

_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
_Ga masu buk'atar son kasancewa da group na *Y'AR GARUWA* za ku iya yin joining ta hanyar amfani da wannan link en,saboda gujewa had'uwa da maza,mata zallah dan Allah👏..._
👇
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EvdAvnFbBaX2BBMAwCCH4E
*~________________________~*
🍟🍟🍟🍟🍟
🎂 *HAPPY BORN DAY*🎂
_OUR SURIKI *HASSAN ATK*_

🎊
🎉🎉🎉
_A birthday is just the first day of another 365-day journey around the sun. Enjoy the trip. *HAPPY BIRTHDAY*_

🍻🍻🍻
🎂🎂🎂

*ONCE AGAIN..HAPPY BIRTHDAY*

H A
A
S T
S
A K
N
💃💃💃💃💃
*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_

*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._

*2⃣7⃣*

*G*idansu KHALEEL ya yanke shawarar zuwa danko baya tunanin a yanzun yasan abunda ya kamata ya aikata...
Driving kawai yake ba dan yana da nutsuwar da zai iya kai kansaba,ikon Allah ne kad'ai ya kaishi,idanunsa sun koma jaa yayin da ta tsakiya har wani layi² yayi na coffee....

Shigansa harabar gidan bayan yayi parking ya nufi hanyan parlor,ta balcony ya hangosa zai shiga parlor,da yake KHALEEL ba mutum ne mai rik'o ba,shi kamar UMMIN sa yake,suna da sanyin hali...
''MAN!''.......
Ya fad'a da d'an k'arfi ta yadda BB en yajiyo shi,d'an waiwayawa yayi ya kalli gurin da yaji maganar,inda yake ya nufa fuskarsa babu annuri a tare da ita...
Chairs en da ke gurin ya zauna yana mik'a masa hannu,duk wani motsinsa idanun KHALEEL na kansa,ganin yadda ya chanja ya koma wani silent duk da dama bai da yawan magana...

''MAN lafiya kake kuwa?"
Kallonsa kawai yayi da rinannun idanunsa...
Sam KHALEEL bai kula da yadda idanunsa suke ba,sai yanzun da ya d'ago...
Cikin tashin hankali KHALEEL ke tambayar BB
''MAN dan Allah ka fad'amin abunda ke faruwa,kaga kuwa yadda ka koma wani abun tsoro.......Dan Allah ka sanarmin abunda yake faruwa,ni kaina hankalina ya gaza kwanciya''

Hawayen da suka fara sauka kan fuskar BB masu matuk'ar k'una su suka dad'a sawa hankalin KHALEEL ya kai mak'ura wajen tashi,zuba masa ido kawai KHALEEL yayi,sai dai sam shi kansa hankalinsa baya tare da shi,ga shi BB en ya kasa masa magana bare ya gano dalilin damuwar tasa.....

《《》》

''Dan Allah d'an uwa nan a ina nake?''
Kallonta yayi yadda take magana baiyi tunanin irin yaren da zai fito daga bakinta ba kenan,daurewa yayi ya bata amsa,yayin da yake k'are mata kallo from head to toe,hawaye ne suka sake b'alle mata,nan ko yaci gaba da kallon ikon Allah,shi dai bai san dalilin kukan ba bare ya bata baki tayi shiru,haka ya ci gaba da kallon ikon Allah har sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru....
Tsab'an kukan da tayi muryanta har ya shige cike baka jin sautin muryanta idan tana magana har sai ka kalli yadda lips enta ke motsi....

Tunanin inda ya kamata ta nufa yanzun take,nan zuciyoyinta suka shiga fafatawa gurin ganin sun bata shawara...
''Shin gidanmu ya kamata na nufa ko kuwa?''
Take wata zuciyar ta sake bata shawaran
''A'a kawai ki koma gidan BABA MA'U''
Ta yi zurfi cikin tunaninta,har lokacin kuma ta kasa samun matsaya guda d'aya,duka kuma ta kasa yin na'am da shawarwarin da zuciyoyintan ke bata...

Tana zaune tana ta kallon jama'a dake ta faman hada-hadar kasuwancinsu,yayin da yara suka sata gaba da ihun ga balarabiya,wasu suce y'ar india ce,da k'yar wanan mutumin ya kore su suka bar gurin....

''Dan Allah MALAM a ina zan samu motan da zai kaini''......
Sai kuma ta d'an karkatar da kai gefe alamar tunani....

《《》》

''A kwai matsala MAN,ban san ya zan billowa al'amarin ba''
Shiru ya d'an yi ya kasa ci gaba da magana sai iska da yake furzarwa,wacce take fitowa cike da hucin zafi..

''Wace irin matsala ne wannan?ni kam duk ka d'agamin hankali,kai kana cikin damuwa,nima ina cikin damuwa.....Buh...Ka k'i sanarmin abunda yake faruwa''....

''Sun sa...ce......ta''
Abunda ya iya furtawa kenan,ko shima sai da yayi kokawa da kalmomin kafin suka bayyana,ta yadda za a gane....

Ido KHALEEL ya fiddo waje
''Wa aka sace? ZUHRA?ko wa???''

Kai ya shiga kad'awa cike da takaici baya ga k'uncin da yake ziyartarsa,zuciyarsa ta gama yin duhu,a iya wannan lokaci baya gane komai.....

''Uhmm!ita suka sace''
Ya sake maimaitawa,shikam KHALEEL ya kasa fuskantar wa ake nufi
''Dan Allah kamin bayanin da zan gane sosai.....Wace ce aka sace?.......Na tambayeka ZUHRA ka ce a'a,wace to daga cikin y'an gidan''

A tak'aice ya furta
''Wannan YARINYAR''

Fad'in hakan da yayi shi yasa ya fuskanci inda zancen ya dosa,take ko ya mik'e tsaye yana maimaita
''HASBUNALLAHU WA-NI'IMAL WAKEEL!!''

Da k'yar ya iya samun guri ya zauna,sun d'auki tsawon lokaci babu wanda ya iya magana cikinsu......

Ransa a b'ace yake fad'in
''Tabbas duk wanda yayi wannan d'anyan aikin,wallahi imaninsa ragagge ne,sam basu da tausayi bare imani....Laifin me ta aikata musu da zasu aikata mata wannan d'anyen hukuncin.....Baiwar Allah babu ruwanta......Wanda duk yake da hannu kan wannan aikin ya cancanci hukunci mai tsaurii''

BB kam ya kasa magana,har KHALEEL ya gama surutansa baibi ta kansa ba,tunani yake sonyi amma sam k'wak'walwarsa ta k'i karb'an ko wane irin hayaniya...
Kafad'ansa ya kalla jin an dafa shi,hannun KHALEEL yabi da kallo,lokaci guda shi kansa KHALEEL en har ya sauya kamanni...

''MAN tashi muje''

''Ina kuma zamu?''
Da k'yar BB ke tambaya

''MALAM kawai ka tashi muje,wannan lokacin bana tunani bane bare b'atawa''

Ganin BB en yak'i motsi yasa KHALEEL bugun shoulder ensa yana fad'in
''Ka tashi mu wuce''

K'in tashi yayi,wanda hakan da yayi ya k'ara fusata KHALEEL en
''Kada Allah ya sa ka taso en,wannan damuwar da kake nunawa duk na banza ne''...
Bai samu daman k'arasawa ba saboda wani banzan kallo da BB ya wurga masa cikin matsanancin fushi ya mik'e
''Me ka sani game da al'amarina da ita da har za ka fad'i haka?Wannan damuwar da nake nunawa duk na banza ne ko ba haka ka fad'a ba?''
Wani murmushi yayi wanda da gani kasan sam bai dace da lokacin da aka yishiba....
''Yeahhh! na fad'a idan da ace ka damu ya kamata ka biyoni muje''

''Baza ka tab'a fuskata ba''
BB ya fad'a yana girgiza kansa....

《《》》

'Bangaren MA'U kam zuwa yanzun duniya sabuwa,al'amura sai dad'a ta'azzara suke,neman maza yanzun ya zame mata jinin jikinta,duk inda take suna manne da farkokintan,babu gida babu waje yanzun har ta kai ga takan kulle gidan tayi ficewarta sai ta yini bata gidan....
Idan ta dawo kuma to za a tarar da ita da wani suka dawo bata tab'a iya kwana ita d'aya...

Duk ko ranar da duniyancintan ya motsa ranar ba zaka tarar da ita gidaba gaba d'aya k'arshe a hotel zata kwana,koma ta shafe tsawon kwanaki kamar dai wacce tayi tafiya ganin gida.....

《《》》

''Unguwan Miltara ko Rijiyan lemo......Wanne ne ma a ciki?''
Tama kanta tambayan,tana ta faman son ta tuna,idanunta sun koma ciki,duk kuwa da yanda KHUBRA ke da yalwar idanu...

''HAJIYA na ga kin kasa tunawa,me zai hana muje gidana''
Ya fad'a yana kallonta,yana kuma kallon abunda ke rungume jikinta,d'an kallonsa tayi da jan fuskanta,ita dai haka kawai taji ta aminta da shi,amma kuma taya za ta amince,ta sani ko bashi da aure,haka kawai ya kaita gidansa alhalin bashi da aure...
Shiru tayi bata ce komaiba,shi kuwa sai kallonta yake da k'unshin bak'in ledanta dake rungume jikinta har lokacin...

Kamar ya san abunda take tunani akai aiko ya shiga fad'in
''Ki yarda muje babu abunda zai faru dake yanzun haka y'ay'ana hud'u da mata ta''

Jin haka yasa ta mik'e ba tare da tunanin komaiba tana fad'in
''Muje to na gode sosai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi''

Y'ar dariya yayi ba tare da ya amsa ba,ya shiga tura kurar ruwansa ita kuma tana biye da bayansa,suna tafiya babu wanda ya kuma tankawa wani a cikinsu.....

《《》》
Chapter 22 · 0% Book details