← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 75

Sashe 9

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya juya ya fice, ya bar su cikin damuwa da rashin tabbas. Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah da Hammad, zuciyarta na bugawa da karfi.

“Ya Allah, ka kawo mana agaji.” Ta furta cikin sanyin murya...

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE: 9_

Hajiya Zaytunah ta runtse idanuwanta da ƙarfi, zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi. Kamar yadda ta taɓa jin irin wannan firgici a baya, haka take ji yanzu, amma wannan ya fi komai muni. Ta dubi gefenta, tana kallon Nabeeha da Hammad da ke a daure kamar yadda ita ma take. Sun yi shiru ba tare da sun furta uffan ba, amma idanuwansu sun bayyana tsananin tsoro da damuwa.

Ta juya idanunta cikin ƙwaryar ɗakin da ake tsare da su. An ajiyesu ne a wani wuri da ya yi kama da tsohon daki, katako ne ke rufe jikin bangon, kuma kowane lungu cike yake da ƙura. Abin da ya fi damunta shine sanin cewa har yanzu ba su san waye ke da alhakin wannan Kamen nasu ba, kuma ba su san me suka yi da har hakan ta faru da su ba.

Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, zuciyarta cike da addu’a. Shin wannan tashin hankalin zai ƙare lafiya kuwa?

A daidai wani dare mai tsananin duhu, cikin wani lungu da baƙin duhu a wani yanki na barikin da suka fake, wani guntun mutumi dake cikin yan fashin ya taho da waya a hannunsa, daya hannun nasa rike da torchlight. Ya mikawa daya daga cikin 'yan fashin da suka kama Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha. Takardar da aka rubuta da dogayen kalmomi masu nauyi, wato in bold letters ta turo text message din Suna ɗauke da umarni daga wacce ta fi kowa kula da lamarin - Hajiya Rumanah.

Kuna cikin bakin aiki, kuma babu wani kuskure da zan lamunta daga gareku. Haka nan, babu wasa a cikin wannan danyen aiki da aka damka muku. Zan yi muku magana ta gaskiya, kuma dole ne ku aikata abin da nake so cikin gaggawa.

Ga umarni na a gareku,

Na farko,
Za ku yanke gashin wannan annamimiyar (Hajiya Zaytunah) ku aiko mini da shi. Gashin kanta dole ne ya iso hannuna. Babu buƙatar yawan tambayoyi ko ɓata lokaci. Idan har ta ƙi yarda, ku tabbatar kun yanke shi da karfi da yaji. Idan ta yi ihu, to ku ƙara mata azaba!

Na biyu,
Kada ku sake a bar wannan ƴar wulakancin (Nabeeha) ta kubuta cikin salama. Idan har za ta rayu bayan wannan dare, to dole ne a ɗauke mata mutuncinta! Ku tabbatar an shanye duk wani alamar mutunci daga jikinta kafin ku bar ta ta numfasa. Idan ta mutu cikin tsananin azaba, to hakan ma zai zama alheri.

Babu wani kuskure da zan yarda da shi! Idan kun yi sakaci, ku sani cewa rayuwarku ce za ta biyo baya. Ku sanar da ni idan kun kammala.

Mutumin ya gama karanta sakon, zuciyarsa ta cika da kasala. Duk da ya saba da aikata muggan laifuka, ya san cewa wannan umarni ya wuce gona da iri. Kallon wasu daga cikin abokan aikinsa ya yi, kowanne yana jiran a ce komai. Daga ƙarshe ya kalli wanda ya kawo sakon ya ce:

"Wannan matar ba zata taɓa yin imani da ƙwaƙwalwarmu ba. Ita ba ta kula da komai sai mugun nufinta!"

Daga gefe, wani daga cikin 'yan fashin da ke jin maganar ya murmusa, yana kaɗa kai,

"Dama mun san cewa akwai wani abu da ke ƙasa da wannan lamarin. Ba so kawai ake su mutu ba, ana son a bar musu tarihi da abin da zai ruguza su tsawon rayuwarsu."

Duk da haka, babu wanda ya ce uffan na tsawon lokaci. Shirun ya yi yawa, sai ƙarar wata tsuntsuwa da ta ketara ta wuce cikin duhun dare. Daga bisani, babban shugaban 'yan fashin ya gyara zamansa, ya saki numfashi mai nauyi sannan ya ce,

"Za mu bi umarninta. Amma idan wata matsala ta taso, sai mu yi tunani kafin mu dauki mataki."

Suka yi shiru na wani lokaci, kafin wani daga cikinsu ya tashi tsaye ya ɗauki wani almakashi, yana kallon shi da kyau kamar yana nazari.

A cikin duhun dare, aka fara tsarawa domin aiwatar da mugun aikin da Hajiya Rumanah ta bayar...

A cikin dakin da aka kulle Hajiya Zaytunah da Nabeeha, ana iya jin numfashinsu yana fita cikin sauri da tsoro. Wutar fitila guda daya ce ke haskaka dakin, tana bayyanar da inuwa a bangon da ke nuna yanayin tsoron da ke tattare da su.

Hajiya Zaytunah tana zaune a gefe, hannayenta daure da igiya, idanunta sun kada saboda tsananin damuwa. Nabeeha kuma tana a gefenta, jikinta yana rawa, zuciyarta cike da tsoron abin da zai biyo baya.

A waje kuwa, daya daga cikin 'yan fashin ya dubi shugabansu, yana girgiza kai cikin shakku.

"Mun san aikinmu ne, amma wannan ai ya yi yawa."

Shugaban ya kalle shi da idanun da suka cika da rashin jin tausayin komai.

"Hajiya Rumanah ba za ta ji daɗin jin cewa ba mu aikata abin da ta umurce mu ba. Kuma ba na son jin bayanin kowa. Za mu aiwatar da umarnin nan da aka bayar!"

Ya juya yana duban wani daga cikinsu, wanda aka fi sani da Gora, ya ce da shi,

"Kai ne za ka shiga ka yanke mata gashi."

Gora ya haɗiye yawu, yana jin wani irin sanyi yana ratsa zuciyarsa. Duk da kasancewarsa da ƙwarewa a aikata laifi, wannan lamarin ya ɗauke shi a matsayin wani mummunan aiki da zai bar tarihi mai muni.

Ya ɗauki almakashin da aka ba shi, sannan ya sa hannu ya tura ƙofar dakin. Kamar yadda ya zata, idanun Hajiya Zaytunah sun zazzaro da ganinsa, tana kallon almakashin hannunsa.

"Mene ne kake shirin yi?" Ta tambaya da muryar da ke rawa.

Gora bai ce komai ba. Ya matsa kusa, zuciyarsa na dukan uku-uku. Ya tsugunna a gabanta, yana kallon gashinta da ke nade cikin mayafi. Ya san cewa wannan ba abu ne mai sauki ba, amma ya san cewa idan bai aikata ba, rayuwarsa tana cikin hatsari.

Hajiya Zaytunah ta fahimci manufarsa nan take. Ta motsa a inda take daure, tana kokarin janye kanta.

"Kada ka kuskura!" Ta ce, idanunta sun cicciko da hawaye.

Gora ya runtse ido yana shirin saka almakashin a cikin gashinta, amma zuciyarsa ta gaza. Sai ya sauke almakashin a kasa, yana jan numfashi mai nauyi.

A waje, sauran 'yan fashin suna jiran jin motsin da zai tabbatar da an yi aikin. Shugaban ya daka tsawa:

"Meye ya tsaida ka?"

Gora ya goge zufar da ta bayyana a goshinsa, sannan ya dubi shugabansu da fuskar da ke nuna rashin yarda da lamarin.

"Ba zan iya ba," Ya ce cikin sauti mai ƙasa.

Shugaban ya fusata, yana matsowa kusa da shi.

"Kana nufin kana ƙin yin abin da aka umurce mu?"

"Ba haka bane," Gora ya amsa, yana kokarin kare kansa. "Amma wannan abu ya wuce gona da iri. Wannan matar ta riga ta wuce wahala. Me yasa ba za mu yanke kanta gaba daya mu huta ba?"

Shugaban ya kara harzuka, sai ya finciki almakashin daga hannun Gora.

"Ka matsa gefe!" Ya ce da tsawa.

Ya shiga dakin cikin sauri, ya kama gashin Hajiya Zaytunah da karfi, yana kokarin yankewa.

A take, Nabeeha ta tashi tsaye, tana kiran cikin kuka,

"Don Allah, kada ku yi haka, Dan Allah !"

Shugaban bai saurare ta ba, sai kawai ya ci gaba da yankewa. Gashin da ya faɗi daga kanta ya shiga cikin wani farin leda da aka tanada, sannan ya kalli wasu daga cikin 'yan fashin.

"Ku shirya, za a aika da sakon nan zuwa wajen su."

Da wannan umarni, wani daga cikin 'yan fashin ya ɗauki ledar, ya fice daga dakin, yana shirin aika da sakon.

A waje kuwa, wata matsala mai girma ta taso saboda wasu daga cikin 'yan fashin sun fara nuna shakku akan abu na biyu da aka umurce su da su aikata…

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE: 10_

A cikin dakin da aka kulle su, Hajiya Zaytunah ta kasa motsi yayin da idanunta ke zub da hawaye. Numfashinta ya tsananta, zuciyarta tana harbawa da sauri. Duk da azabar da aka yi mata da yankar gashinta, wani abu mafi muni ya fi tada hankalinta, wato abin da zai biyo baya...

Nabeeha ta kankame jikinta, tana jin gabanta yana faduwa da wani irin tsoro da ba ta taba jin irinsa ba. A zuciyarta, tana rokon Allah ya kawo mata mafita. Idanunta sun cika da hawaye, amma ta kasa kukan da zai sa su nuna rauni.

A waje kuwa, shugabansu ya sake duban sauran ‘yan fashin, yana furta abin da ya fi rudani.

“Ku tabbata an aiwatar da abu na biyu da Hajiya Rumanah ta bukata.”

Da jin haka, gaba daya ‘yan fashin suka yi shiru. Wasu sun zuba masa ido, wasu kuma suka dauke kai. Ko da sun saba da aikata miyagun ayyuka, hakan ba zai sa su yi wannan aikin da ya zama wulakanci ba.

Wani daga cikinsu, mai suna Bala, ya kalli shugaban da ido kamar yana tunani.

“mu dan dakata mu dauki lokaci kafin mu aiwatar da wannan,” Bala ya ce, yana kokarin kaucewa matsalar.

Shugaban ya dube shi da harara.
Chapter 9 · 0% Book details