← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 75

Sashe 19

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai ce komai ba, sai ya sunkuya kadan cikin girmamawa... Da kunyar data gama dabaibaye shi. Sai a lokacin ya tuna da baranbaramar da yayi. Na rike mata hannun 'ya gam sai kache zaa kwace masa ita. Ya sosa keyarsa yana sake sunkuyawa.

“Ina wuni, Aunty..”

Ta kalle shi, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da mamaki. A lokacin da ta tuno wannan yaron a baya, sai ta dauka mutum ne mai yawan fushi da fadin kai da rashin kulawa. Amma a yau, sai ta fahimci cewa akwai wani zurfi mai girma a halayensa.

“Lafiya lau, Captain Fawaaz. Allah ya saka da alheri.”

Ya dan gyada kai a hankali, sannan ya juya ya kalli Hammad, wanda ke tsaye yana kallonsa da murmushi.

“senior man. Da fatan kalau kake?” Ya tambaye shi da wata murya mai laushi.

Hammad ya gyada kai, yana murmushi. “Eh, Yaya.. Ba wani abu.. mungode Allah ya saka da alkhairi.”

Fawaaz ya dan shafi kansa a hankali, yana jin wani irin yanayi na tausayin su duka. Sun shafe lokaci cikin tsoro da damuwa, amma yanzu suna nan cikin kwanciyar hankali.

Ya dubi duka mutanen fashin da aka kamo na sauran dazukan. Ya sauke katuwar ajiyar zuciya, ya tabbatar da cewa babu wanda ke da wata gagarumar matsala.

Sai ya kara wa Nabeeha kallon ƙarshe, kafin ya juya zuwa ga abokan aikinsa.

“Mission accomplished.” Ya furta da kwarin gwiwa. “Let’s go home.... Soldiers. Weldone"

Hajiya Zaytunah ta kalli Fawaaz da idanu masu cike da gaskiya da nauyin abin da take shirin furtawa. Ta numfasa, sannan ta ce da murya mai taushi tana Mai Saka hannu tana nuni da gora da bala..

"Fawaaz, akwai wani abu da nake son ka sani. Wadannan mutanen nan guda biyu, Gora da Bala—tabbas sun kasance cikin waɗanda suka yi fashin da suka kama mu tun farko. Amma daga baya, su ne suka taimaka mana muka kubuta. Sune suka cire mu daga hannun ‘yan fashin, suka dawo da mu inda kuka same mu a cikin dajin nan. Da awata bukka aka ajiye mu ana azabtar da mu."

Ta kalli Gora da Bala, wadanda ke tsugunne, fuskokinsu a kasa cike da fargaba da shakku. Daga bisani ta ci gaba,

"Tabbas sun yi mana adalci. Duk wasu munanan ayyukan azabtarwa da aka bukaci su aikata mana, sun ki aikata su. A zahiri, sun butulce wa shugaban su ne don su taimake mu. Da ba don su ba, da har yanzu muna hannun ‘yan fashin, ko ma fiye da haka..."

Ta yi shiru na wani lokaci, tana kallon Fawaaz kamar tana neman karbuwa daga gare shi. Sannan ta ce da murya mai tausayawa,

"Don haka, ina rokonka, a kyale su. Na san cewa ba mugaye bane. Sun yi abin da za a iya kira da sadaukarwa domin su ceto mu. Ina neman afuwarka a bar su su tafi, domin sun riga sun zabi kyakkyawan hanya a lokacin da suka yanke shawarar taimakonmu."

Fawaaz ya saurara ba tare da ya ce uffan ba. Idanunsa sun kada, yana nazari. Daga can gefe, Bala da Gora suka ji zuciyarsu na bugawa da karfi, suna jiran hukuncin da zai biyo baya... Don fawaaz din bana wasa bane. Fuskar sa yadda ya hade rai yana duban su goran zakasan soja ne mai cikakken Iko..

Fawaaz ya dauki lokaci yana nazari, yana kallon yadda Hajiya Zaytunah ke magana da cikakkiyar gamsuwa. Idanunsa sun sauka kan Gora da Bala, wadanda suka kasa hada ido da shi, kamar suna jiran kaddarar su.

Daga can gefe, Hammad ya matsa kadan ya ce da rauni,

"Kuyi tunani sosai. Idan suka ci gaba da zama a hannun mu, me zai faru da su? Shugaban yan fashin har basu sako yayi yace an bashi umarni a raba sister Nabeeha da mutuncin ta..Kuma goran ya saka da bala amma ba wanda ya amince yayi acikin su. Da kansa shugaban ya yanke gashin Ammi..... "

"What? A raba nabeeha da me?" Fawaaz ya fada yana cakumo wuyan Hammad tamkar shi yayi masa lefin. Can ya sake shi ya juya yana naushin mota.

Hajia zaytunah tayi kansa tana bashi hakuri tare da kwantar masa da hankali,

"Ai Allah bai basu dama ba. Allah bai amince ba. Ba abunda ya faru da ita. Basu kai ga cinma burin su ba. Waɗannan yara gora da bala sune suka kubutar da mu."

Fawaaz bai ce komai ba. Sai dai yana jin zuciyarsa na yarda da bayanan Hajiya Zaytunah. Idan da gaske wadannan mutanen sun butulcewa ‘yan fashin domin ceton su, hakan na nufin akwai ragowar mutunci a zuciyarsu.

"Alhamdulillah..." Ya ambata yana sauke zuciya..

Ya dago kai ya dubi Bala, sannan ya watsa wa Gora kallon bincike.

"Kun san abin da kuka aikata. Ku ne kuka taimake su, amma kuma kun kasance tare da su tun farko. Me yasa?"

Bala ya gyada kai, yana kokarin samun karfin guiwa.

"Mun shiga rayuwar fashi da makami ne saboda rayuwa ta tilasta mana. Ba mu da mafita a baya. Amma bayan mun ga irin wahalar da mutane ke sha a hannun manyan mu, zuciyarmu ta girgiza. Ba mu iya ci gaba da kallon hakan ba. Mun san cewa abu ne mai hadari, amma mun zabi taimakon su."

Gora ya daga kai da sauri ya kara da cewa,

"Kuma da mun so mu tafi tare da ku, amma kun san cewa idan muka bayyana kanmu a wancan lokacin, ba wanda zai yarda da mu. Mun yanke shawarar bin bayanku daga nesa, domin mu tabbatar kun tsira lafiya."

Fawaaz ya sake duban Hajiya Zaytunah, sannan ya dauki tsawon minti yana tunani. A karshe, ya numfasa ya ce,

"Ku tafi. Get lost.."

Gora da Bala suka dago da mamaki. "Ka yafe mana?"

Fawaaz ya girgiza kai, yana kallon su da tsananin natsuwa.

"Ba wai an yafe muku ba ne, amma kun nuna cewa kuna da damar gyarawa. Ku fita daga nan kafin wasunmu su canza shawara."

Hajiya Zaytunah ta yi murmushi a hankali, zuciyarta ta saki da jin dadin yadda lamarin ya kaya. Bala da Gora suka mike da sauri, suna mai godiya, kafin su ruga cikin daji da sauri, suna fatan samun sabuwar rayuwa.

Hajiya Zaytunah ta kalli Fawaaz ta ce, "Ka dauki babban mataki yau. Ka nuna halin jagora."

Fawaaz bai amsa ba, sai dai ya ci gaba da kallo cikin nesa, zuciyarsa cike da tunani.ya juya yayi mata murmushi kawai yana Jan kasan leban sa.. domin wata gagarumar kunyar ta ce take dimauta shi..

Bayan Gora da Bala sun bar wurin, shiru ya ratsa tsakanin su Hajiya Zaytunah da Fawaaz. Kowa na nazarin abin da ya faru. Hammad ya numfasa da nauyi, sannan ya ce,

"Da ace wasu ne, ba za su taba barinsu su tafi ba. Amma gaskiya sun cancanci a basu wannan damar."

Hajiya Zaytunah ta gyada kai cikin gamsuwa.

"Hakane. Rayuwa ba ta da tabbas. Watakila wata rana, su ma su ga damar taimakon wani."

Fawaaz ya mike tsaye, yana yamutsa gira kamar wanda ke jin wani abu a zuciyarsa.

"Ba wai na basu dama ne saboda sun cancanta ba. Na basu dama ne domin sun fi wasu mutanen da muka hadu da su kyau. Kuma na fi son su yi tafiyarsu fiye da barinsu a nan suna ci mana zarafi ko su zama barazana."

Hajiya Zaytunah ta fahimci cewa ko da yake Fawaaz bai furta kai tsaye ba, amma zuciyarsa ta karaya da yanayin da Gora da Bala suka shiga. Idan da Fawaaz ne a matsayinsu, da watakila shima ya dauki irin matakin da suka dauka.

Hammad ya kada kai yana murmushi. "Ko dai yaya ne, ai hakan ya nuna kai mutum ne mai tunani da adalci."

Fawaaz bai ce komai ba. Ya dan matsa gefe yana duba yanayin wurin.

"Muna bukatar mu koma cikin gari da wuri. Wannan wurin bai da aminci sosai."

Hajiya Zaytunah ta gyada kai. "Hakane. Allah yasa mu dache"

Fawaaz ya yi shiru, yana nazari. Yana jin yadda tsananin gajiya ya lulluɓe shi, amma bai so ya bayyana hakan. Duk da haka, yana fahimtar cewa hakan ne kawai mafita.

Daga can gefe, Hammad ya dago yana kallon sararin samaniya.

"Da alama, gobe zata kasance wata sabon kamawa."

Hajiya Zaytunah ta murmusa.

"Allah ya sa hakan ya zama mafi alkhairi."

Su Fawaaz suka shirya don barin dajin. Hajiya Zaytunah ta daura gyale a kanta, fuskarta cike da nutsuwa, yayin da Hammad ya ja tsaki yana yamutsa fuska.

"Ba zan ce komai ba, amma daji bai dace da ni ba," ya fada yana shafa wuyansa. " idan na koma gida, sai na kwana rana biyu ina barci inshaa Allah.. God I'm soo tired."

Fawaaz ya dan kalle shi daga gefen ido.

"Ka ce ka fi so a bar ka a hannun ‘yan fashin?"

Hammad ya girgiza kai da sauri.

"What? Noo! Omo.. A’a fa! Na gode wa Allah da muka tsira. Amma dai... gaskiya sai nayi sati ina cin abinci mai kyau don dawo da kuzari. "

Hajiya Zaytunah ta yi murmushi. "Allah ya kai mu lafiya."

Ba tare da bata lokaci ba, suka fara tafiya cikin dajin, suna bin hanyar da za ta mayar da su cikin gari. Duk da cewa ba su san ko wani hadari zai sake zuwa ba, sun yarda cewa komai zai tafi daidai...

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE: 16_

A lokacin da motocin suka soma tafiya cikin dajin, an samu nutsuwa sosai fiye da daa. Hasken fitilar motocin na haskaka hanya, yana bayyana ƙurar da take tashi a kan titin ƙasa. Kowa a cikin motar ya yi shiru, kowanne da tunanin da yake yi a zuciyarsa.
Chapter 19 · 0% Book details