← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 75

Sashe 5

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Roger that, captain yanzu ya zamuyi what's next? "

"Muyi grouping into 4,. Ku nan ku yanki dajin kudu, ku kuma dajin yamma, Ku Kuma nan haka gabas zakuyi. Kai da Kai da Kai muyi arewa. Let's go.no time ...move it soldiers.."

"Aye aye captain" suka amsa shi cikeda zafin nama da Kuma girmamawa. Motocin su suka shisshiga suka fara barbazuwa cikin dazukan don neman su Hajiya Zaytunah..

Captain fawaaz suna tafiya acikin mota yana jera tsaki ba adadi. Ya sauke numfashi Mai zafi yana dartse lebensa. Mahaifinsa ya kira a awaya ya sanar masa yadda suke ciki ya karkare da,

"Amma mun rabu wings hudu sir, yanzu haka Muna mota ma zamuyi arewa. Inshaa Allah su aunty, Hammad da Nabeeha zasu dawo gidah cikin koshin lafiya in Allah ya yarda"

"Allah ya amince captain. Sannu ku da kokari" major general ya amsa a sanyaye a nasa bangaren..

Gwaggo Hafsatu da tunda suka fara wayar take dubansa ganin sun kammala wayar bai ce komai ba ya sata cewa,

"Wani abune ya faru?"

"Aa inshaa Allah kalau Gwaggo. Ai sun barbazu ma cikin dazukan kudu da arewa, gabas da yamma. Su Hajiya Zaytunah zasu dawo gidah cikin koshin lafiya inshaa Allah"

"Toh Allah ya amince dawuda. Allah ya yarda dawuda. Allah ya kawo karshen wannan mummunan labari Amin"

"Aameen Gwaggo.. Aameen"

Yana rufe bakinsa. Wayar sa ta fara Kara. Ya dauka ganin chief judge Abdulfatah ne. Bayan sun gaysa yake sanar dashi dazu jikin Gwaggo ne ba lafiya. Ankwantar da ita a asibiti ma amma sun dawo gidah..

"Toh shikenan babu damuwa... Allah ya kawo su lafiya. Okay kai baka nan ma? Ayyah ehh. Supreme court. Toh Allah ya bada saa. Alright sai munyi magana. Nagode. Zataji inshaa Allah yauwa sai ka dawo"

Ya katse Kiran yana hurar da iskar bakinsa Mai tsananin zafi..ya dubi gwaggo yache,

"Abdulfatah ne. Yana duba jikin naki. Yana miki sannu yace na gayshe ki idan ya dawo zai zo ya dubaki inshaa Allah. Wai shugaban kasa ne yake neman su da gaggawa kan shari'ar nan ta supreme court."

"Allah sarki... Nagode kwarai. Allah yabada saa"

"Aameen gwaggo. Sai Kuma yake sheda mun mahaifan Muhammad mai neman Nabeeha sun taho suna kan hanya zasu karaso gidah"

Ya karasa fada yana duban gwaggon da itama shi take kalla. Allah yaso su biyu ne a parlorn. Daga ita sai shi. Hajiya Hauwa ta tashi.

"Tohh fa... Allah ka kawo mana sauki... "

"Aameen Gwaggo. Yanzu ya zamuyi kenan?"

"Dawuda ni kaina banida abun cewa.. Bamuda wani abun fada. Kaga dai halin da muka tsinci kanmu aciki ma. "

"Ko ca za'ai musu sunyi tafiya basa nan? Nabeehan"

"Toh kadai san me zaka sanar musu... Allah zai shiga cikin lamuran namu in Allah ya yarda"

"Aameen gwaggo. In shaa Allah"

Bai karasa rufe baki bayan maganar da yayi. Horn din dake jikin gate din gidan mai bada sauti ga bakin motocin da suka dososhi ne zasu shigo ya farayi ba kakkautawa. Inda masu gadin kafin su danna permit button sai da suka kira intercom na sashen major general dawud suka sanar masa. Nan yace abude musu bakin sane...

A lokacin da su Alhaji Amiru, Alhaji Uzairu, Muhammad, Gwaggo Zainabu, da mai aikinta suka iso gidan Major General Dawud, an shigo da su ta babban kofar gidan, inda masu gadin gidan suka gaishe su cikin ladabi. A nan ne suka zarce zuwa cikin babban parlour, inda aka sauke su domin jiran Major General Dawud.

A yayin da suke zaune, ma’aikatan gidan suka shiga da kayayyakin da suka kawo. Manya manyan ledoji shake da kaya. Da kwalaye. Harda Karin wasu akwati guda biyu...

Akwatinan da suka ƙunshi kayan kyauta da wasu kayayyakin alatu, da manyan kwalaye.. Akwai ma wasu ledodi na kaya da aka mika wa wata daga cikin masu aikin, wadda ta shigar da su zuwa ɗakin da Gwaggo Hafsatu ke amfani da shi.

A hankali, an gama sauke komai, sannan aka tabbatar da cewa babu wani abu da aka bari a waje. Duk da cewa ma’aikatan ba su fahimci dalilin kawo kayan ba, sun kasance cikin girmamawa da kwarewa, suna kokarin yin komai ba tare da hayaniya ba...

Bayan ma’aikatan gidan sun gama shigar da kayan cikin tsari, daya daga cikinsu ya iso kusa da Alhaji Amiru cikin ladabi, yana sanar da su cewa an kammala jera kayayyakin a inda ya dace.

Gwaggo Zainabu ta ɗan zubawa parlourn ido, tana nazarin yadda gidan yake. Ita kanta ta san cewa gidan ba ƙaramin gida ba ne, kuma tsarinsa yana nuna cewa yana ɗauke da duk abubuwan jin daɗi. Sai dai hakan bai hana ta jin wani ɗan ɗaci a ranta ba, saboda tunani da damuwar da take ciki.

Muhammad ya matsa kusa da mahaifinsa, yana dan shafa KIRJIN sa da hannunsa kamar mai son yin magana amma yana kokarin kame kansa. Alhaji Uzairu kuwa, ya ɗan lumshe ido na wani lokaci, yana jin shiru da yanayin gidan ya lullubesu.

Gwaggo Zainabu ta kalli mai aikinta, wadda ke tsaye cikin nutsuwa kusa da ita, sannan ta ce da ita da sassanyan murya,

"Samu waje ki zauna kema.. sannu da kokari"

"To Hajiya," mai aikin ta amsa a ladabce, sannan ta juya zuwa hanyar wani dan corridor da kujera a wajen ta zauna tana nazarin kawataccen parlorn dayaci kayan kudi ya lashe..

A dai-dai wannan lokacin, wata daga cikin masu aikin gidan ta iso kusa da su cikin nutsuwa, sannan ta rusuna cikin girmamawa tana cewa,

"Barkan ku da zuwa. Yallabai yana zuwa yanzu."

Alhaji Amiru ya jinjina kai kawai ba tare da ya ce komai ba. Amma yana cikin zurfafa tunani. Ya san cewa wannan zama ba sauki ba ne, kuma ya shirya yin duk abin da zai yi don tabbatar da cewa an warware matsalar da ya kawo su.

Gidan ya kasance cikin tsananin shiru, kowannensu yana cikin tunaninsa, har sai da aka fara jin alamun takun mutum yana matsowa daga waje...

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE: 6_

  A hankali, cikin kasaita da nutsuwa, Major General Dawud ya taka zuwa cikin babban falon gidan nasa, inda bakin suka hallara. Yana ɗauke da wani irin kwarjini da kamun kai da suka dace da mutumin da ya saba da shugabanci.

Da zarar idonsa yana sauka kan Gwaggo Zainabu, wadda ke zaune cikin kamala da haiba, sai ya taka da girmamawa, yana sunkuyawa kaɗan cikin dattako. A matsayinta na babbar macen data Isa ta haife shi, kuma dattijuwa mai cikakken daraja, ya san dole ya gaisheta da irin gaisuwar da ta dace da ita.

A nutse, cikin ladabi da haiba, ya ɗan rusuna kaɗan, yana faɗin da murya mai zurfi da cike da girmamawa,

“Ranki ya daɗe, Hajiya barka da wannan lokaci. Kun zo kalau?. Allah Ya ƙara lafiya da nisan kwana. Allah Ya ƙara girma da daraja.”

Gwaggo Zainabu ta kalle shi da murmushin jin daɗi, tana jin daɗin yadda ya girmamata kamar yadda ya kamata. Ta amsa cikin kulawa da jin daɗi,

“Alhamdulillah! Sannu da kokari. Yaya aiki? Allah Ya ƙara maka nasara da rufin asiri.”

Ya ɗaga kai cikin girmamawa, yana amsawa,

“Amin, Hajiya. Mun gode da addu’a. Allah Ya bar mana ke.”

Bayan ya gama gaisheta da mutuntaka, sai ya juya zuwa sauran da suka zo. Ya miƙa wa Alhaji Amiru hannu, yana kallonsa ido cikin ido da cikakken mutuntaka.

“Sannu da zuwa, Alhaji Amiru. Da fatan an zo kuma hanya lafiya?”

Alhaji Amiru ya kama hannun nasa da ɗan murmushi, yana gyada kai.

“Lafiya kalau, Major General. Mun gode da kulawa.”

Bayan haka, ya miƙa wa Alhaji Uzairu hannu, suma suka gaisa cikin mutuntaka da ladabi.

A ƙarshe, idonsa ya sauka kan Muhammad, matashin saurayin da ke zaune kusa da mahaifinsa.

Muhammad Hammad, da zarar idonsa ya haɗu da Major General Dawud, sai ya ji wata irin kunya da girmamawa sun mamaye shi. A matsayinsa na mutum mai natsuwa da kamun kai, Muhammad ya san yadda ake mutunta manya, musamman irin su Major General Dawud, wanda shahararsa da mutuncinsa sun bazu a ko’ina. Uwa uba kuma mai babban matsayi ga zuciyar da yake kaunar kasancewa da ita wato Nabeeha..

A hankali, ya miƙa masa hannu cikin girmamawa, yana faɗin da wata murya mai cike da girmamawa,

“Ina wuni, Baba barka da war haka.”

Major General Dawud ya karɓi hannunsa da kulawa, yana kallonsa da idanu masu zurfi, amma ba tare da ya nuna wani abu a fili ba. Ya fahimci yadda Muhammad ke ji a lokacin, kuma bai da niyyar tsorata shi ko sanyaya masa guiwa.

“Lafiya lau, Muhammad. Ya wajen su mama?”

Muhammad ya gyada kai cikin girmamawa, yana cewa,

“Alhamdulillah, suna lafiya.”

Bayan haka, Major General ya matsa kaɗan ya zauna cikin kwanciyar hankali, fuskarsa na bayyana cikakken nutsuwa da sanin ya kamata.

Duk da cewa kasancewarsa mutum mai ƙwarewa a lamurran tsaro ya sa yana da natsuwa da ƙarfin zuciya, yana da kyakkyawar dabi’ar girmama mutane, musamman waɗanda suka girme shi da shekaru ko matsayi.

A cikin falon, an ɗan yi shiru na wasu ‘yan dakiku, kowa yana duba yadda yanayin zaman zai kasance. Kafin a soma tattaunawa kan batun da ya kawo su, Major General Dawud ya ɗauki lokaci yana duban fuskokinsu, yana nazarin yadda kowannensu ke kallon sa.

Wannan shiru da nutsuwa da ya nuna, ya ƙara tabbatar wa da su cewa mutumin da ke gabansu ba mai sake-sake bane. Sai dai duk da haka, yana da halin yin biyayya da girmama waɗanda suka cancanta. Tuni maaikatan suka cika gaban su da abinci da sauran abubuwan motsa baki..
Chapter 5 · 0% Book details