← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 75

Sashe 67

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali, ta buɗe baki. Ya saka mata abincin cikin taushin hali, yana kallon ta yadda take ci. Sai da ta haɗiye sannan ya ce, “Daga yau, zan kula da ke fiye da yadda kike zato.”

Hannunsa ya ɗora saman nata, yana dan matsawa. “Nabeeha, kin san me yasa nake son ki haka?”

Ta girgiza kai a hankali, idonta yana cikin nasa.

“Saboda ke ce wacce zuciyata ta amince da ita tun kafin ki san hakan. Ke ce nutsuwa ta, ke ce addu’ata. Kin san yaushe na fara son ki?”

Nabeeha ta ɗan lumshe idanu, tana jin wani irin sanyi na ratsata.

Fawaaz ya ɗan yi murmushi, yana ci gaba, “Tunda na gane cewa ba za ki iya rayuwa da ciwon kewa ba, na rantse a raina cewa zan dinga kasancewa kusa da ke. Amma sai na lura cewa soyayyar da nake ɓoyewa ta fi ƙarfi fiye da abin da na zata.”

Nabeeha ta kafe shi da idanu, tana jin yadda kalamansa ke ratsa zuciyarta. Dama ya iya kalaman magana haka? Haka ya iya tsara zance? Haka ya iya zuba soyayya tamkar a film? Ta murmusa kawai, kalaman sa na ratsa magudanar jini da tsokar jikin ta.

Fawaaz ya ɗauki wani cokali na abinci, ya sake miƙa mata. “Ki ci, domin na san dole ne ki sami ƙarfi. Ba na so ki rame saboda tunani ko damuwa.”

Bayan sun gama cin abinci, Fawaaz ya jasu sallah tare. Ya tsaya yana kallon yadda take yin addu’a da nutsuwa. Idanunsa sun cika da ƙauna da girmamawa.

Bayan sallar, ya matsa kusa da ita, yana ɗora hannunsa saman nata. “Allah ya bar min ke, Nabeeha. Ina addu’ar alheri a gare ki, kuma ba zan daina ba.”

Sai dare ya ja, suna tare cikin kwanciyar hankali, zuciyoyinsu sun haɗu da juna ba tare da wata shakka ba. Wannan shi ne matakin yarda—matakin da babu komai face soyayya da kulawa ta gaske.

Daren ya tsawaita, amma Fawaaz bai damu ba. Yana kallon Nabeeha da wata irin nutsuwa da bai taɓa jin irinta ba a rayuwarsa. Idanunsa sun cika da so da kulawa, zuciyarsa tana bugawa da wani irin shauƙi da yake wahalar bayyana.

Ya sake kamo hannunta cikin nasa, yana jin yadda tafin hannunta ke da ɗumi mai daɗi. "Nabeeha," ya ambaci sunanta a hankali, kamar yana jin daɗin furta shi.

Ta ɗago idanuwanta da suka cika da kwanciyar hankali, tana kallonsa.

"Kin san cewa zuciyata ta dade tana son ki?" Ya tambaya da muryarsa mai laushi.

Ta lumshe idanuwa a hankali, tana jin wani sanyi yana ratsata. "Na sani, Ya fawaaz."

Ya ɗan yi murmushi, yana jin yadda furucinta ke ƙara ƙarfafa shi. "Amma ba wai kawai son ki nake ba, Nabeeha. Ina ƙaunarki da zuciyata gaba ɗaya. Ina kallon ki, ina jin kamar kin mallake ni tun kafin ma ki sani. A yau, babu wata shakka, babu wata shinge. Na baki zuciyata gaba ɗaya."

Nabeeha ta lumshe idanu, ta ɗan saki numfashi mai nauyi. "Ni ma na yarda da kai, Yaa Fawaaz. Na amince da kai fiye da kowa. Ka daɗe kana ɓoye komai, amma zuciyata tana karanta ta taka, ko da baka furta ba."

Fawaaz ya murmusa, yana jin yadda furucinta suka saukar masa da natsuwa. "Kin san me yasa na daɗe ina ɓoye soyayyata?"

Ta girgiza kai, tana jiran jin amsar sa.

"Saboda bana son zuciyata ta takura ki. Bana son na ɗora miki damuwar da ba ki shirya da ita ba. Amma yau, ba zan iya ɓoye komai ba. Nabeeha, kin mallake ni gaba ɗaya."

Hannunsa ya ɗaga ya shafi fuskarta a hankali, yana kallon yadda idanuwanta ke cike da ƙyau da kwanciyar hankali. "Duk da haka, ina son ki fiye da abin da zan iya furtawa. Ina addu'ar Allah ya tabbatar min da ke."

Hannunta ya sake rikewa, yana matse shi a hankali. "Kuma daga yau, ina son na dinga kula da ke. Ba zan bar ki da yunwa ba, ba zan bar ki da damuwa ba. Ba zan bari wani abu ya taɓa ki ba, har abada."

Nabeeha ta sunkuyar da kanta, zuciyarta tana bugawa da nauyin farin ciki.

Fawaaz ya kalli fuskarta, sannan ya kai hannunta zuwa KIRJIN sa. "Ji yadda zuciyata take bugawa saboda ke, Nabeeha."

Hannunta ya ji yadda bugun zuciyarsa ke da ƙarfi, yana tafiya da daɗin ƙauna mai tsafta.

Daren yana ƙara ja, amma babu wanda ya damu da lokaci. Sun shagala cikin soyayyar da take tafiya a hankali, cikin tsafta da aminci.

Fawaaz ya dubi kyawun fuskarta, sannan ya lumshe idanu. "Ina addu’a Allah ya albarkaci rayuwarki, Nabeeha. Ina addu’a ki kasance cikin farin ciki har abada."

Sai ya sake kallonta da murmushi. "Kin yarda da ni?"

Ta gyada kai, murmushi yana bayyana a fuskarta. "Na yarda da kai, Ya fawaaz."

Daga nan, shiru ya ratsa tsakanin su, amma zuciyoyinsu suna magana fiye da furuci. Wannan matakin da suka kai ba wai kawai soyayya ba ce, aminci ne, kulawa ne, addu’a ce da ba ta yankewa.

Soyayyarsu ta kai matakin da babu komai face tsarkin zuciya da yarda. Wannan matakin ne da ba zai taɓu ba, har abada.

,,,,,,

A hankali Hammad ya turo kofar falon yana rike da basket dauke da warmers na abinci. Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya shiga, yana murmushi.

"Assalamu Alaikum."

Nabeeha ta dago daga inda take zaune tana duba wayarta. "Wa’alaikumus Salam, Hammad! Dear bro..iyye me muka samu? "

Ya ajiye ledojin a kan teburi yana fadin, "Abinci daga gidan Granny. Tace a gaishe ku."

Fawaaz, wanda yake zaune gefen kujera yana kallon wasan kwallon kafa a TV, ya dan kalle su, sannan ya mayar da hankalinsa ga wasan.

"Nagode sosai," Nabeeha ta fada tana bude ledar don ganin me aka kawo. "Sannu da kokari ."

Hammad ya yi murmushi yana zama. "Babu komai. Yanzu dai ku ci kafin yayi sanyi."

A lokacin Fawaaz ya dan juya kansa ya kalli Hammad. "Ya fawaaz barka da rana"

Hammad ya gyara zama, yana murmushi. "Lafiya kalau, bro"

Fawaaz ya dan kada kai, ya maida kallonsa kan wasan da ake yi a TV. "Daga gani Barcelona ce take wasa da Real Madrid."

Hammad ya yi dariya. "Eh mana! Kuma kaga yadda suka rike ball, ai dole su yi nasara."

Fawaaz ya dan gyara zama yana kallon yadda ake buga wasan. "A ganina Real Madrid suna da damar cin kofin wannan shekarar."

"Wallahi kuwa," Hammad ya amsa, yana kallon TV. "Messi dai ba wasa ba ne, amma kalli yadda Benzema ke kokari."

Suka dan ci gaba da hirar kwallon kafa na tsawon mintuna kadan, kowannensu yana fadin ra’ayinsa kan wasan. Sai da suka ji sun dan gamsu, sannan Hammad ya sauke numfashi yana gyara zamansa.

"Yaa Nabeeha, Yaa Fawaaz... zan koma makaranta gobe in sha Allah."

Nabeeha ta dago da sauri, tana kallonsa da mamaki. “Hammad? Haka kawai? Da wuri haka?”

Fawaaz bai ce komai ba, sai dai ya dan kalli Hammad.

Hammad ya gyada kai. "Eh, hutuna ya kare, dole na koma."

Nabeeha ta dan lumshe ido. "Allah ya kiyaye hanya."

Fawaaz ya gyada kai. "Allah ya tsare."

Hammad ya mike yana murmushi. "Nagode. Zan tafi yanzu, sai mun yi waya."

Nabeeha ta raka shi da kallo, zuciyarta cike da kewar tafiyarsa. Fawaaz ya ci gaba da kallon wasan, amma yana sauraron yadda Hammad ke ficewa daga falon.

Bayan dan lokaci, Nabeeha ta numfasa a hankali. "Zan rasa yawan damun Hammad kenan."

Fawaaz bai ce komai ba, sai dai ya dauki remote ya kara volume din TV kadan, yana mai mayar da hankalinsa ga wasan da ake yi.

Tuwon shinkafa da motar ganye dataji tantakwashi. Sai peppersoup na kaji da gasasshen cat fish. Sai doya da kwai da kunun gyada. Sai fruits da meat pie da samosa. Lamarin sai Wanda yagani kawai....

Fawaaz ya Mike ya dakko tray ya zuzzuba musu komai. Ya karasa wajen nabeeha batayi aune ba tajita a sama. Fawaaz ya daga chak ya dora ta akan cinyarsa..

Ya samu kansa da juyar da fuskar ta ya kamo labbanta da nasa yana tsotsar bakinta...

Hannunsa daya Kuma ya zura shi rigar ta yana wasa da abubuwa Mafi soyuwa daga jikinta a zuciyar sa..

"Na...k...ko... Shi" ta fada a rarrabe tamkar zata shide saboda sabon lamarin da hannun fawaaz keyi acikin rigarta.

"Sai da ruwan ciki akejan na rijiya... Beautiful Nabeeha" fawaaz ya radamata a kunne yana lasar gefen kunnen ta.

Ta sauke ajiyar zuciya da kyar tana ajiye sautin numfarfashi...

Ta shiga zame hannun fawaaz amma ya riketa kam. Sai dayaga ma jagulata sannan ya kyaleta yana bata abincin a baki. Sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta...

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:60_

Fawaaz ya Mike tsaye yana mikawa Nabeeha hannunsa. Dakyar ta iya kama nashi ya mikar da ita yana rarumar ta. Ya rungumeta tsam wanda zaa kwace masa ita..

"Muyi wanka mu raya daren yau ko love?"

Nabeeha tayi shiru batace dashi komai ba. Gabanta ya tsananta bugawa fat fat fat.
Chapter 67 · 0% Book details