← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 75

Sashe 49

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Amiru ne ya fara magana da muryar nutsuwa, amma a ciki akwai wata alama ta tuhuma.

"Ina Zaytunah?"

Gaba ɗaya suka dubi juna, sannan suka girgiza kai da ƙarfin gwiwa.

"Mun ce ba mu da masaniya," cewar rumanah, tana kallon Alhaji Amiru da kyar.

"Tun batan da tayi shekaru da suka wuce, ba mu sake jin labarinta ba," in ji Hajiya Rumanah.

Alhaji Amiru ya kalli kowannensu ido cikin ido, sai ya sake tambaya, "Ina Zaytunah?"

Gaba ɗaya suka mayar da amsa iri ɗaya, ba tare da wata alamar shakku ba,

"Ba mu sani ba."

Sai da ya sake tambaya karo na uku.

A wannan karon ma, babu wanda ya canza furuci, "Ba mu sani ba."

Sai kawai ya murmusa, yana daga kansa sama da jinjina labban sa. A take ya mike tsaye, yana mai daga dogon gyale yana gyara hularsa. Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya juya ya fita daga falon.

Ba a jima ba, sai gashi ya dawo. Amma ba shi kaɗai ba, yana shigowa tare da wasu sojoji biyu, hannunsu rike da wani mutum da aka daure da ankwa.

Bokan ne!

Bokan da suka taɓa kaiwa don a mata asiri!

Cikin tsananin firgici, suka miƙe gaba ɗaya, fuska ɗauke da fargaba. Hajiya Ladi ta dafe KIRJIN ta, tana duban bokan da tsananin tsoro.

Hajiya Karama ta shiga rawa a tsaye, muryarta na kerma. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!"

Hajiya Rumanah kuwa, sai ta sunkuyar da kai, jikinta na rawa. Muhammad ya daskare a kan kujerarsa, idonsa waje yana kallon mahaifiyarsa da kuma sauran matan. Bai iya cewa uffan ba.

Alhaji Uzairu ya cilla musu wani kallo mai cike da takaici. Kamar wanda ya daɗe yana shakkunsu, amma yau shaidar ta bayyana.

"Kun janyo wa kanku," Alhaji Amiru ya furta da kakkausar murya. "Kun janyo wa kanku!"

Alhaji Uzairu ya sake kallonsu, zuciyarsa na cunkushe da ɓacin rai.

"Na gama zama da ke! Na gama!!" Ya faɗa da ƙarfi, yana daga murya.

A take a wajen, cikin shaidun da ke zaune da tsaye, ya dankarawa hajia rumanah saki uku..

Shiru ya ratsa falon. Kamar an ajiye dutse a cikin iska. Kowacce cikinsu ta ji tamkar an caka mata wuka a zuciya.

"Allah! Uzairu, ka duba da kyau!" Hajiya Ladi ta kurma ihu, tana dafa hannunsa.

"Wallahi ba laifinmu bane! Hajiya Rumanah ce ta ɗora mu a hanya!" Ta ƙara faɗi, hawaye na zubo mata.

Hajiya Karama ma ta durƙusa da sauri, tana roƙo: "Wallahi ita ce ta sa mu! Ba mu da hannu cikin hakan!"

Amma sai Hajiya Rumanah ta yi saurin miƙewa. Idanunta sun cika da hawaye, amma har yanzu tana da ɗan ƙarfin hali.

"Karya su ke yi! Su ne suka sa ni ciki! Ni ba ruwana!"

Muhammad ya cije lebensa. Wannan wane irin abu ne yake faruwa? Mahaifiyarsa ce da ta shuka irin wannan mugunta..

Da zarar suka hango shi, gaba ɗayansu suka miƙe tsaye cikin razana.

"Boka?!?!" Hajiya Ladi ta furta da wata muryar da ba ta saba da ita ba.

Muhammad, ɗan Hajiya Rumanah, wanda tun farko ya kasa fahimtar me ke faruwa, ya ji gabansa ya faɗi. Ya tsure da ganin mahaifiyarsa cikin wannan tashin hankali.

Idanunsu sun ciko da tsantsar tsoro, yayin da boka ya kada baki cikin wata murya mai cike da mugunta,

"Gaskiya ta fito! Dukan ku ne kuka haɗa baki kuka raba Zaytunah da mijinta! Ku ka raba ta da 'ya'yanta! Ku ka hana ta dawowa cikin danginta! To yau kun ƙare!"

Gaba ɗayansu suka daskare, jikinsu na rawa. Kamar su yi magana, amma harsunansu sun makale.

Alhaji Uzairu ya yi ajiyar zuciya mai nauyi. Babu shakka, idanun shi sun cika da takaici, kuma lokaci ne ya nuna masa gaskiya. Bai tsaya wata-wata ba, a take ya dubi su uku, da murya mai ƙarfi da ba ta buƙatar maimaitawa,

"Na sake ki saki uku, saki uku... Uku! Babu sauran zaman aure tsakanina da ke"

Wani irin shock ya kama su. Gaba ɗayansu suka girgiza kai, suka durƙusa suna roƙon sa, amma kamar ya gama yanke hukunci.

Hajiya Karama da Hajiya Ladi sun zabura suna kuka, suna cewa ba su da laifi, wai Hajiya Rumanah ce ta jefa su cikin wannan hali.

Ita kuwa Rumanah ta zabura cikin ɓacin rai, ta nunasu da yatsa tana cewa,

"Karya suke yi! Sune suka ɗaura ni a ciki! Ni ba ruwana!"

Duk parlorn ya cika da hayaniya, yayin da kowacce ke ƙoƙarin wanke kanta. Amma daga Alhaji Uzairu har Alhaji Amiru, babu wanda ya damu da jin bahasi.

Gwaggo Zainabu, wadda tun farko ke zaune shiru, ta dafe kai tana kallonsu da takaici. Tana jin kamar zuciyarta za ta fashe. Idanun ta sun ciko da hawaye.

A nan, Alhaji Amiru ya ɗaga hannu ya dakatar da hayaniyar, sannan ya dubi su da tsantsar ƙiyayya,

Gaba ɗayansu suka girgiza cikin matsanancin firgici. Babu wanda ya iya cewa komai, sai dai kuka da nadama. Amma ya riga ya kure musu.

Muhammad ya sunkuyar da kansa, yana jin wani irin bakin ciki a ransa. Yau ya ga wata fuskar mahaifiyarsa da bai taɓa zato ba. Yau komai ya gama tonuwa!

Gaba ɗaya falon ya dauki shiru na wani lokaci. Sai kukan Hajiya Ladi da Hajiya Karama ke tashi, suna durƙushe a ƙasa, suna roƙon Alhaji Uzairu da kada ya raba su da shi. Amma a yau, ba zai saurare su ba. Ya yi ajiyar zuciya, ya dubi su da kallon takaici, sannan ya ce da kakkausar murya,

"Kuka ɓata mini aure na, kuka raba ni da iyalina, kuka hana ni jin daɗin rayuwa na tsawon shekaru! To yau kun ga sakamakon abinda kuka aikata! A fitar mini da su daga gidana. Na sake ku Kuma saki uku uku!"

Jin haka yasa Hajiya Rumanah ta zabura da sauri, ta dubi shi da idanunta cike da hawaye. Tana neman mafita, amma babu ko ɗaya.

"Yaya Uzairu, ka saurareni! Ni ba ruwana! Ni fa su ne suka jefa ni cikin wannan fitinar! Dan Allah kabawa Yaya Amiru hakuri"

Ta nuna Hajiya Karama da Hajiya Ladi da yatsa, tana kallonsu da tsantsar ƙiyayya. Su kuwa suka yi saurin juyowa suna fadin:

"Karya take! Ita ce ta ja mu! Ita ce ta kitsa komai! Mu fa ba mu da hannu!"

Sai dai babu wanda ke son jin uzurinsu. Muhammad yana zaune a gefe, idonsa jajir, yana kallon mahaifiyarsa da matan kanin babansa suna zagin juna. A zuciyarsa, akwai bakin ciki da takaici. Mahaifiyarsa da yake ji da ita, ita ce jagorar wannan zalunci? Bai iya gaskata hakan ba, amma abun yana a bayyane.

Ya juya yana kallon Alhaji Amiru, wanda ke tsaye yana kallon su da ɗarɗar. Ya girgiza kai cikin takaici, sannan ya ce:

"Tun da kun ce ba ku da hannu a cikin wannan lamarin, to menene wannan?"

Ya ɗaga hannu ya nuna bokan da aka daure da ankwa, wanda ya tsaya a gefe yana kallon su da murmushin raini.

"Shin bokan ma ne ya ɓullo da kansa? Ko kuwa wani ya tura shi?"

Gaba ɗayansu sun toshe baki, sun kasa cewa komai. A yau, komai ya fito fili.

"Bari na baku labari!" Bokan ya furta da wata murya mai nauyi, yana kallonsu da raini. "Wadannan matan nan da kuke gani, su suka zo wajena, suka nemi a raba Zaytunah da mijinta. Suka nemi a tozarta rayuwarta, suka hana ta dawowa. Kuma suka ɗauka cewa za su ci nasara har abada. To yau, kuzo ku fuskanci sakamakon abinda kuka aikata!"

Hajiya Ladi da Hajiya Karama suka zabura da sauri suna girgiza kai.

"Wallahi ba mu da hannu!"

"Wannan boka karya yake! Bamu san shi ba!"

Hajiya Rumanah ma ta yi saurin cewa,

"Karya yake! Wannan sharrin ne ake son ɗaura mana!"

Sai dai babu wanda ya saurare su.

Alhaji Uzairu ya yi shiru na ‘yan mintuna, yana kallonsu da idanunsa jajir, yana tunanin rayuwarsa, da irin zaluncin da aka yi masa. Duk tsawon shekarun da ya shafe yana zargin Zaytunah, da tunanin cewa ita ce mai laifi, ya fahimci cewa ya yi babban kuskure.

"Kuka raba ni da iyalina," ya faɗa cikin wata murya mai tsanani. "Kuka raba ni da ‘ya’yana. Kuka saka na rayu cikin ruɗu da baƙin ciki. Yau kuma kuna son ku kare kanku da ƙarya? Ai ba zan yafe ba! Kullum ina addu’a Allah ya tona asiri, kuma yau Allah ya tona!"

Ya juyo ya kalli Alhaji Amiru da Major General Dawud, waɗanda suka tsaya suna kallon abin da ke faruwa.

"Wallahi duk yanda kuka ga dama, ku yi da su. Ni na rabu da su har abada!"

Ya juyo ga matansa, ya ɗaga murya:

"Na sake ku uku, saki uku-uku! Ku fice daga gidana!"

A take suka zabura, suka zube a ƙasa suna kuka, amma babu wanda ke son jin uzurinsu.

Gwaggo Zainabu, wadda tun farko ke zaune shiru tana kallonsu da takaici, ta dafe kai tana jin kamar zuciyarta za ta fashe.

"Ku tafi ku bar mu da rayuwarmu lafiya," Alhaji Amiru ya faɗa, yana juyawa ba tare da ya sake kallon su ba.

Hajiya Rumanah ta dubi ɗanta Muhammad, tana neman taimako a idonsa, amma ya ɗauke kansa gefe. Bai san me zai yi ba. Ya girgiza kai kawai, yana jin kamar zuciyarsa ta fashe da takaici.

A haka aka kori su daga gidan zuwa court.. Rayuwarsu ta rushe a take. Asirinsu ya tonu, aure ya ƙare, ƙiyayya ta girma. A yau, duniya ta sauya musu fuska.

Muhammad ya yi tsaki alokacin daya karasa kallon faifon bidiyon wajen. Ya danna dakatawa. Yana cije lebensa hadi da busa numfashi mai dumi daga bakinsa. Ransa baki daya a dagule yake. Wannan abubuwa da mahaifiyar sa ta aikata don kwa itace shugabar komai baki daya ya hargitsa masa duk wani lissafin kansa.... Ita tayi abun amma baki daya shi yake jin kunya!!!

Ya cigaba da kalla yana jujjuya kai cike da tsantsar takaici marar misaltuwa....

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?
Chapter 49 · 0% Book details