Sashe 42
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Boka ya dubi kowa sannan ya saki ajiyar zuciya. “Ba laifina ba ne,” ya fara bayani. “Su Hajiya Rumanah ne suka zo wajena. Sun kawo min kudi masu yawa, sun ce ba sa son Zaytunah da ‘ya’yanta su dawo gidan Alhaji Uzairu. Sun ce idan na hana ta dawowa, za su kara min kudi.”
“Me ka yi musu?” Alhaji Uzairu ya tambaya, yana runtse idanu.
Bokan ya gyara zamansa, yana kallon su daya bayan daya. “Na yi wa Zaytunah tsibbu na mantuwa. Na sanya ta zama kamar mara tunani, ta manta duk abin da zai sa ta dawo gidan nan. Na yi mata kurciya, na hana ta nutsuwa. Idan har ta yi niyyar dawowa, to zuciyarta za ta kasa jurewa, ta shiga cikin wani yanayi na hauka ko tsananin tsoro.”
Ya kara da cewa, “Nabeeha da Hammad kuwa, na sanya musu masifar da za ta bi su har karshen rayuwarsu. Duk inda suka tafi, za su hadu da bala’i.”
Kowa ya yi shiru. An rasa abin cewa. Sai dai daga gefe, Gwaggo Zainabu ta fashe da kuka. “Wato haka suka yi wa zaytunah baiwar Allah! Sun so su hallakata da ‘ya’yanta!”
Alhaji Amiru ya kalli ‘yan sanda. “Ku tabbatar kun gurfanar da wannan boka da su Hajiya Rumanah a gaban hukuma. Dole a yi musu hukunci!”
Kafin a tafi da boka, sai ya daga kansa ya dubi Alhaji Uzairu. “Matar ka tana bukatar addu’a. Idan kana so ta dawo hayyacinta, sai ka nemi wanda ya fi ni karfi ya fitar da abin da na saka a jikinta.”
An yi shiru. Kowa ya cika da firgici. Wannan al’amari ya wuce tunanin kowa. Wannan shine karshen mugunta da zalunci. Daga wannan rana, dole a dauki mataki don kare Zaytunah da iyalanta daga makiyan su!..
A fadar Gwaggo Zainabu, shiru ya lullube dakin bayan boka ya fadi munanan ayyukan da ya aikata wa Zaytunah da 'ya'yanta. Kowa ya yi shiru, zuciya cike da fargaba da takaici. Sai dai Gwaggo Zainabu ce ta katse wannan shiru da wata zabura da ta yi, tana nunin boka da yatsa.
"Wato har haka kake da mugunta? Ka hada kai da matan nan don hallaka zaytunah da jikokina? To, wallahi ba za mu kyale ka ba!"
Jikin boka ya yi sanyi, ya sunkuyar da kai, yana girgiza kansa. "Ba laifina ba ne. Kudinsu ne ya rude ni."
Alhaji Uzairu ya nisa, ya dafe goshinsa. A yau ya fahimci cewa muguntar matansa ta kai matakin da ba zai iya jurewa ba. Sun so halakar da iyalinsa ne kawai don girman kai da hassada? Ya dago yana kallon Gwaggo Zainabu, idanunsa cike da nadama.
"Gwaggo, ni ma ba zan yafe musu ba. Sun fiye munafunci da zalunci!"
"Ba magana kawai za ka yi ba!" Gwaggo Zainabu ta fada da fushi. "Dole ne a dauki mataki! Wallahi yau sai an hukunta su!"
Alhaji Amiru ya kalli ‘yan sanda da ke tsaye kusa da boka, yana girgiza kai. “Ku tabbatar an kai wannan boka da su Hajiya Rumanah gaban hukuma. Dole a yi musu shari’a ta gaskiya.”
Nan take ‘yan sanda suka ja boka, suka fitar da shi daga dakin. Daga nan ne Gwaggo Zainabu ta dubi Alhaji Uzairu da idanu masu cike da tsantsar takaici.
"Yanzu ka tabbatar da maganganun su hajia Hafsatu ko? Bayan shekaru da yawa da Zaytunah ta sha wahala saboda matanka? Idan ba don Allah ya kubutar da ita ba, da yanzu ba ma san halin da take ciki ba."
Alhaji Uzairu ya girgiza kai, yana jin zafi a ransa. "Gaskiya kike faɗa, Gwaggo. Ban taba tunanin cewa mugunta ta kai haka ba. Amma yanzu, dole a nemo hanyar da za a wanke wannan asiri da aka yi mata."
Alhaji Amiru ya gyara zamansa, yana kallon Gwaggo Zainabu. "Ya kamata mu tuntubu masana, wato malaman fiqhu su duba lamarin. Idan ba a cire wannan tsibbu ba, to, Zaytunah ba za ta taba samun kwanciyar hankali ba."
...
A bangaren su Hajiya Rumanah, kukan da suka tsunduma yana karaji a cikin dakinsu. Sun ji labarin cewa boka ya shiga hannu, kuma ya bayyana duk abubuwan da suka faru. Hajiya Ladi ta zube a kasa, tana rike kanta.
"Mun shiga uku! Wannan boka wallahi zai jawo mana matsala."
Hajiya Karama ta rungume jikinta, tana karkarwa. "Kun san cewa idan aka dauki mataki, to ba za mu fita ba! A shirye kuke da ku shiga gidan yari?"
Hajiya Rumanah ta miƙe tsaye cikin hargowa. "Wallahi ba zan bari a kama ni haka nan ba! Ya kamata mu nemi mafita kafin su zo su kama mu."
Hajiya Ladi ta yi shiru na dan lokaci, sai kuma ta girgiza kai. "Babu wata mafita, Rumanah. Mun shiga tarkon da ba za mu iya fita ba. Idan kuwa aka kamamu, to fa ba za mu taba samun 'yanci ba."
A daidai wannan lokacin, sai ga wasu jami’an tsaro sun shigo gidan.
"Ku fito!" wani daga cikinsu ya daka musu tsawa. "Mun zo daukarku bisa umarnin kotu!"
Kamar an tsikare su, nan take suka rude. Hajiya Rumanah ta juya kamar za ta gudu, amma wani dan sanda ya rike hannunta.
"Ba gudu ba tsira! Kun gama aikata mugunta, yanzu lokaci ne na sakamako!"
Kafin su ankara, har an daure su da sarka, aka tafi da su.
..
A bangaren su Alhaji Amiru, an riga an fara kokarin nemo malamai domin cire asirin da aka yi wa Zaytunah. An kai ta wani wuri na musamman, inda wani malami mai ilimi ya fara addu’o’i domin wanke ta daga wannan kurciya da aka mata. Bayan an bata ruwan tofi na ayoyi da aka yu na ganyen magarta..
Sai dai abin mamaki, da zarar malamin ya fara karanta ayoyi masu karfi, sai Zaytunah ta fara karkarwa. Hawaye suka fara kwarara daga idanuwanta, tana jin wani irin nauyi yana sauka daga zuciyarta.
Wani daga cikin malamai ya kalli Alhaji Uzairu. "Gaskiya ne, an yi wa wannan mata asiri mai karfi. Amma in sha Allah, za mu cire shi."
A lokacin da aka ci gaba da addu’a, Zaytunah ta fara jin sauki. A hankali, tana bude idanuwanta, tana kallon mutanen da ke kewaye da ita.
"Na... na ji kamar wani abu ya sauka daga kaina," ta furta cikin raunanniyar murya.
Gwaggo Hafsat ta matso kusa, hawaye suna cika idanuwanta. "Alhamdulillah! Allah ya wanke ki daga muguntar su!"
A gefe guda, Nabeeha da Hammad suna kuka, suna kallon mahaifiyarsu da farin ciki. Sun san cewa daga wannan rana, rayuwarsu ba za ta sake kasancewa kamar da ba. Sun sha wahala mai yawa, amma yanzu sun samu haske.
Sai dai tambaya daya ta rage: shin Alhaji Uzairu zai iya gyara abin da ya faru? Ko kuwa kaddara za ta ci gaba da gwada su?
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE: 38_
Bayan doguwar addu’a da azancin malamai, a hankali Zaytunah ta soma dawowa cikin hayyacinta. Kamar wadda aka cire wa kaya masu nauyi, ta ji wani irin saukin da bata taba jin irinsa ba. Tana daga kwance, idanunta sun kada saboda dogon shan wahala, amma yanzu tana iya kallon mutanen da ke gefenta da cikakken tunani.
Gwaggo Hafsat ta kama hannunta cikin kulawa. “Zaytunah, ya kike ji yanzu?”
Zaytunah ta motsa bakinta cikin wahala. “Ina jin... sauki... amma zuciyata cike take da abubuwa da ba zan iya tuna komai ba sosai.”
Malamin da ya jagoranci addu’o’in ya yi murmushi. “Wannan al’amarin na tsibbu ba abu ne mai sauki ba. Amma da ikon Allah, kin samu ‘yanci daga wannan mugunta. Za ki fara tuna abubuwan da suka faru a hankali.”
A gefe, Nabeeha da Hammad sun rungume juna suna kuka. Ba wai kuka na bakin ciki ba, sai na farin ciki da fargabar irin halin da mahaifiyarsu ta tsinci kanta a ciki. Hammad ya matso kusa da ita, yana kallon fuskarta cikin tausayi.
“Ammi, kin san ni ne?”
Zaytunah ta dubi yaron nata, hawaye suka cika idonta. Ta daga hannunta tana shafa sumar kansa, kamar wadda ke jin labarinsa ne a karon farko. “Hammad…” Ta kalli Nabeeha wadda ke durkushe a kusa da ita, ita ma idonta cike da kwalla.
“Nabeeha…”
Nan take kuka ya kara karfi a dakin. Gwaggo Hafsat ta shafa kanta, tana murmushi mai cike da godiya. “Alhamdulillah! Wannan ne abu mafi muhimmanci.”
Alhaji Amiru ya kalli Alhaji Uzairu, wanda tun dazu ya kasa cewa uffan. Idanunsa sun cika da nadama, sai dai bai san ta ina zai fara fadin abin da ke zuciyarsa ba. Yana jin kamar ya zube ya roki gafarar Zaytunah, amma yana shakkar cewa za ta iya yafe masa.
Dakin ya dauki shiru na wasu sakanni, kafin a hankali Alhaji Uzairu ya karasa kusa da gadon da Zaytunah ke kwance. Ya durkusa a gabanta, yana fuskantar ta kai tsaye.