← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 75

Sashe 40

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Zaytunah, wannan ba lokaci ba ne na tsoro. Wannan lokaci ne na dinke barakar da aka jima ana fuskanta. Idan kika bari tsoro ya hana ki fuskantar su, hakan na iya jawo bakin ciki har karshen rayuwarki

Hajiya Zaytunah ta sauke ajiyar zuciya, tana wasa da yatsun hannunta. A hankali ta dago kai ta dubi Gwaggo Hafsatu, idanunta cike da ruɓaɓɓen tunani.

"Gwaggo, me zai faru idan ba su fahimce ni ba? Me zai faru idan suka yanke hukunci cewa ni ce na watsar da su?"

Gwaggo Hafsatu ta murmusa, tana shafa hannunta cikin kwantar da hankali. "Zaytunah, su Alhaji Uzairu da sauran su ba yara ba ne. Sun yi shekaru suna neman ki, da basa kaunar sake sanya ki a idanuwan su ai duk tarin shekarun nan da ba zasu dinga neman ki ba.., suna neman hakikanin abin da ya faru. Wannan shi ne lokacin da za su ji gaskiya daga bakin ki. Babu wanda zai zarge ki idan suka fahimci matsalar da kika shiga."

Hajiya Zaytunah ta jinjina kai a hankali, tana jin wani sanyi a zuciyarta. Duk da haka, fargaba ba ta gushe ba.

A wancan lokacin, a gefen Alhaji Uzairu, zuciyarsa tana tafasa. Tun bayan da suka bar falon Major General Dawud jiya, ya kasa samun natsuwa. Tunani ya hana shi barci. Shin zai sake ganin Zaytunah? Shin zata gane shi? Shin zata yarda ta dawo da komai kamar da?

"Uzairu," murya ta katse masa tunani. Alhaji Amiru ne ke magana, yana dubansa da kulawa. "Kana da yakinin cewa kana shirye ka fuskance ta?"

Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin zuciyarsa na harbawa. "Ya Amiru, ba wai tambayar ko na shirya ba ce. Tambayar ita ce—shin zata yarda da ni? Shin zata fahimce ni?"

Alhaji Amiru ya dan murmusa, yana dafa kafadar shi. "Zaytunah ba matar da zata manta da kai haka kawai ba. Idan da hakan ne, da tuni ba ta damu da ciwon da take fama da shi ba. Ka yi hakuri, ka bari lokaci ya yi aiki."

A can gefe, Major General Dawud ya fito daga sashensa yana kallon su duka. A yau ne suka shirya haduwar da suka jima suna jira. Ya kalli Gwaggo Hafsatu, wadda ta jinjina kai, tana nufar su Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru.

"Lokaci ya yi." Ta fada a hankali.

Alhaji Uzairu ya mike, ya gyara rigarsa. Zuciyarsa na bugawa da sauri. Wannan haduwar ba zai taba mantawa da ita ba.

Duk da sanyin gari, idanun Alhaji Uzairu sun cika da zufa. Yayi nisa a tunani har sai da suka iso bakin kofar dakin da Hajiya Zaytunah take.

Gwaggo Hafsatu ta ja numfashi sannan ta tura kofar a hankali.

Cikin nutsuwa, Hajiya Zaytunah ta dago daga inda take zaune, idanunta cike da tsoro da fargaba. Kamar dai yadda take a daren jiya, zuciyarta ta kasa natsuwa.

A hankali, Alhaji Uzairu ya taka zuwa ciki, yana kallonta da ido. Tsawon shekaru bai ganta ba, amma yau, gashi a gabansa.

"Zaytunah..." Muryarsa ta fito cikin karyewa.

Hajiya Zaytunah ta sake kakkarwa, zuciyarta na bugawa. Ta dauke kanta gefe, tana jin yadda numfashinta ke rikicewa.

Alhaji Uzairu ya matsa kusa, amma ba tare da matsawa fiye da kima ba. Ya lura da yadda take a tsorace, hakan yasa ya daidaita kansa.

"Zaytunah, ni ne. Uzairu. Ki kalleni."

Idanunta sun cika da kwalla, amma ta kasa dago su. Babu abin da take ji sai bugun zuciyarta da wani irin sanyi a gabanta.

"Ban taɓa mantawa da ke ba." Ya fada a hankali, hawaye suna taruwa a idonsa. "Ban san me ya faru da ke ba. Ban san inda kika shiga ba. Amma ban taɓa dena tunaninki ba."

Hawayenta sun gangaro, amma har yanzu bata iya motsi ba.

"Idan har da gaske kika manta da ni, idan har da gaske kika manta da rayuwarmu..." Ya runtse ido, yana jin yadda zuciyarsa ke suya. "To zan tafi. Amma da fatan za ki gaya min gaskiya, menene ya faru?"

A wannan lokacin ne zuciyar Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa. Kamar wacce ta sha ruwa mai sanyi, ta fashe da kuka.

"Uzairu..." Muryarta na rawa. "Ban guje ku ba. Ban manta da kai ba. Ban manta da komai ba."

Alhaji Uzairu ya kafe ta da ido, zuciyarsa na suya da karaya. "To me ya faru? Menene ya hana ki dawowa?"

Hajiya Zaytunah ta runtse ido, tana jin yadda hawayenta ke bin fuskarta. Cikin wani irin shesshekar kuka, ta furta kalmomin da suka kasa fita tsawon shekaru.

"Asiri aka min, Uzairu. An rabani da ku da sihiri da tsibbu. An tursasa min tafiya, aka hana ni dawowa. Ban yi hakan da kaina ba!"

A take zuciyar Alhaji Uzairu ta buga, ya dafe kirjinsa kamar wanda aka caka wa mashi. Idanunsa suka firfito da mamaki.

"Asiri?" Ya tambaya cikin rawar murya.

Hajiya Zaytunah ta gyada kai, tana jin yadda zuciyarta ke kunshe da zafi. "Kurciya aka yi min, Uzairu. An kulle ni cikin wani hali da bai barni na koma gare ku ba. An sace rayuwata."

Shiru ya ratsa dakin. Alhaji Uzairu ya dafa goshinsa, yana jin yadda nauyin abu ya hau kansa. Idan har wannan gaskiya ne, to hakan na nufin shekaru da dama na rashin sanin hakikanin abin da ya faru.

Bai san lokacin da hawaye suka gangaro daga idonsa ba. Bai san lokacin da zuciyarsa ta fashe da raɗaɗi ba.

A hankali, ya matsa kusa da ita. Babu kalma da zai iya furtawa, sai ya tsugunna gabanta, yana kallonta da ido.

"Zaytunah..." Ya kira sunanta cikin rawar murya.

A hankali, ta dago ta kalle shi. Idanun su cike da hawaye.

"Kin dawo gare ni?"

A wannan lokacin ne zuciyarta ta fashe, ta sunkuya, ta boye fuskarta cikin tafukan hannunta, tana kuka mai karfi.

A wannan lokacin ne Alhaji Uzairu ya fahimta duk tsawon shekarun da suka shude, duk radadin da suka sha, wataƙila wannan ce ranar da za a fara farfaɗowa daga ciki.

Ranar da komai zai fara gyaruwa...

MX🧕

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:36_

Hawaye suka ci gaba da sintiri a fuskar Hajiya Zaytunah. Hannunta yana rawa, zuciyarta na bugawa da karfi. Ta kasa motsawa, ta kasa yarda da cewa yau, gashi da gaske Alhaji Uzairu na a gabanta.

"Yaya uzairu..." Ta sake furta sunansa cikin raunaniyar murya, kamar mai neman tabbaci.

Alhaji Uzairu ya gyada kai, yana kallonta da ido mai cike da tausayi. "Eh, ni ne, Zaytunah. Na zo, na zo gare ki. Amma kina nufin shekaru duka wadannan ba ki san yadda za ki dawo ba? Ko da sandar sako?"

Hajiya Zaytunah ta runtse ido, wani sabon hawaye na gangarowa.

"Ba ku fahimta ba, Uzairu. Ba wai kawai an rabani da ku ba ne. An tsare ni a wani hali na kurciya da ba zan iya bayyana ba. Wataƙila har yanzu ba ku san cewa har cikin barcin ku an danƙa min tsinuwa da tunzuri akan kin waiwayar gidah ba"

Alhaji Uzairu ya dafe goshinsa, zuciyarsa na kuna. Wani irin tausayin Zaytunah ya lulluɓe shi, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi. Duk da shekara da shekaru da suka shude, ba zai iya musanta cewa wannan matar da ke gabansa ita ce zuciyarsa, soyayyarsa, iyalinsa da ya dade yana nema.

A hankali ya kalli cikin idanunta da suka cika da hawaye.

"Zaytunah..." Ya kira sunanta da wani irin sanyin murya, yana jin yanda kalmomin suka makale masa a makoshi. "Kina nufin duk wannan lokaci kina raye da kike fama da wannan hali?"

Zaytunah ta lumshe ido, tana jin zuciyarta na rawa. "Uzairu, ba abu ne mai sauƙi ba. Wallahi ba zan iya bayyana azabar da na sha ba. A kowace rana ina jin kaina a cikin duhu. Akwai lokutan da nake jin kamar na salwanta, kamar rayuwata ta kare."

Ta runtse ido, hawaye suna sintiri a kumatunta.

"Ban san yadda zan iya komawa gare ku ba. Ko da na so, ba zan iya ba. Duk hanyoyin da zan bi an toshe min su."

A can gefe, Gwaggo Hafsatu ta dafa hannun Zaytunah, tana girgiza kai.

"Ai mun san hakan, Zaytunah. Mun san cewa ba da kanki kika bar su ba. Muna tare da ke, mun sha wahala wurin fahimtar abin da ya faru."

Alhaji Amiru ya dubi Major General Dawud, yana dan gyara zamansa. "Wannan abu da aka yi mata ba ƙaramin zalunci ba ne. Na sha bincike a baya, amma ban taɓa tunanin cewa har tsibbu da asiri ne aka yi mata ba."

Gwaggo Zainabu, wadda tun farkon maganar take kallonsu da damuwa, ta numfasa. "Wai shin waye ya yi wannan asirin? Su waye suka shirya wannan makircin?"

Shiru ya ratsa falon. Kowa ya juya yana kallon Zaytunah, amma sai ta kauda kai gefe. Akwai abubuwan da ba za ta iya faɗa yanzu ba.

Major General Dawud ne ya dubeta da kulawa. "Zaytunah, babu abinda zai faru idan kika faɗa gaskiya. Wannan lokaci ne na yanke hukunci akan abin da ya faru da ke. Idan har akwai wanda yake da alhakin hakan, to dole ne mu san shi."

Zaytunah ta dan lumshe ido, ta sake jan numfashi. Sannan cikin wata irin murya mai rauni, ta furta: "Kishiyoyi hadi da wasu daga cikin yan uwana na ne suka yi min wannan asirin. Sun haɗa kai da wasu bokaye suka kulle ni da tsibbu da kurciya, suka hana ni komawa gidana... ."

Wata irin faduwar gaba ta kama Alhaji Uzairu. Ya kafe ta da ido, yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi. "Wannan gaskiya ne, Zaytunah?"

Ta gyada kai, hawaye suna cika mata ido.

"Yaya Uzairu, wallahi gaskiya nake faɗa. Su ne suka yi min haka. Su suka raba ni da kai, suka sa na bar gidan da Muhammad wanda yake Hammad a yanzu da mai sunan Gwaggo da muke kira da Nabeeha a yanzu."

Alhaji Uzairu ya rintse ido, yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. Bai taba tunanin cewa matan sa za su iya aikata hakan ba. Bai taba zaton cewa makircinsu zai kai haka ba.

"Allah ya isa!" Ya furta cikin zafin rai.
Chapter 40 · 0% Book details