Sashe 21
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu dai, ko menene zai biyo baya, sun kusa isa gida........
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE: 17_
MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RESIDENCE:
Tunda motocin suka ratsa kofar shigowa gidan, farin ciki ya bayyana a fuskar kowa. Wutar fitilu masu launi na musamman sun haska ko'ina, suna bai wa ginin kamannin gata da martaba. Dawakan tsaro suna ta kai-komo, kowannensu cikin shirin ko-ta-kwana, amma a wannan rana komai ya sauya, dukansu suna murmushi, wani ma har yana daga hannu yana gaisawa da su.
A lokacin da motocin suka tsaya, kafin ma kowa ya fito, Gwaggo Hafsatu ta riga ta fito da sauri daga cikin gida, ba tare da la’akari da shekarunta ko nauyin da ke kanta ba. Har lokacin da suke bude kofar mota, ta riga ta tarbe su da hawaye a idanuwanta, na farin ciki da godiya ga Ubangiji... Ta durkusa tana yin sujjadar godiya ga Allah madaukakin sarki da ya kubutar dasu hajiya Zaytunah..
Da kyar ta iya jira har suka fito daga cikin motar. Da zarar Hajia Zaytunah ta fito, sai Gwaggo Hafsatu ta rungume ta da karfi, kamar ba za ta sake ta ba. Ta dinga shafa kanta tana duban fuskarta cike da tausayawa da kaunar da ke cikin zuciyarta.
"Ina godiya ga Allah! Allah mai iko ne, Allah mai taimako ne!" Ta fada tana sharar hawaye, hannuwanta biyu na rike da hannun Hajia Zaytunah.
Idanunta sun cika da soyayya lokacin da ta juyo ta rungume Nabeeha da Hammad.
"Ya Allah, Alhamdulillah! Kun dawo lafiya, ko? Babu ciwo? Babu komai, ko?"
"Eh, Gwaggo, mun dawo lafiya," Nabeeha ta fada a hankali, muryarta cike da kauna.
"Allah mai iko! Allah mai cikakken iko!" Gwaggo Hafsatu ta sake nanatawa, tana jin kamar zuciyarta za ta fashe da farin ciki.
Daga gefe, Fawaaz ya tsaya cikin nutsuwarsa, kamar kullum, yana kallonsu da ido mai cike da kulawa. Duk da rashin sakewarsa, akwai wani yanayi na kwanciyar hankali a tattare da shi. Bai yi wani yunƙurin shiga cikin tarbar ba, amma idanunsa sun bayyanar da yadda zuciyarsa ke farin ciki da ganin sun dawo lafiya.
Gwaggo Hafsatu ta juyo da murmushi tana kallonsa.
"Fawaaz, Na gode maka sosai. Na gode da komai, da kulawa, da fahimta, da jarumtarka."
Maimakon ya amsa da kalmomi, sai ya kada kai yana mai nuna cewa babu komai. Sai dai idanunsa sun furta abin da bakinsa ya kasa fadi.
Gaba daya gidan ya kaure da murna. 'Yan gidan, masu aiki, hatta ma'aikatan tsaro sun yi tattaki zuwa bakin babban falon don nuna farin cikinsu. Ga kamshin abinci daga cikin gidan, alamar an dafa girki na musamman don tarbar su.
A falon, kowa ya zauna cike da nishadi. Hammad ya dinga yawo da fara’a yana gaisawa da kowa, shi kadai yana cikin karamin nishadi. Nabeeha kuwa ta zauna kusa da mahaifiyarta, tana dubanta da kulawa.
Gwaggo Hafsatu tana ta duban Hajia Zaytunah da kulawa.
"Ya jikinki? Yana ciwo? Me kike bukata?"
Zaytunah ta yi murmushi mai rauni.
"Alhamdulillah, Gwaggo. Sai dai radadi kadan ne."
"Allah ya sawwake, kin ji?" Gwaggo Hafsatu ta fada tana shafa bayanta da kuncinta.
Cikin shafar bayan zaytunah sai ga dan kwali ya fadi cike da tsananin tashin hankali gwaggo Hafsatu ta hango keyar da aka saisaye da gashi.. hawaye suka cika idanunta.
Gwaggo Hafsatu ta dago tana duban Fawaaz.
"Subhan'Allah... Dawuda, Kaga Zaytunah an aske gashin ta. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Waɗannan mutane da sukai wannan abu Ubangiji Allah ya saka muku Allah ya bi muku hakkin ku.. Gwara mu tashi mu tafi asibiti kafin gabatar da komai...Har a tabbatar da lafiyar su. Ina so mu rankaya asibiti, ko da babu wata matsala, A dai tabbatar."
Fawaaz ya kada kai yana amincewa. "Tohm gwaggo . Hakan yayi" ya fada a takaice.
"Subhan'Allah. Ai a hakan ma gwaggo an auna arziki. Ubangiji Allah yasa karshen wahalar kenan ... Bayaga haka babu wani abun na daban ko?" Cewar major general dawud. Yana duban hajia zaytunah.
Hajiya Zaytunah tayi hanzarin girgiza kanta da sauri ta Kuma ce,
"Babu wani abu na daga labari marar dadi. Sai dai duka da sukayi mana sun azabtar da mu sosai.. Duk kuwa da umarni ne daga wadanda suka turo su acewar su. Don dayan umarnin nema Allah ya tsare bai faru ba. Kusan akansa nema wasu daga cikin yan fashin suka bijere maganar shugaban su. Suka ketare suka kubutar da mu"
"Subhan'Allah Subhan'Allah..ai idan Allah yarda duk masu hannu acikin wannan abu zamu kamasu red handed. Shin wani abu ne wannan da basu kaiga aikatawa ba Allah ya takaita ku ka kubata?"
Hajia Zaytunah ta dubi major general dawud tana tunanin yadda zata fada. Don maganar batasan fadar tama saboda tsananin muninta,
Falo ya ɗauki shiru bayan da Major General Dawud ya yi tambaya mai nauyi,
"Zaytunah, me ya faru da ku?"
Gwaggo Hafsatu ta gyara zama a kujerarta, zuciyarta tana tafasa da fargaba. Nabeeha da Hammad kuwa sun natsu a gefen mahaifiyarsu, suna jiran jin yadda zata bayyana abin da suka fuskanta. Fawaaz yana gefe, yana kallon fuskar Hajia Zaytunah da idanun da ke cike da zurfin nazari.
A farkon fara magana, Hajia Zaytunah ta runtse idonta na dan lokaci, kamar wadda take kokarin tattara karfin gwiwa. Zuciyarta tana bugawa da karfi, wani irin tsoro da ba ta san yana ciki ba yana neman turnuke ta.
Sai ta bude idanu, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta soma magana da muryar da ke sanyi, amma mai nauyi.
"Sun kama mu... sun yi mana azaba fiye da tunanin dan adam," ta fara, tana jin yadda muryarta ke rawar jiki.
"Sun daure hannuwanmu da kafafuwan mu da igiya mai karfi... kamar wata dabba da ba ta da iko da jikinta. Sun toshe mana baki da zani don kada mu iya kiran wani."
Duk wanda ke cikin falon ya zura mata idanu, babu wanda ya motsa.
Ta ɗauki wani numfashi mai nauyi, hawaye na taruwa a idonta. "Sun... sun aske min gashi. Ba don......"
Sai Kuma tayi shiruh ta kalli Gwaggo Hafsatu da Major General Dawud, idanunta cike da hawaye. Kamar tana sake jin raɗaɗin abin da suka fuskanta a hannun miyagun mutanen da suka kama su. Ta ɗan tsaya na wani lokaci, kamar mai tattara ƙarfin gwiwa, sannan ta ci gaba da magana.
"Sun kama mu a dare, babu wanda ya san inda aka kai mu. Sun daure hannuwan mu da kafafuwan mu da igiya mai ƙarfi, kamar wasu dabbobi da ba su da iko da jikin su. Sun toshe mana baki da zani don kada mu iya kiran wani. Munyi ƙoƙarin tserewa, amma igiyar da suka ɗaure mu da ita tana matse ƙasusuwanmu har ba ma iya motsawa.
"A lokacin da suka kawo Nabeeha da Hammad a gabana, zuciyata ta karye. Na ga yadda suka dinga dukansu. Hammad yana ihu yana kiran sunana, yana kuka, amma babu wanda ya ji shi. Idanunsa sun kumbura saboda dukan da suka masa. Nabeeha kuwa, ba zan taɓa mantawa da yadda wani daga cikin su ba ya taka ruwan cikinta..Sun yi ƙoƙarin raba ta da mutuncinta! Amma Allah bai nufa hakan ya faru ba!
Ta runtse idanu, hawayenta na sauka
"Nabeeha ta yi ta kokawa da karfinta, tana kuka tana ihu. A karshe, daya daga cikinsu ya daga hannu zai mare ta, amma wani daga cikinsu ya hana shi. Har yanzu, ban san dalilin da yasa ya hana ba, amma yana daya daga cikin dalilan da yasa bata fuskanci mafi munin abin da suka nufa ba."
Fawaaz ya matse hannayensa, jijiyoyin wuyansa sun fito. Idanunsa sun kada da tsananin fushi, amma bai ce uffan ba. Kawai yana saurara, zuciyarsa na tafasa.
Hajia Zaytunah ta ci gaba,
"Sun ci mutuncinmu da kalmomi, sun dinga zaginmu suna dariya. Sun ce babu mai kubutar pda mu, sun ce za su kashe mu a ranar da suke so. Amma Allah ya kawo mana agaji a hannun wasu da ba mu yi tsammani ba, wasu daga cikin su, wato su Gora da Bala."
Tana ambaton sunayen, sai Gwaggo Hafsatu ta ɗago kai da sauri. "Gora da Bala?"
"Eh, su ne suka taimaka mana. Duk da cewa suna cikin 'yan ta'adda, amma sun nuna jinƙai. Sun nemo mana abinci da ruwa. Suna boye mu daga sauran miyagun. A ƙarshe, su ne suka sassauta igiyoyin da suka ɗaure mu da su, har suka samar mana hanya muka tsere daga hannunsu."
Tana gama faɗin haka, sai ta sunkuyar da kai, tana jin kamar duk tsawon lokacin da suka shafe a hannun miyagun ya dawo da ita cikin wannan dakin.
Shiru ya biyo baya, amma shiru mai cike da nauyi. Kowa yana jin girman azabar da suka sha.
Fawaaz ne ya fara magana, cikin muryar da ke cike da ƙarar zuciya.
"Wadanda suka aikata wannan azaba ba za su tsira ba."
Major General Dawud bai ce komai ba, amma idanunsa sun nuna alamar hukunci. Ba zai bari su tsira ba.
Gwaggo Hafsatu kuwa ta rungume Hajia Zaytunah cikin kulawa da ƙauna.
"Alhamdullillah, Kun tsira da ran ku, Sannan baa yi Wa nabeeha wannan danyen aiki ba. kuma wannan shine abu mafi muhimmanci."
Haka dai suka cigaba da tattaunawa. Kafin daga bisani sukayiyyi wanka bayan sunci abinci suka dauro tsarki. Suka rama sallolin da basuyi ba .. sannan suka rankaya zuwa asibiti kamar yadda gwaggo tabada shawara.
A cikin motocin soja da ke rakiyarsu, suka isa asibitin cikin girmamawa. Likitoci da nas-nas sun riga sun shirya don karbar su, saboda Fawaaz da Major General Dawud sun tabbatar an sanar da su kafin isowarsu.