Sashe 36
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana tsaye a tsakiyar dakin, yana kallonta da idanuwansa masu nuna tsananin takaici. Hajiya Hawwa Maijiddah ta sunkuyar da kai, tana kokarin kauce wa kallonsa. Duk da cewa a zuciyarta ta san cewa bata da wata hujja mai kwari da zata iya kare kanta da ita, har yanzu tana kokarin boye gaskiyar lamarin.
"Hawwa," ya kira sunanta da murya mai cike da natsuwa, amma hakan bai sa zuciyarta ta daina bugawa da karfi ba.
"Daga ina kika samu wannan bayanin? Waye yake ba ki shi? Waye kike tura wa wannan sakon?"
Ta dinga hadiye yawu, tana jin tsoron bayyana gaskiya. Idan har ta fada masa komai, tabbas hakan zai kara dagula al’amura.
"Dawud, wallahi ba wani abu bane… Ni dai kawai… kawai ina son sanin abubuwan da ke faruwa ne. Na tsinci labari ne daga inda ba zan iya bayyanawa ba."
Ya saki murmushin takaici, yana jin yadda zuciyarsa ke kara tafasa.
"Kin san mene?" Ya kalle ta kai tsaye. "Bani da bukatar jin wani karin bayani daga gare ki, domin abinda nake gani ya ishe ni."
Ya juya, ya dauki wayarta yana sake duba sakonnin da ta tura. Yayi mamakin yadda ta samu cikakken bayani game da shirin komawar Zaytunah da ‘ya’yanta. Wannan ya tabbatar masa da cewa dibar rahotan komai take tana barbadawa..
"Hawwa, ni da ke muka zauna a wannan gidan tsawon shekaru, amma ban taba tunanin cewa wata rana za ki iya cin amanata haka ba."
Hajiya Hawwa Maijiddah ta dago kanta a hankali, idanunta cike da hawaye. "Wallahi ba hakan bane, Dawud… Ni dai kawai—"
"Ya isa!" Ya katseta da muryar da ta firgita ta. "Na ce ki bani amsa, ba na son jin wata ‘yar magana maras amfani."
Ta yi shiru. Idanunta sun kada da tashin hankali, amma ta kasa furta komai.
Major General Dawud ya runtse idonsa na wani lokaci, yana kokarin kwantar da fushinsa. Amma hakan ba abu ne mai sauki ba. A zuciyarsa, ya fara tunanin duk wata hanya da zata iya fallasa bayanan SIRRIN da suka dade suna kokarin rufewa.
Idan Hajiya Hawwa Maijiddah ta iya sanin wannan labari, hakan na nufin cewa akwai wanda ke ba ta bayanai a cikin gidan. Ko kuma ta samo su daga wajen wani da ke da masaniya game da lamarin.
Ya dauki wayarta, yana kokarin ganin idan zai iya gano wanda take turawa sakonni. Amma abin mamaki, lambar da ta aika wa sakonnin ba ta da suna. Wata lamba ce da ba a rubuta mata suna ba, wata sabuwa ko wata da aka boye.
Wannan ya kara tabbatar masa da cewa akwai wani abu mai girman gaske da ke faruwa.
A take ya juya, ya dubi Hajiya Hawwa Maijiddah da idanuwansa masu nuna bacin rai.
"Na dauki alkawari, babu wanda zai taba Zaytunah da ‘ya’yanta ba tare da sunan Allah ya tabbata akai ba. Idan har kina da hannu a cikin wani shiri na cutar da su, to ki sani, ba zan taba lamunta ba."
Ya wuce zuwa kofar fita, amma kafin ya fita, ya tsaya ya sake dubanta.
"Ki tanadi amsa, domin zan dawo."
Ya fice daga dakin, zuciyarsa na cike da tunani. Wannan batu ba zai tsaya nan ba. Dole sai ya gano wanda ke bayan wannan al’amari—da kuma abinda ya kawo hakan.
Major General Dawud yana fita daga dakin, zuciyarsa cike da tunani. Bai yi kokarin rufe kofa da karfi ba, amma Hajiya Hawwa Maijiddah ta san cewa hakan ya fi komai nuna tsananin fushinsa. A karo na farko cikin shekaru da suka yi tare, ta fahimci cewa tana gab da rasa amanarsa gaba daya.
Ya nufi dakin sa na aiki, inda ya zauna a kan kujerarsa yana sake nazarin sakonnin da ya gani. Bai so ya dauki hukunci cikin fushi, amma dole ne ya san gaskiyar al’amari kafin lamarin ya fi kamari.
Ya sake duba lambobin da Hajiya Hawwa Maijiddah ta tura wa saƙonni. Lambar da ba ta da suna ta fi daukar hankalinsa. A matsayinsa na soja mai kwarewa da bincike, ba zai bar wannan lamari haka nan ba.
Major General Dawud ya dan jinkirta kafin ya kira Captain deen, domin ya san cewa idan ya dauki wannan mataki, komai zai sauya. Wannan ba matsala ce ta iyali kawai ba, matsala ce ta tsaro—wacce dole sai an dauki matakin gaggawa.
Ya latsa kiran, yana sauraron karar ringi. A lokaci guda, yana ta faman dannawa cikin wayarsa domin gano wata hanya da zai iya bin diddigin lambar da Hajiya Hawwa Maijiddah ta tura wa sakonnin sirri.
"Sir!" Muryar Captain Deen ta karade kunnensa, cike da girmamawa.
"Deen, ina bukatar bincike cikin gaggawa. Akwai lambar waya da zan tura maka yanzu—dole ne ka gano wa take da ita da kuma inda take aiki. Hakanan, ina bukatar ka bincika ko akwai wani shiri da ake kullawa da SIRRIN gidan nan."
"An gama, Sir!" Deen ya amsa ba tare da bata lokaci ba. "Zan tura bayanai cikin kankanin lokaci."
Major General Dawud ya katse kiran, sannan ya aika da lambar wayar. Yana gama hakan, sai ya lumshe idanuwansa, yana kokarin nazarin duk abin da ke faruwa.
Ya san cewa Hajiya Hawwa Maijiddah ba ita kadai ce ke da masaniyar SIRRIN Zaytunah da ‘ya’yanta ba. Idan har ta samu bayanai da yawa haka, hakan na nufin akwai wanda ke mata bayanai daga cikin gidan ko kuma daga wajen sa. Wannan ya kara masa damuwa.
Bai dauki lokaci mai tsawo ba, Captain Deen ya sake kiran sa.
"Sir, mun fara samun bayani akan lambar da aka tura sakonnin nan."
"Muna sauraron ka."
"Lambar tana da alaka da wata mace da ake kira Hajiya Rumanah. Matar da ke da dangantaka da wasu mutane masu tasiri a birnin mawii da Fubu. Tana kasuwanci, amma kuma ana kyautata zaton tana da alaka da wasu mutane da ke tattara bayanai na SIRRI."
Major General Dawud ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ta kara tafasa.
"Kana nufin akwai yiwuwar Hajiya Rumanah na tattara bayanai akan Zaytunah da iyalanta?"
"Hakan yayi kama da gaskiya, Sir. Kuma abu mafi hadari shine, tana da alaka da wata mata, Hajiya Zaytunah... Gwaggo Zainabu... "
Dawud ya dan runtse ido. Wannan batu yana kara rikicewa. Gwaggo Zainabu? Me take da niyyar yi da Zaytunah? Kuma me yasa Hajiya Hawwa Maijiddah ke kokarin tona SIRRIN gidan?
Dole ne a dauki mataki cikin gaggawa.
"Deen, ina bukatar ka ci gaba da bincike cikin nutsuwa. Kada a bari wani ya gane muna kokarin gano gaskiya."
"An gama, Sir!"
Bayan kiran ya kare, Major General Dawud ya dauki lokaci yana nazari. Yanzu ya tabbatar da cewa Hajiya Hawwa Maijiddah na da alaka da Hajiya Rumanah, kuma hakan na iya nufin cewa tana da wani shiri da bata bayyana masa ba.
Ya mike tsaye a hankali, yana tafiya zuwa dakin da ya bar Hajiya Hawwa Maijiddah. Lokacin da ya isa, ya tarar da ita zaune akan gado, amma a bayyane take cewa hankalinta a tashe yake.
Ba tare da bata lokaci ba, ya zauna a gefen kujerar dake kusa da ita, yana kallonta kai tsaye.
"Ki gaya min gaskiya, Hawwa. Me kike nema?"
Tayi shiru. Ta ji nauyin furta komai, domin ta san cewa duk abin da zata fada, zai iya kara tsananta lamarin.
"Me yasa kike tura bayanai akan Zaytunah da iyalanta? Wace alaka kike da Hajiya Rumanah?"
A wannan lokacin, jikinta ya fara rawa. Idanunta suka kada, sai ta dan ja numfashi kafin tace:
"Dawud, ni ba nufina na cutar da kai bane. Ni dai kawai ina kokarin kare martabarka ne."
"Kare martabata?" Ya maimaita, yana kallonta da mamaki. "Ta yaya yin cin amana zai kare martabata?"
Hajiya Hawwa Maijiddah ta sunkuyar da kanta. "Ina jin tsoro. Ina tsoron cewa wata rana, Zaytunah da ‘ya’yanta za su kwace maka hankalinka har ka manta da ni da ‘ya’yanmu."
A wannan lokacin, Dawud ya yi shiru. Wani irin takaici da ba zai iya misaltawa ba ya lullube shi. Ashe saboda kishin duniya ne yasa Hajiya Hawwa Maijiddah ke aikata haka? Tamkar ya sharara mata uban Mari ya lakada mata duka yakeji. Cike da takaici yache,
"Ke kin san cewa tun farko ba ke kika kawo Zaytunah gidan nan ba. Kin san cewa mahaifiyata ce ta bukaci hakan. Ni na tsaya domin ganin cewa babu wanda zai cutar da ita, saboda sanin cewa ba laifinta bane aka jefa ta cikin wannan hali."
Ya girgiza kai. "Kuma ki sani, idan har ina da amana, babu wanda zai iya kwace martabarki a idona sai dai ke da kanki."
Hajiya Hawwa Maijiddah ta dan rusuna, zuciyarta na tafasa da tunani.
"Kiyi kokarin tunani, Hawwa. Idan har kika ci gaba da wannan makircin, ba ke kadai zai shafa ba. Idan aka gano cewa ke kika tona SIRRIN gidan nan, kin san me hakan ke nufi?"
Ta runtse ido, tana jin yadda maganganunsa ke sauka akanta kamar toka mai zafi.
"Da na fi so ki zo ki gaya min matsalarki, ba ki shiga wannan lamarin ba. Amma yanzu dole ne a dauki mataki. Kuma dole ne ki daina duk wani alaka da Hajiya Rumanah.
Bayan barin dakin, Major General Dawud ya nufi ofishinsa. Ya kira Captain Deen a waya. Domin ya kyale hajia hauwa Maijidda ne batare da ya sake mata wata barazanar ba so yake ya gama gano dukkanin kullalliyar da suke shiryawa itada mutanenta na cikin waya...
"Deen, akwai bukatar a ci gaba da sanya ido akan Hajiya Rumanah. Kuma ina so a san takamaiman abin da take nema da wannan bayanan."
"An gama, Sir!"
Yana katse kiran, ya mike tsaye yana nazari. Wani sabon shiri zai dauka. Domin yanzu ya fahimci cewa akwai wata babbar makarkashiya da ake kokarin kullawa a kan Zaytunah da iyalanta. Kuma ba zai bari hakan ya faru ba.
Ba tare da bata lokaci ba, ya fara tsara matakin gaba—wanda zai tabbatar da cewa ba wanda zai iya cutar da Zaytunah da ‘ya’yanta, ko da kuwa hakan na nufin yin abin da bai taba yi ba a rayuwarsa.
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)