← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 75

Sashe 14

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Zaytunah ta matse hannun Nabeeha, sannan ta dube su Bala da Gora.

"Babu komai, Allah yana tare da mu. Yadda ya kubutar da mu daga sansanin yan fashi. Da yardar Allah zai karasa warware duk wani tuggu da makirci, sharri da ma sihiri da ake aikatawa da yardar Allah. Komai nisan dare gari zai waye..Allah zai bayyana gaskiya.. Kuma shi sharri dan aike ne..idan ka turashi karka rufe kofa zai dawo maka..."

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE: 12_

Suna isa wani wuri da ke da nisa da inda aka tsare su, inda Bala da Gora suka tanadi wani tsohon gida mai matukar kango. A nan suka tsaya domin su huta, kuma su tattauna gaba ɗaya a kan matakin da ya kamata su ɗauka.

Hajiya Zaytunah ta kalli su Bala da Gora, zuciyarta na tafasa da mamaki da kuma fushi. Duk da cewa sun kubuta daga sansanin yan fashin suna dai cikin dajin. har yanzu ba ta iya fahimtar dalilin da yasa Hajiya Rumanah za ta nemi hallakata ba...

“Bala, me yasa? Me nayi mata da har ta tsaneni haka ita wadda ta turo ku?”

Bala ya yi shiru na ɗan lokaci, yana nazarin yadda zai bayyana gaskiyar. Gora ya jefa masa harara, yana son ya yi magana kawai. A karshe, Bala ya numfasa sannan ya ce,

“Akwai wata magana da na ji daga bakin shugabanmu kafin a kawo ku. Yana cewa Hajiya Rumanah tana tsoron cewa idan kika ci gaba da rayuwa, to akwai wani babbar SIRRI da zai tonu.”

Hajiya Zaytunah ta runtse ido, zuciyarta na kara harbawa da sauri. SIRRI i? Wane irin SIRRI ne hakan?

Nabeeha, wadda ke zaune a kusa da ita, ta dafa hannunta.

“Ammi, ko da wasa ban taba tunanin cewa yar uwarki ta jini za ta iya yin haka ba... shine dalilin daya sa bamu san su ba kenan? ”

Hajiya Zaytunah ta girgiza kai.

“Ni ma haka. Amma yanzu dole ne mu san komai... Dalilai da yawa Nabeeha. Amma kwata kwata bana Saka rumanah aciki. Nasan akwai zazaafar gaba da take yi akai na..Amma bansan ta tsananta haka ba"

Bala ya kalli Hajiya Zaytunah kai tsaye.

"Hajiya, kin taɓa jin wani abu game da wata mata da ta bata a baya?"

Hajiya Zaytunah ta cika da mamaki.

"Yarinya? Wacece kuma?"

Gora ne ya amsa da wata irin murya kamar yana kokarin kauce wa wata masifa. "

A cewar shugabanmu, akwai wani SIRRI da ke tsakanin ku da Alhaji Uzairu wanda ya shafi wata mata da ta bata shekaru da suka wuce. Kuma ana zargin cewa idan kika ci gaba da rayuwa, akwai yiwuwar gaskiya ta bayyana."

Hajiya Zaytunah ta runtse ido, zuciyarta na dukan uku-uku. Yarinya? Ko dai babbar mace...Hmm Me ya faru? Sai dai wani abu yana dawowa cikin tunaninta, tsohuwar rayuwarta a gidan Alhaji Uzairu. Shekaru da suka wuce, akwai abubuwa da suka faru da ba ta taba tunanin za su iya dawowa gare ta ba.

Nabeeha ta kalli Ammin ta da damuwa.

"Ammi, ko akwai wani abu da kike tunawa?"

Hajiya Zaytunah ta dago kai, idanunta na cike da ruɗani.

"Ban da tabbas... amma ina jin cewa akwai wata babbar magana da ban sani ba."

"Shin wannan wane SIRRI ne haka ammi?" Hammad ya tanbayi mahaifiyar sa yana jujjuya zancen a fatar bakin sa...

"Tarin SIRRI ka ne da yawa Hammad. Wanda ni kaina bazan iya gaya maka takamaimai yadda suke ba. Amman nasan akwai boyayyen lamarin dake faruwa Wanda yasa ta hauhawa haka"

"Kaico rayuwar duniya kenan. Da ya yi kokarin kashe mahaifinnsa ko mahaifiyar sa. Yan uwa su cinye gadon marayu.. Sannan dangi su nemi kashe dayan su saboda abunda suka qudirar na daga dukiya da sauran su" gora ya fada yana furzar da iskar bakinsa.

🎀🎀

A cikin dakin shakatawarta, Hajiya Rumanah tana tafiya a zage-zage, zuciyarta cike da tsana da fushi. Ta kasa zama, ta kasa natsuwa. Labarin da ta samu a safiyar yau ya dagula mata lissafi, ya ruguza duk wata kwanciyar hankali da take da ita.

"Suka tsira?😂!" Ta furta cikin matuƙar mamaki da takaici, tana watsa kwanon shayi da ke gabanta. "Su suka tsira?! Me kuke nufi da hakan?"

A gefe, Hajiya Karama da Ladi suna tsaye cikin nutsuwa, suna kallonta da mamaki. Sun san cewa yau Hajiya Rumanah tana cikin wata irin damuwa da ba ta taɓa shiga ba.

"Wallahi ba zan taba bari su tsira ba! Ba zan bari wannan masifar ta cigaba ba!"

Ta ja tsaki mai karfi, ta dafe kanta kamar wacce ke jin zafi kwakwalwarta. "Me yasa ita ce kullum ke ci min buri?!"

Hajiya Karama ta dan rankwafa. "Hajiya, ki kwantar da hankalinki. Me zai hana mu sake daukar mataki?"

Hajiya Rumanah ta juyo da mugun kallo.

"Mataki? Mataki?! Me kika san game da mataki? Kin san tun daga ina wannan masifar ta fara?"

Ta ja kujera ta zauna, amma har yanzu jikinta yana bari saboda takaici. Ta dubi su da idanuwan da suka cika da tsana.

"Kullum ita ce matsalata tun farkon rayuwata! Mahaifiyarta ta aure min mahaifi! Babana wanda ya fi kowa so, mahaifiyarta ce.. Tun daga ranar muka dena zaman lafiya."

Ladi ta waro ido. "Anya kuwa?"

"Eh! Zahiri! Da mahaifiyarta ta zo, sai mahaifiyata ta koma kaskiya! Komai ya canza, babana baya shiri da mahaifiyataa, sai dai ita!"

Ta numfasa da karfi, kamar wacce ke jin zuciyarta tana kuna.

"Mahaifiyar ta. Shegiya la'ananniya data haifo mana dangin jaraba da kulafici. Kanin mahaifina ne mahaifin ta. Bayan rasuwar sa sai mahaifiyar ta aure babanmu..a baya bakuga mutuncin da ake ba. Gidanmu daya ashe ashe jira take dama tana sonsam mijinta na rasu ta aure babanmu. Kunji cin amana daya?"

Hajiya Karama ta dafe baki. "To amma menene hakan ya shafe ki?"

Hajiya Rumanah ta yi dariyar takaici. "Me yasa ba zai shafe ni ba?! Dole ne nai kishi, dole ne na tsane su! Mahaifiyarta ta aure min mahaifi, ita kuma ta aure min miji!"

Ta runtse ido, ta kaɗa kanta da sauri kamar wacce ke jin wani abu mai zafi a kanta.

"Na rasa saurayi na saboda ita! Alhaji Uzairu ni zai aura a baya, amma sai gashi ita ya aura. Ni da nake jin shi ne kad’ai nawa, amma sai aka ɗauke shi aka miƙa mata!"

Ladi ta dan girgiza kai. "To yanzu ai duk ya wuce."

"Ya wuce?!" Hajiya Rumanah ta dauke mata kafa, ta watsa mata harara. "Kika ce ya wuce? Ai wannan shine babbar matsalar! Tun da na haifi Muhammad, na dauki alkawarin cewa shi zai fi kowa a gidannan. Sai gashi yanzu, dan cikina, jinina, shi ma yana bibiyar ‘yar Zaytunah?! Wacce iriyar bakar lukutar masifar kaddara ce wannan?"

Ta tashi tsaye da sauri, ta fara tafiya a cikin dakin, tana girgiza kai da takaici.

"Na rasa uba a hannunta. Na rasa miji a hannunta. Kuma yanzu har da dana? Har da Muhammad? Ku duba fa! Muhammad yana so ya auri ‘yar waccan munafukar? Wannan ai cin fuska ne! Baiwa ne aka raina!"

Hajiya Karama ta numfasa, tana kokarin kwantar da ita. "To ki yi hakuri. Muhammad ba zai aure ta ba."

"Da gaske kike?" Hajiya Rumanah ta watsa mata wani kallo mai cike da hauka. "Da gaske kike? Idan ban dauki mataki ba, Muhammad zai aure ta! Zai zama surikin Zaytunah, ni kuwa me zan zama?! Wai ni ce za a kira da uwar surikin yarinyar da mahaifiyarta ta kwace min rayuwa?"

Ta dafe KIRJIN ta, zuciyarta na bugawa da sauri. Tsananta, haushi, kishi, bakin ciki,duk sun taru suka mamaye ta.

"Wallahi bazan yarda ba. Bazan taba yarda ba! Ba za ta ci gaba da samun nasara a kaina ba!"

Ta dauki waya, zuciyarta na tafasa. "Dole a nemo su, kuma a wannan karon ba zan yarda a yi wasa ba. Idan har suka ci gaba da rayuwa, to hakan yana nufin cewa ni na gaza. Kuma bazan yarda da hakan ba!"

Sai a lokacin ta tuna yadda labarin ya zo gare ta. Akwai wanda ya sanar da ita cewa su Hajiya Zaytunah sun tsira daga hannun Gora da Bala. Wata zuciyarta na gaya mata cewa wani daga cikin mutanenta ne ya yi sakaci.

Ta kalli Hajiya Karama da Ladi da idanuwanta da suka yi jajir.

"Ku saurara! Ba zan yarda da shirme ba. Duk wanda ya saba umarnina, zai gamu da fushina!"

Ta matse wayarta a hannunta, zuciyarta tana tafarfasa. "Na tsani Zaytunah! Na tsani iyalanta! Kuma ko da wane hali, ba zan bar Muhammad ya aure Nabeeha ba! Ko da kuwa hakan na nufin... dole ne in dauki babban mataki!"

Ladi ta kalli Hajiya Karama da mamaki. "Kin fahimci inda zaytunah ke shirin dosa?"

Hajiya Karama ta jinjina kai, ta lumshe ido. "Eh... Kuma ina jin tsoron hakan."

Hajiya Rumanah ta ja numfashi, idanuwanta na dauke da mugun ƙuduri. "Wannan karon, Zaytunah ba za ta tsira ba."

Hajiya Rumanah ta zura ido cikin wayarta, zuciyarta na tafasa da tsana da bakin ciki. Ta san cewa idan har ta zauna kawai tana magana ba tare da ta dauki mataki ba, to hakan na iya zama dalilin da zai sa komai ya rushe mata. Dole ne ta dauki matakin da zai tabbatar da cewa wannan masifa ta kare nan take.

Ta latsa lambar daya daga cikin abokan huldarta a boye, tana jiran a dauka. Da zarar an daga, ta numfasa sannan ta furta cikin wata murya da ke cike da hadari,

“Ina son ku nemo min su. Ku kama su, amma a wannan karon, ba na son kuskure.”

A dayan bangaren, muryar wani namiji mai karfi ta amsa. "Kiyi hakuri hajiya"
Chapter 14 · 0% Book details