← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 75

Sashe 20

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fawaaz yana riƙe da sitiyari, amma hankalinsa ya kasa kwanciya. Duk da cewa sun samu Nasara, har yanzu zuciyarsa ba ta bar jin wani irin nauyi ba. Idanunsa sun dan kalle ta cikin madubin motar, yana kallon Nabeeha da ke zaune a baya kusa da Hajiya Zaytunah.

Ta jingina kanta da jikin kujera, idonta a rufe, amma Fawaaz ya fahimci ba barci take ba. Sai dai ko kawai tana kokarin dan hutawa ne ko tunani.

Hajiya Zaytunah ta juyo ta dubi Fawaaz, idonta cike da godiya.

"Allah ya saka da alkhairi, Captain. Da baku zo da wuri ba, da ko me zai faru damu, Allah ne kadai ya sani... Don mun kasa tsarewarwa waɗannan mugayen mutanen da ke ta bibiyarmu"

Fawaaz ya dan sauke numfashi, yana jin nauyin wannan magana. Ba don wani abu ba, sai don yasan irin hatsarin da su Nabeeha suka tsallake.

"Mun gode wa Allah,.. Inshaa Allah su Kuma waɗannan da muka kama duka zasu Sha tambayoyi bayan mun hora su." ya amsa a taƙaice.

Bayan wani lokaci, sai Nabeeha ta bude idonta a hankali. Duk da cewa idonta yana nuna alamun gajiya, amma akwai wani irin natsuwa a fuskarta. Ta juyo tana kallon Fawaaz, yana tuƙi hankalinsa kwance.

"Da gaske ka yi tracking din wayata ne har ka gano inda muke?" ta tambaya da wata murya mai rauni, amma da alamun sha’awa.

Fawaaz bai juyo ba, amma ya gyada kai. "Eh."

Nabeeha ta dan yi murmushi, sannan ta ce, "Mashaa Allah ."

Ya ɗan danne numfashinsa, bai san dalilin da yasa zuciyarsa ta daka da karfi ba a lokacin da ta fadi hakan. Amma sai ya ce,

"Dole ne na tuna da ke, domin nasan kina cikin hatsari." Ya furta a zuciyar sa..

"Kasan sun kwace wayoyin mu sun Kona su duka?" ta kara tambaya, tana so ta ji ko zai kara wani abu.

Ya dan yi shiru, yana tunanin amsar da zai bayar. Bai saba bayyana abubuwan da yake ji ba, ko yawan amsa tambayoyi musanman game da ita, kuma yanzu ba shi da niyyar yin hakan.

"Allah ya kyauta , abu mafi muhimmanci shine mun same ku lafiya."

Nabeeha ta dan tabe baki, amma bata ce komai ba. Ta san halinsa , miskili ne. Sai dai yadda ya zo domin cetonsu, yadda ya damu da ita fiye da kowa, hakan kadai ya ishe ta sanin cewa akwai wani abu mai girma a zuciyarsa.

Tafiyar su ta cigaba cikin shiru na wani lokaci, har suka fara fita daga cikin dajin. Lokacin ya kusa wayewa, iskar safiya tana kadawa cikin sanyin daren da ya kusa karewa.

Hammad ya juyo yana duban Captain Fawaaz, yana murmushi.

"Captain, ka zama jarumin labarina!" ya fada da dariya.

Duk wanda ke cikin motar ya dara, har da su Lieutenant Ibrahim da ke gaba. Fawaaz ya girgiza kai, yana murmushi a hankali.

Nabeeha kuwa sai ta lumshe ido, zuciyarta cike da natsuwa. Wannan daren ba zai taba goguwa daga zuciyarta ba. Kuma ko da Fawaaz ba zai iya furtawa ba, amma ta san cewa akwai wani abu a tsakaninsu da babu wanda zai iya musantawa.

Motocin sojojin suka ci gaba da tsula gudu a kan titin ƙasa, suna barin dajin Arewa a baya. Ana iya jin sautin gurnanin tayoyin motar suna neman nutsuwa a ƙasa mai laushi. Iskar safiya tana kadawa, tana ɗauke da dumin farkon rana.

Nabeeha ta jingina da kujerar motar, tana kallon yadda titin ke ratsa ta cikin duhun da ya rage a sararin samaniya. Kowane numfashinta yana ɗauke da jin daɗin tsira, amma a lokaci guda, zuciyarta ta cika da tunani. Idanunta sun kai ga Captain Fawaaz, wanda ke riƙe da sitiyari da kwanciyar hankali kamar yadda ya saba.

A zuciyarta, tana tambayar kanta, shin wannan shi ne Fawaaz ɗin da ta sani? Miskilin da ke guje mata? Amma yau, ya tsaya tsayin daka ya cetota. Hakan ya sa zuciyarta cika da wani yanayi da ba ta iya bayyanawa ba.

A gefe guda, Hajiya Zaytunah ta juya tana duban Fawaaz, sannan ta sauke ajiyar zuciya.

"Allah ya saka muku da alheri, Captain," ta furta cikin gamsuwa. "Kai da mutanenka kun cika jarumai. Allah ya biya ku da gidan aljanna"

"Aameen" su lieutenants suka amsa..

Fawaaz bai ce komai ba, sai ya gyada kai kaɗan, yana mai mayar da hankali kan tuƙinsa. Amma idan aka kalli fuskarshi da kyau, za a iya hango wani irin natsuwa a cikinta.

A baya, Hammad yana kallon sojojin da suka jera a motocin baya ta cikin taga. Cikin farin ciki, ya ce,

"Kai! Kamar a fim! Captain Fawaaz da sojojinsa sun zo sun ceci talakawa daga hannun azzalumai!"

Duk wanda ke cikin motar ya dara. Nabeeha ta ɗan yi dariya, amma ta lura da cewa Fawaaz bai ce komai ba.

A hankali, ta matsa kusa da shi, ta ɗan sassauta muryarta.

"Yaya jikinne??"

Ya ɗan kalleta ta cikin madubi, sannan ya maida dubansa gaba. "Lafiya lau."

Nabeeha ta taɓe baki
. "Kamar ba ka da lafiya."

Fawaaz ya sauke numfashi, ya ɗan rage gudun motar. Yana jin tambayarta tana tasiri a zuciyarsa, amma bai so ya bayyana hakan ba.

A ƙarshe, ya furta cikin wata murya mai taushi fiye da yadda ta zata,

"Wani lokaci, akwai abubuwan da mutum bai taɓa tunanin zai yi ba, amma sai gobe ta zo da nata labarin."

Nabeeha ta yi shiru tana kallonsa, tana ƙoƙarin fahimtar abin da yake nufi.

"Me kake nufi?" ta tambaya.

Fawaaz ya ɗan yi shiru kafin ya ce, "nothing much, Babu komai."

Nabeeha ta dan murmusa. Tana jin cewa akwai wani abu da yake ji a zuciyarsa, amma kamar kullum, Fawaaz na ɓoye komai. Amma hakan ba zai hana ta fahimtar cewa akwai abu mai ƙarfi da ke tattare da shi ba.

"Na sani." Ta furta a hankali.

Ya ɗan kalleta, alamar tambaya a fuskarsa.

"Na sani cewa ka damu da ni." Ta fada cikin zuciyar ta.,

Fawaaz bai ce uffan ba. Amma yadda ya kalleta da yadda numfashinsa ya sauya, hakan kadai ya tabbatar mata da cewa ta fadi gaskiya.

A hankali, motar ta ci gaba da tafiya, har sai da suka soma shiga birni. Rana ta fara fitowa a sararin samaniya, tana bayyana sabon safiya, amma a gare su, wannan safiya sabuwa ce ta rayuwa, ta fahimta, da kuma ƙaddara da ba su san yadda za ta kaya ba.

Fawaaz ya kalli titin gaba, yana tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. An dade ana tafiya, amma yanzu gida yana kusa. Ya ji wani nauyi yana sauka daga zuciyarsa, kamar wanda aka daga masa wata babbar kaya da ta dade tana damunsa.

Ya zaro wayarsa daga aljihunsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa a hankali. Lokaci ne na kiran mahaifinsa, Major General Dawud, don sanar da shi cewa suna kan hanya, kuma suna nan kusa da isowa.

A lokacin da ya danna lambar, ba a dauka ba sai da aka buga sau biyu. Yana cikin shirin sake kira, sai ga amsa daga dayan bangaren.

"Fawaaz?"

Muryar mahaifinsa ta fito da karfi, cike da zurfin tunani da kulawa. Akwai wani nauyi a cikin sautin sa, wanda ya tabbatar da irin damuwar da yake ciki tun lokacin da aka fara wannan abu.

Fawaaz ya dan lumshe idanu, yana jin yadda numfashinsa ke fita da sauki. "Morning sir!! gamunan muna hanya, za mu iso gida yanzu, Insha Allah."

Shiru ya biyo bayan hakan, kamar Major General Dawud yana kokarin fahimtar cikakken abinda ya ji. Bayan wasu ‘yan dakiku, sai ya sauke wata ajiyar zuciya.

"Kun iso gari... Sun kubuta? "

"Eh,Baba. Mun tsira, babu wata matsala. Su Aunty Zaytunah dasu Hammad suna lafiya. Muna cikin motocin mu yanzu, kuma muna gab da shigowa cikin anguwa."

A daya bangaren, an sake yin shiru. Sai daga baya aka ji muryar Major General Dawud yana cewa, "Allah ya muku albarka.. ka gayawa lieutenants Ina godia kwarai. Akwai gwaggwabar tagomashi da zai biyo musu da yardar Allah. Tell them I say weldone...."

Fawaaz yayi murmushi yana duban su lieutenants yace da mahaifin sa,

"Inshaa Allah sir. Allah ya Kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka. Aameen.."

"Aameen muna jiran ku," Major General Dawud ya kara fada, muryarsa na nuna cewa yana cikin tsananin shirin ganin su..

"Zamu iso cikin mintuna goma zuwa sha biyar," Fawaaz ya fada.

"Allah ya kiyaye hanya," Major General Dawud ya kara fada, kafin ya katse.

"Aameen" kit major general ya katse Kiran. Fawaaz ya dubi su lieutenants yana sanar musu abunda mahaifinnsa yace ya gaya musu. Nan da nan Kuma wayoyin kowannen su Sako ya shigo masa daga major general dawud mafia.

"Weldone soldier! Your Legacy Will Live Forever, Long after the battles are won, your bravery and dedication will be remembered. You are not just a soldier, you are a hero, a protector, and a symbol of strength. Stand tall, keep the fire of duty burning, and never forget the difference you make. Check your account balance. Allah ya Saka da alkhairi"

Suka fara murna baki daya da farin ciki... Fawaaz yayi murmushi bayan lieutenant ya karanto masa sakon.. sai murna sukeyi sunata godiya. Don tuni har wasunsu sun fara Jin alerts na kudi daya tuttura musu..

Fawaaz ya lumshe idanu na dan lokaci, yana jin yadda gajiyarsa ke sauka a hankali. Ya san cewa komai bai kare ba, amma akalla sun tsira daga wani babban hatsari.

Ya juyo yana duban Hajiya Zaytunah, wadda ke zaune cikin motar da kwanciyar hankali. Duk da alamun gajiya a fuskarta, akwai murmushi mai cike da natsuwa a saman lebbanta.

"Su baba suna jiranmu," Fawaaz ya fada mata.

Hajiya Zaytunah ta gyada kai a hankali. "Allah ya nuna mana lokacin da za mu samu kwanciyar hankali bayan wannan wahala."

Hammad ya dan ja numfashi mai zurfi yana gyara zamansa. "Wai ma gida dai ya kusa kenan?"

Fawaaz ya kalle shi daga gefe. "Idan ba canzawa akayi ba, eh, mun kusa isa gida.... Senior man"

Hammad ya sake gyara zamansa yana fadin,

"Toh, idan muka iso, sai a samo min abinci mai kyau. Na gaji da wannan yunwar!"

Suka sake Saka dariya baki daya... Banda Fawaaz da bai ce komai ba, sai ya juyo ya kalli titin gaba. Motar na cigaba da tafiya a hankali, tana ratse cikin titunan da suka saba bi.
Chapter 20 · 0% Book details