← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 75

Sashe 75

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ya yi dariya, yana dora goshinsa a nata. "Sai dai in ci gaba da nuna miki cewa bazan taba sauya tunani ba. Ke ce SIRRINa, kuma har abada, ke ce AKWATIN SIRRINa."

Ta lumshe ido, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da nishadi. "Kuma kai ne komai nawa, Fawaaz. Ba zan taba iya rayuwa babu kai ba."

Ya kama hannunta, yana dora mata kiss a bayansa. "Ko bayan rayuwa ma, soyayyata gare ki zata ci gaba da wanzuwa. Zuciyata ta kasance taki ce har abada, Nabeeha."

Duk da maganar tana da nauyi, sai da ta yi murmushi. "Ka fiye soyayya, Captain. Yanzu dai ka barni in ci gaba da barci, saboda Muhammad Dawud na iya farkawa da dare."

Ya jinjina kai, yana sake kwantar da ita. "To Allah ya sa mafarkin ki na da dadi."

"Amin."

A hankali ya rufe idanunsa, yana rungume ta da kwanciyar HANKALI. Cikin zuciyarsa, yana jin wani irin nutsuwa da bazai iya misaltawa ba.

HANKALI ya kasance cikin KIRJI, amma SIRRI yana da nasa mazauni. Kuma a karshe, Fawaaz ya fahimci cewa ba KIRJI bane ke dauke da SIRRIN MAI HANKALI, ba HANKALI bane ake ajiye shi. SIRRIN mai hankali yana hannun wanda aka mallaka masa zuciya da rayuwa gaba daya. Kuma gareshi, wannan mutum daya tilo ce, Wato...Nabeeha uzair Muhammad..Mrs Fawaaz dawud mafia..

Ta rungume shi da ƙarfi, tana jin tsantsar soyayyarsa yana ratsa zuciyarta. "Kauna ta gare ka ba zata taba gushewa ba, Ya Fawaaz dina." A haka bacci mai nauyi ya dauke su...

A wannan dare, soyayyarsu ta cika, zuciyoyinsu sun hadu, kuma SIRRIN su ya ƙare cikin ƙauna da aminci.

°°°°°
_Alhamdulillah! Duk da gajiyar tafiya, da ƙalubalen rubutu, da neman kyakkyawar mafita ga labari, a yau na kammala littafin KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA) gaba ɗaya._

_Na fara wannan tafiya da zuciya cike da burin bayar da labari mai ma’ana—wanda zai ƙunshi soyayya, sirri, hakuri, da yarda da kaddara. A ƙarshe, labarin ya zama fiye da haka. Ya zama tafiya ta soyayya da ƙaddara. Tafiya ta sirri da amana. Tafiya ta mutum da zuciyarsa, da wanda ya cancanci ya zama Akwatin Sirrinsa._

_Ina roƙon Allah Ya sa albarka a cikin wannan aiki, Ya yafe mun da ku duk wani kuskure da na rubuta, Ya kuma saka lada ga duk wanda ya karanta da niyyar neman nishaɗi ko darasi._

_Dukkan halaye da aiyuka na kyawawan jaruman wannan littafi ina fatan su zama abin koyi. Kuma kuskuren da suka aikata ya zama izina gare mu. Ina rokon Allah Ya gafarta mana, Ya sa mu zama cikin waɗanda suke koyi da alheri, su kauce wa sharri._

_Na gode da soyayya, goyon baya, da addu’o'in da aka yi mun a wannan tafiya. Sai littafi (zafafa paid books) na gaba, idan Mai Duka Ya kai mu!_

_Alhamdulillah!_ _Alhamdulillah!_ _Alhamdulillah!_

_wannan littafi na kudi ne, wato daya daga cikin jerin littattafan zafafa biyar... Nera dari biyar N500 ne ga duk mai son mallakar sa.... Domin karin bayani sai a tuntubeni ta 09134848107_

_Taku: Nana hafsatu... (Mss xoxo)_
Chapter 75 · 0% Book details