← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 75

Sashe 46

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawud ya harare ta. “Kiyi shiru! Na fahimci cewa kin fi son mutanen waje fiye da mutanen gidan nan. Kina ba su SIRRIN gidan mijinki, kina ba su damar cutar da iyalansa!”

Hajiya Zaytunah ta dafe KIRJI, tana jin yadda zuciyarta ke tafarfasa. “Hauwa, don me kika yi haka?”

Hajiya Hauwa ta sunkuyar da kai, ba ta da bakin cewa komai. Tunanin yadda za ta kare kanta ma ya gagara.

Bayan wani dan lokaci na shiru, Major General Dawud ya dubi Hauwa da tsananin fushi.

“Babu wata maganar da za ta iya kare ki a wannan lamarin. Hajiya Hauwa, daga yau… na sake ki saki biyu!”

Gaba daya dakin ya dauki shiru. Gwaggo Hafsat ta zabura. “Dawud! Ka yi hakuri… Ka yi tunani. Kada ka yanke hukunci cikin fushi.”

Dawud ya girgiza kai, yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa. “Gwaggo, ba zan iya rayuwa da mace wacce ba ta girmama amana ba. Mace wacce ba ta kula da lafiyata da tsaron iyalina ba.”

Hajiya Hauwa ta fashe da kuka, amma Dawud bai kula da ita ba.

Gwaggo Hafsat ta dafa kafadarsa. “Dawud, na fahimci halin da kake ciki, amma kada ka yi sauri wajen cika saki na uku. Ka ba kanka lokaci. Ka bar wa Allah komai.”

Dawud ya runtse ido, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Ya janye numfashi da karfi.

“Na bar miki ita, Gwaggo. Ki yanke hukunci a kanta.”

Hajiya Hauwa ta sunkuyar da kai, hawaye na kwarara daga idonta. Ta san cewa bata da wata mafita. Aminta ya kare, martabarta ta rushe.

Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi, tana jin wani irin yanayi mara dadi. Duk da cewa ta sha wahala a hannun kishiyoyinta, amma ba ta taba tunanin cewa Hajiya Hauwa za ta iya aikata hakan ba.

Daga wannan rana, komai ya canza a cikin gidan Major General Dawud.

Gwaggo Hafsat ta ci gaba da rarrashin danta, yana kokarin samun nutsuwa daga abin da ya faru.

A gefe guda kuwa, Fawaaz da Nabeeha sun fahimci wani abu—aminci da soyayya ba kawai ana fada su suke ba. Sai an kiyaye su, sannan ake iya samun kwanciyar HANKALI.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:41_

Gidan ya dauki shiru, sai karar kukan Hajiya Hauwa kadai ke tashi. Ta durkushe a kasa, hawaye na kwarara daga idanunta, tana girgiza kanta cike da nadama.

Ta rarrafa zuwa wajen Hajiya Zaytunah, ta rike kafafunta da rawar jiki. “Dan Allah, Zaytunah, ki yafe min! Ki dubi Allah ki gafarta min. Wallahi na yi kuskure!”

Hajiya Zaytunah ta dauke kai, zuciyarta cike da radadi. Ba ta taba tunanin cewa hajia hauwa za ta iya cin amanarta haka ba.

“hajiya hauwa, me na miki da kika yanke shawarar ba su bayanan da suka kusa hallaka ni da ‘ya’yana?” Muryarta ta bayyana rauninta da takaici.

Hajiya Hauwa ta kara rushewa da kuka, tana girgiza kai. “Na yi kuskure! Na yi babban kuskure, Zaytunah. Ba na so hakan ta faru! Wallahi sharrin zuciya ne ya rufe ni.”

Sai ta koma wajen Gwaggo Hafsat, ta kama hannayenta da karfi. “Gwaggo, ki yafe min! Ki tausaya min! Na san na cutar da ku, amma dan Allah, ki gafarta min.”

Gwaggo Hafsat ta girgiza kai, tana jin yadda zuciyarta ke tafarfasa. “Hauwa, ba wai yafe wa ba ne matsala… matsalar ita ce, me ya sa kika aikata hakan? Kin yi aure da d’a na, amma har yanzu ba ki san darajar iyali ba?”

Hajiya Hauwa ta durkushe a kasa, ta rike kafafuwan Gwaggo Hafsat, tana kuka kamar jaririya. “Na tuba, Gwaggo. Wallahi na tuba! Ku yafe min, kada ku yanke min hukunci na har abada!”

Ta juyo zuwa ga Major General Dawud, wanda ke tsaye cikin rashin jin tausayinta. Idanunsa sun nuna takaicinsa.

“Dawud, Alhaji… dan Allah ka yi hakuri!” Ta fashe da kuka, tana rike hannunsa. “Wallahi ban san abinda na aikata zai kai ga haka ba! Ka yafe min, kada ka rabu da ni haka.”

Dawud ya sauke numfashi, yana jin wani nauyi a zuciyarsa. Ya sha wahala a aikinsa, amma bai taba tunanin cewa matsala mafi muni za ta fito daga gidansa ba.

Ya dubi Hauwa, yana jin takaicin yadda ta wofintar da amana.

“Hauwa, ba wai fushina kawai kika haddasa ba. Kin wargaza amana, kin jefa rayuwar mutane cikin hadari, kuma kin ci amana ta a matsayin miji.”

Hajiya Hauwa ta kara fashewa da kuka. “Ka tausaya min! Na yarda da hukuncinka, amma dan Allah kada ka rabu da ni haka!”

Duk wanda ke dakin ya cika da mamaki. Nadamar da Hajiya Hauwa ke ciki ta bayyana karara.

Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi, sannan ta kalli Gwaggo Hafsat. “Gwaggo, ni na yafe mata.”

Hajiya Hauwa ta dago da mamaki, tana kallon Zaytunah da hawaye. “Zaytunah… kin yafe min?”

Zaytunah ta girgiza kai. “Eh, na yafe miki. Amma hakan ba yana nufin zan iya mantawa da abin da kika aikata ba.”

Dawud ya jinjina kai, yana jin yadda zuciyarsa ke girgiza.

“Gwaggo,” ya fadi a hankali. “Zan bari komai a hannunki. Na yanke saki biyu, amma ba zan cika na ukun ba har sai na yi dogon tunani.”

Hajiya Hauwa ta rushe da kuka, tana jin cewa ko da kuwa ba a sake ta yanzu ba, ta riga ta lalata amana da soyayyar da take da mijinta.

A wannan dare, ta kwana cikin nadama. Ta fahimci cewa amana bata da kyan tozarta, kuma cin amana na iya wargaza rayuwar mutum.

Daren ya ci gaba da shuru a cikin gidan, amma zuciyar Hajiya Hauwa na kara daukar zafi. Duk da cewa Hajiya Zaytunah ta yafe mata, har yanzu ba ta iya kallon idon kowa ba. A zuciyarta, tana jin nauyin zunubin da ta aikata, cin amana a cikin gidan da ya bata mafaka.

Tana durkushe a kasa, jikinta na karkarwa, tana cigaba da kuka mai tsanani. “Gwaggo… Dan Allah… Dan Annabi, ki shawo kan Dawud kada ya rabu da ni. Wallahi na tuba. Na gane girman kuskurena!”

Gwaggo Hafsat ta sauke ajiyar zuciya. Idanunta sun nuna takaici, amma a lokaci guda, tana jin tausayin Hauwa. Sai dai, cin amana ba karamin abu bane.

“Idan muka yafe miki, Hauwa,” Gwaggo ta fada cikin nutsuwa, “yaya za mu sake dogaro da ke? Yaya za mu koma mu cigaba da rayuwa da ke, muna jin tsoron cewa wata rana za ki sake cin amana?”

Hajiya Hauwa ta girgiza kai da sauri, hawaye na kwarara daga idonta. “Wallahi Gwaggo, ba zan sake ba! Na tuba har abada! Zan iya rantsuwa da komai mai tsarki!”

Major General Dawud ya dafa goshinsa da hannu biyu, yana jin nauyin tunani. Yana son ya yi hukunci bisa adalci, amma zuciyarsa na gaya masa cewa ba abu ne mai sauki ba. Ya dauki lokaci yana tunani, sannan ya kalli mahaifiyarsa.

“Gwaggo, idan ba ke ba… wacece za ta iya yanke hukunci a kan wannan lamarin?”

Gwaggo Hafsat ta kalli danta. Ta jima tana nazari, sannan ta juyo ga Hauwa.

“Hauwa, ki tashi.”

Hajiya Hauwa ta mike da sauri, jikinta yana karkarwa. Ta sunkuyar da kai, tana jiran hukunci.

Gwaggo Hafsat ta sauke numfashi. “Na ji rokonki. Kuma saboda darajar auren da kuka yi da Dawuda, zan roke shi da kada ya cika saki na uku. Amma akwai sharadi.”

Hajiya Hauwa ta dago kai cikin fargaba. “Gwaggo, komai ne zan yi! Ki fada min.”

Gwaggo Hafsat ta kalli Major General Dawud, sannan ta mayar da kallonta ga Hauwa. “Zaki bar gidan nan. Ba zan ce ya sake ki ba, amma dole ki bar gidan nan na wani lokaci har sai an tabbatar da cewa ba za ki sake yin irin haka ba.”

Hajiya Hauwa ta bude baki da mamaki. “Gwaggo… amma ina zan je?”

“Ki koma gidan iyayenki ko gidan ‘yan uwanki. Idan har da gaske kina son komawa cikin wannan gidan, sai mun tabbatar cewa kin shiryu.”

Shiru ya biyo baya. Hajiya Hauwa ta yi shiru, zuciyarta tana tafarfasa. Kamar dai a yanzu aka kada ta daga rayuwarta.

Ta juyo ga Dawud, tana neman sassauci. “Dawud… kai ne mijina. Ka yanke hukunci.”

Dawud ya girgiza kai. “Na bar wa Gwaggo hukunci, kuma ba zan canza ra’ayi ba.”

Hajiya Hauwa ta sulale a kasa, tana kuka. Ta fahimci cewa ta yi babban kuskure da ba za ta iya gyarawa ba a dare daya.

Hajiya Zaytunah ta kalli yadda take kuka, ta kalli Dawud, sannan ta sauke ajiyar zuciya. Ta san cewa Hauwa ta ci amana, amma zuciyarta ba ta so a kore ta da zafi haka ba.

“Gwaggo, idan zan iya magana…”

Dawud ya dago kai yana kallonta. Gwaggo Hafsat kuwa ta ce, “Ki fadi.”

Hajiya Zaytunah ta gyara zamanta, ta dubi Hauwa da nutsuwa. “Ina so ta bar gidan nan na wani lokaci kamar yadda kika ce, amma kada mu haramta mata dawowa gaba daya. Idan har ta gyara halinta, sai a sake tunani.”

Hajiya Hauwa ta dago kai, tana kallon Zaytunah da mamaki. “Zaytunah… kina nufin har yanzu kina tunanin zan iya dawowa?”
Chapter 46 · 0% Book details