← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 75

Sashe 47

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaytunah ta jinjina kai. “Na san cewa cin amana ba abu bane mai sauki. Amma idan har da gaske kina nadama, ba zan hana ki damar gyarawa ba.”

Gwaggo Hafsat ta jinjina kai. “Shikenan. Wannan hukunci ne mai kyau.”

Major General Dawud ya sauke ajiyar zuciya. “Za ki bar gidan nan gobe da safe.”

Hajiya Hauwa ta lumshe ido, tana jin wani irin nauyi a zuciyarta. Ta san cewa ba ta da wata mafita da ta wuce karbar hukunci.

A wannan dare, ta kwana cikin tunani. Ta fahimci cewa wasu kura-kurai suna da kudin da sai an biya su kafin a iya cigaba da rayuwa.

_______

Toh haka rayuwar ta cigaba da garawa, hajia hauwa maijiddah ta bar gidan major general dawud mafia na wani dan lokaci kafin a sake nemanta. Sannan itama kotu taci tarar ta tunda tabada gudunmawa a Kamen da aka yiwa su hajia zaytunah. Sai dai kotu ta sassauta mata hukunci saboda ba ita akaje wajen boka. Batada masaniya akan Kamen su hajia zaytunah da irin azabar da aka gana musu duk batada hannu aciki. Lefinta daya. Tura sakonnin da ta yiyyi sune kawai. Amman bayaga wannan batada lefin komai...

Bangaren su Alhaji Amiru da uzairu kuwa sai hamdala. Alhaji uzairu yana zuwa ya ziyarci ya'yansa ya gana dasu, haka zalika yaran nasa na zuwa su gayshe da shi suna ziyartar su...

A karshe dai, an saka ranar bikin su Humayrah da Raudah. An tsaida sati biyu daga lokacin za a ɗaura aure. Amma sai aka daga bikin Nabeeha da Muhammad zuwa gaba, bayan wata guda da auren su Raudah. Dalili kuwa shine, halin da suka tsinci kansu a ciki, zancen aure na Nabeeha da Air Captain Muhammad ya zo ba zato ba tsammani, har wasu na ganin kamar al’amari ne da za a iya jinkirta don komai ya lafa.

Amma wani ne bai iya fahimtar hakan ba… Fawaaz!

Lokacin da ya samu tabbacin cewa idan bai yi maza ba, za a aurar da Nabeeha ga wani, hankalinsa ya gushe. Bai taba tunanin wani zai iya kasancewa mijinta ba sai shi. Bai san sanda zuciyarsa ta fara tafarfasa da tsoro ba.

Rashin cin abinci, rashin samun barci, da damuwa suka fara shafar shi. Har ya soma rama! Wannan ba abu ne mai sauki ba ga shi da shi. Yana da mugun girman kai, amma kishi ya wofintar da shi.

Yanzu komai ya gaza, idan bai dauki mataki ba, Nabeeha za ta zame masa tarihi…

--
Bikin yayan Major General, Raudah da Wysha Humayrah Dawud, da angonta Fahad, dan gidan Chief Judge Abdulfatah, ya soma ne da tea party. Aka tsara komai cikin nutsuwa da kwalliya mai kyau. Farfajiyar gidan Major General Dawud ta sha ado da kyawawan furanni da haske na musamman.

Bayan tea party, an shirya bachelorette party mai kayatarwa. Ita da Raudah Dawud Mafia, wadda za ta auri Barrister Ridwan, sun kasance cikin farin ciki.

Ana tsakiyar shagalin ne aka zo da wani tsari na musamman..Black & White Party! Amaren da kawayensu duk sun sanya white gowns masu daukar hankali, yayin da mazajen suka sanya black suits da white ties.

Humayrah da Raudah sun kasance cikin farin ciki...

Nabeeha ta fito cikin wani black gown mai daukar hankali. Rigar ta kwanta daidai da jikinta, ta zauna a kugu, tana fidda kwarjini. Gashinta mai laushi an warware shi, yana sauka har bisa kafaɗunta. Bata saka komai a wuyanta ba face wani siririn sarka mai kyau. Hannayenta sun sha zoben azurfa, idanunta sun sha kwalliya kamar ta fito daga labarin soyayya.

Sai dai Fawaaz bai so ganin hakan ba. Hankalinsa ya tashi!

Ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi da bai taba shan irinsa ba. Yana jin kishi kamar zai cire ransa. Wannan kyawun fa, ba shi kadai ne zai gani ba!

Yana tsaye, idanunsa sun kafa kan Nabeeha, sai dai ita ta kasa lura da shi. Ta shiga jin dadin wasan tare da sauran kawayenta, tana dariya, tana motsa jikinta cikin nishadi.

Wani abu ya daki zuciyarsa.

Hankalinsa ya gushe. Bai san sanda ya nufi sashensa ba. Bai san sanda ya jawo wata rigarsa ba, sannan ya dawo inda take.

Lokacin da ya iso, har lokacin tana cikin wasan. Ba tare da jin kunya ba, ya ja hannunta.

Nabeeha ta zabura. “Yaa Fawaaz! Me haka?”

Bai bata amsa ba, sai kawai ya dauki rigarsa, ya dora mata a kafada.

Ta daga idanunta da mamaki. “Lafiya?”

“Ki saka,” ya fada a hankali.

“Me ya faru?”

Ya dube ta da idanunsa masu zurfi, sai ya matsa kusa da ita. Muryarsa ta dan murya, cikin rada,

"Da gaske so kike kowa ya cigaba da kallon ki haka?"

Zuciyarta ta buga. Idanunta suka fadi.

Ji take tamkar yana ce mata "kin fi dacewa da idanuna kawai."

Ba tare da bata lokaci ba, ya rike hannunta, ya jata daga wajen. Kowa ya tsaya da abin da yake yi, yana kallonsu da mamaki.

Ya kaita motarsa. Ya bude mata, ta shiga da rashin fahimta, sannan ya zagaya ya shiga shima.

Maimakon ya tada motar, sai ya kwantar da kansa a kan sitiyari.

Shiru ya biyo baya.

Nabeeha ta juyo ta kalle shi. “Yaa Fawaaz?”

Bai ce uffan ba. Sai dai idanunsa sun rufe, yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa.

Ta kura masa ido. A yanzu, da gaske ya rame. Ya yi duhu kamar ba Fawaaz ba.

Ta dafa hannunsa. “Ka kwantar da hankalinka.”

Sai ya dago, idanunsa suka hadu da nata. A karo na farko, bai iya boye damuwarsa ba.

"Da gaske za ki bar ni?"

Ta bude baki, amma bata san me za ta ce ba.

"Da gaske za ki auri wani?"

Zuciyarta ta buga da karfi. Bai taba tambayar ta haka ba. Bai taba fadin irin wadannan kalmomin da kansa ba.

Sai ta runtse idonta, zuciyarta tana neman bugawa da sauri. Soyayyar Fawaaz... ta fara bayyana!

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:42_

Zuciyarta tana bugawa da sauri. Tambayar da Fawaaz ya yi mata tana yawo a kunnenta,

"Da gaske za ki bar ni?"

"Da gaske za ki auri wani?"

Nabeeha ta kasa bude baki. Tana jin numfashinsa yana fita a hankali, amma yana da nauyi kamar yana shan wahala.

Tana kallonsa, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama. Ta san Fawaaz miskili ne, ba ya fada kai tsaye, ba ya taba bayyana soyayya ko damuwarsa. Amma wannan karon… ya kasa boyewa!

Ta hadiye yawun bakinta. “Yaa Fawaaz…”

Ya dago idanunsa, suka hadu da nata. Idanuwansa sun canza, akwai damuwa, akwai tsoro, akwai kishi… akwai abu da ba ta taba gani a tare da shi ba.

Bata taba ganin Fawaaz a haka ba. Bai da karfin yin kuka, amma idanunsa sun bayyana rashin kwanciyar hankali.

Ta dafa kan giyar mota a hankali. “Ka kwantar da hankalinka.”

Shiru. Bai ce komai ba. Sai dai ya lumshe idanunsa na wasu dakiku, sannan ya bude su a hankali.

Ya dago hannunta daga inda take dafe da shi, ya matse cikin nasa.

Jikinta ya dauki rawa. Duk da sanyin AC, amma tafin hannunsa yana da dumi.

"Me yasa zuciyata ke bugawa haka?" Ta raya a ranta.

A hankali, ya bude baki, muryarsa kamar mai radadi. “Nabeeha… ki fada min, da gaske ne?”

Ta runtse ido, ta bude. “Menene da gaske?”

Ya dan saki ajiyar zuciya. “Zaki aure shi?”

Ta dauke kanta gefe. Babu abin da ta tsana irin wannan tambayar, saboda itama ba ta san me zai faru da ita ba.

“Bana son ayi auren.” Muryarsa ta soma sauyawa.

Ta dago da sauri. “Me kake nufi?”

Fawaaz ya juyo, ya kalle ta sosai, ya bude baki, amma sai ya sake rufe shi. Bai san me zai fada ba.

"Ba zan iya fadin cewa ina son ki ba. Amma ba zan iya barin wani ya same ki ba."

Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. “Kiyi wani abu. Karki amince.”

Ta girgiza kai. “Ya Fawaaz, aure ba wasa ba ne.”

Ya dan rike kansa. “Ke kike tunanin wasa nake? Ke kike tunanin wannan abu wasa ne?”

Ta yi shiru.

Ya ci gaba da fadin, “Tun da kika san cewa aure ba wasa ba ne, me zai hana ki duba zuciyarki ki tabbatar ko kina son shi?”

Hankalinta ya tashi. Ta furta cikin kasa da murya, “Bana son shi…”

Ya dago da sauri, yana kallonta da mamaki. “Me kika ce?”

“Bana son shi,” ta maimaita.

Numfashinsa ya fara sauka a hankali. Ya kura mata ido.

“Ina so ace na samu hanyar kubuta daga wannan matsala,” ta fada a hankali.

Fawaaz ya jinjina kai. “To ki fada. Idan bakya so, ni zan fitar da ke.”

Ta dago ido, tana kallonsa. “Ta yaya?”

Ya shafa sumar kansa. “Ki bar wannan a kaina.”

Zuciyarta ta doka.

Fawaaz zai iya yin komai don ya hana ta barinsa? Don Allah, menene ma’anar hakan? Wannan ba kishi ba ne kawai… wannan soyayya ce!

Ta sake kallonsa, zuciyarta cike da mamaki da ruɗani. A karon farko, zuciyarta ta fara fahimtar Fawaaz.

Shiru ya biyo baya. Shiru mai nauyi.
Chapter 47 · 0% Book details