← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 75

Sashe 45

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gaggauce, Nabeeha da Fawaaz suka tashi daga inda suke zaune a lambun gidan. Karan bugun kofa ya kara karfi, alamun mai bugun yana cikin gaggawa ko fushi.

Nabeeha ta dubi Fawaaz da damuwa. “Waye zai iya bugun kofa haka?”

Fawaaz bai amsa ba. Sai ya nufo kofar, yana kokarin ganin wanda ke waje. Da ya bude, sai ya hango wani matashi tsaye, fuskarsa cike da gumi, yana sauke numfashi.

Matashin ya dubi Fawaaz da Nabeeha cikin gaggawa. “Dan Allah, ina son ganin Major General Dawud.”

Fawaaz ya hade gira. “Me ke faruwa?”

Matashin ya dan rankwafa. “Sun kama wani mutum da ke da alaka da abubuwan da suka faru a baya. Shi ne mutumin da ya taimaka wajen hada bokan da su Hajiya Rumanah!”

Zuciyar Nabeeha ta buga. Ta kalli Fawaaz, shi ma yana kallonta da wani irin yanayi.

Fawaaz ya matsa gaba. “Ina aka kama shi?”

Matashin ya girgiza kai. “An kama shi ne a kusa da garin Dunaka Yana kokarin tserewa zuwa wani yanki na yankin Arewa. Amma jami’an tsaro sun gano inda yake suka cafke shi.”

Nabeeha ta sauke numfashi. Wannan sabon labari yana nufin cewa har yanzu akwai wasu bayanai da ba a sani ba game da shirin da aka yi na hallaka su da mahaifiyarta.

Fawaaz ya shafa kansa, sannan ya dubi matashin. “Major General Dawud yana nan ba?”

“Ina tunanin yana ofishinsa.”

Fawaaz ya juyo zuwa ga Nabeeha. “Ina ganin ya kamata mu sanar da shi nan da nan.”

Nabeeha ta gyada kai, zuciyarta cike da tsanani. Wannan sabon labari yana nufin cewa akwai wani sabon abu da zai fito fili wataƙila wanda zai canza komai.

A cikin gida, Zaytunah tana zaune tare da Gwaggo Hafsat a daki, suna tattaunawa.

Gwaggo Hafsat ta gyara zamanta, sannan ta dubi Zaytunah da kulawa. “Zaytunah, akwai wata magana da nake son yi da ke.”

Zaytunah ta kalle ta. “Mene ne Gwaggo?”

Gwaggo Hafsat ta sauke numfashi. “Akwai wani mutum da ya zo mini da zancen ki.”

Zaytunah ta bude ido da mamaki. “Mutum?”

Gwaggo Hafsat ta gyada kai. “Eh. Mutumin da ya san halin da kika shiga, kuma yana son ya taimaka miki.”

Zaytunah ta dan numfasa. “Gwaggo, idan maganar aure ce, ni fa har yanzu ba ni shirya ba.”

Gwaggo Hafsat ta murmusa. “Na fahimta. Amma ki sani, babu wanda yake shirya a lokaci daya. Sai dai a hankali ake fahimtar cewa lokaci ya yi.”

Zaytunah ta sunkuyar da kai, zuciyarta cike da tunani. Shin ta shirya budewa wani sabon zuciyarta?

A bangaren Major General Dawud kuwa, yana cikin ofishinsa lokacin da sakon kama wannan mutumin ya iso gare shi.

Ya kira Fawaaz da Nabeeha, sannan suka zauna a gaban sa.

“Kun san wanda aka kama?” in ji Major General Dawud.

Fawaaz da Nabeeha suka girgiza kai.

Major General Dawud ya cigaba. “Sunan sa Malam Balarabe. Shine mutumin da ya yi wa su Hajiya Rumanah jagora zuwa wurin boka. Kuma yana da wasu bayanai da zai iya fada mana.”

Zuciyar Nabeeha ta buga. “Me yasa yake kokarin guduwa?”

Major General Dawud ya dan numfasa. “Saboda yana jin tsoron cewa bayanin da zai fadi zai iya jawo masa matsala.”

Fawaaz ya hade gira. “Me kuke son mu yi yanzu?”

Major General Dawud ya mike. “Za a yi masa tambayoyi a ofishin ‘yan sanda. Idan har yana da wasu sirrika da zai bayyana, to lokaci ya yi da za mu ji komai.”

Fawaaz ya dan kalli Nabeeha, sai ya ga yadda take ta tunani. Duk da cewa ta yi kokarin boye damuwarta, amma yana iya fahimtar cewa zuciyarta cike take da rikicewar tunani.

A zuciyarsa, Fawaaz ya dauki alkawari, duk abinda zai faru, zai kasance tare da ita.

A daren ranar, Major General Dawud, Fawaaz, da Nabeeha sun isa ofishin ‘yan sanda don sauraron bayanan da Malam Balarabe zai bayar.

A cikin dakin tambayoyi, Malam Balarabe ya zauna cikin rashin kwanciyar hankali. Idonsa a kasa, yana ta kokarin guje wa kallon kowa.

Major General Dawud ya gyara zamansa, yana dubansa da tsananin kulawa. “Mun san cewa kai ne jagoran da ya hada su Hajiya Rumanah da boka. Muna so ka fada mana komai.”

Malam Balarabe ya hadiye yawu. Ya san cewa babu inda zai iya tserewa daga wannan al’amari. Sai ya dauke numfashi, sannan ya soma magana.

“Tabbas, ni ne na kai su Hajiya Rumanah da su Hajiya Ladi da Hajiya Karama wajen boka. Sun zo wurina ne da bukatar su kawar da Hajiya Zaytunah da ‘ya’yanta gaba daya. Sun ce idan ba ta mutu ba, to su tabbatar ba za ta taba komawa gidan Alhaji Uzairu ba.”

Zuciyar Nabeeha ta buga da karfi. Fawaaz ya runtse idanuwansa, yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa.

Malam Balarabe ya cigaba, “Bokan ya musu aiki, amma bai tsaya nan ba. Ya kuma saka wata kurciya a jikin Hajiya Zaytunah, wanda zai hana ta tunanin komawa gidan mijinta ko yunkurin neman hakkin ‘ya’yanta. Wannan shine dalilin da yasa ta zauna a boye tsawon shekaru, tana gudun abinda ba ta fahimta ba.”

Duk wanda ke cikin dakin sai da zuciyarsu ta buga. Nabeeha ta rasa abin cewa. Tsawon rayuwarta, ba ta taba tunanin cewa akwai irin wannan mugunta a duniya ba.

Major General Dawud ya gyara zamansa. “To me yasa kake kokarin guduwa?”

Malam Balarabe ya sunkuyar da kai. “Boka ya fadi cewa idan aka tona asirin wannan aiki, akwai bala’i da zai bi wadanda suka aikata shi. Na san cewa da zarar an gano gaskiya, mutanen da suka ba da umarni za su yi kokarin kawar da ni. Shine yasa nake kokarin tserewa.”

Major General Dawud ya kalli daya daga cikin jami’an tsaron dake tsaye a gefen dakin. “Ku tabbatar da cewa an cigaba da tsare shi. Wannan mutumin na da matukar mahimmanci a bincikenmu.”

Bayan sun gama tambayoyin, Fawaaz ya fita daga dakin, zuciyarsa na tafarfasa. Nabeeha ta bi bayansa da sauri.

Ya tsaya a gefen wata bishiya, yana maida numfashi da karfi.

“Nabeeha,” ya fada cikin murya mai karfi. “Ina so ki san cewa ba zan taba barin wani ya cutar da ke ba. Ko da kuwa har abada ne.”

Nabeeha ta kalle shi da ido cike da al’ajabi. Wannan shine karo na farko da Fawaaz ya fadi irin wannan kalma gare ta.

Zuciyarta ta dan buga, amma sai ta sunkuyar da kai tana murmushi. “Nagode, Yaa Fawaaz.”

Daga wannan rana, komai ya fara komawa dai-dai.

Gwaggo Hafsat ta tabbatar da cewa Zaytunah ta samu cikakken lafiya. Hajiya Zaytunah ta sake farfadowa da karfinta, tana tunanin yadda zata sake gina rayuwarta da ‘ya’yanta.

Alhaji Uzairu ya kara kokarin gyara kura-kurensa, yana kokarin dawo da martabar sunansa a idanun Nabeeha da Hammad.

A bangaren Fawaaz kuwa, zuciyarsa ta fara karbar gaskiya, son da yake yiwa Nabeeha ba abu ne da zai iya gujewa ba.

Wata rana, lokacin da rana ke faduwa, Fawaaz da Nabeeha suna zaune a harabar gidan Major General Dawud.

Fawaaz ya kalleta da murmushi. “Kin taba jin cewa akwai soyayyar da ake ji a hankali, amma tana zurfi fiye da duk wata?”

Nabeeha ta kalle shi da dariya kadan. “Eh, na taba.”

Fawaaz ya yi murmushi, sannan ya dauke kansa daga kallonta. Zuciyarsa na bugawa, yana jin cewa wata rana, zai samu damar fada mata komai.

A yau, ba lallai ba ne. Amma yana da tabbacin cewa lokaci yana tafe.

Daren ya yi tsit a cikin gidan Major General Dawud. Ba kowa a lambun gidan sai Hajiya Hauwa, wadda take cikin rashin nutsuwa tana danna waya a gefe guda. Kamar yadda ta saba, tana kokarin tura sakonni ga wadanda suke tare da ita a boye.

Abin da ba ta sani ba shi ne, tun kwanaki Major General Dawud ya soma zargin cewa akwai wanda yake ba da bayanai a cikin gidan nasa. Ya lura da yadda wasu abubuwa suke tafiya ba dai-dai ba. Lokacin da aka yi garkuwa da Hajiya Zaytunah da ‘ya’yanta, sai abubuwa suka soma bayyana masa a hankali.

Yana tsaye a gefe yana kallonta, ba tare da ta sani ba. Idanunsa sun yi kalar takaici. A hankali ya dan matsa kusa, yana kallon yadda take rubuta wani sakon:

"Idan har kuna bukatar cikakken bayani, zan tura muku. Amma ina bukatar tabbatarwar ku cewa babu wanda zai iya kamani."

Gaban Major General Dawud ya fadi. Bai jira komai ba, ya karbe wayar daga hannunta da karfi.

Hajiya Hauwa ta zabura, idonta cike da tsoro. “Me kake yi haka?”

Major General Dawud bai kula da ita ba, ya shiga duba sakonninta. Akwai gamsassun shaidu masu nuna cewa ita ce ta sanar da mutanen da suka yi garkuwa da su Hajiya Zaytunah da iyalanta. Ita ce ta bada bayanin cewa suna cikin gidansa, wanda ya ba da damar a shirya yadda za a yi musu kisan gilla.

Gaba daya jikinsa ya dauki rawa. Ya dago kai ya kalleta, idanunsa cike da takaici.

“Hauwa… ke ce kika ba su bayanai?”

Hajiya Hauwa ta dauke kai, tana kokarin karyata shi. “Ni kuma?”

Dawud ya daga wayar yana nuna mata sakonnin da ta tura. “To me wadannan?”

Hajiya Hauwa ta kasa magana. Zuciyarta ta buga da karfi. Ta san cewa wannan karon ba ta da mafaka.

Major General Dawud bai bata lokaci ba. Nan take ya kama hannunta ya nufi sashen Gwaggo Hafsat, inda Hajiya Zaytunah ke zaune tare da ita.

Hajiya Zaytunah na zaune da dan nutsuwa, har yanzu tana kokarin farfadowa daga matsalolin da suka addabe ta. Gwaggo Hafsat kuwa tana zaune a kusa da ita, tana lura da ita.

Suna shigowa, Gwaggo Hafsat ta dubi Dawud da mamaki. “Lafiya? Me ke faruwa?”

Dawud ya saki hannun Hauwa da karfi. Ta durkushe a kasa, jikinta yana rawa.

“Gwaggo,” Dawud ya soma cikin muryar takaici. “Ganin da kike yi da wannan matar… tana da hannu a cikin duk abin da ya faru!”

Hajiya Zaytunah ta zabura. “Subhanallah! Me kake fada haka?”

Dawud ya daga wayar, yana nuna mata sakonnin da Hajiya Hauwa ta tura. “Duba wannan. Ita ce ta sanar da su inda kuke. Ita ce ta bada bayanai, kuma tana da alaka da wadanda suka yi garkuwa da ku.”

Gwaggo Hafsat ta kalli Hauwa da mamaki. “Hauwa! Ashe haka kike?!”

Hajiya Hauwa ta fashe da kuka. “Wallahi ba haka bane…”
Chapter 45 · 0% Book details