← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 75

Sashe 63

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidah sama da kasa gwaggo hafsatu ta bawa fawaaz kyauta. Da babban kamfaninta na sarrafa shinkafa da wani asibiti da yake mallakinta da wata gidauniya tadan itama duk ta bawa fawaaz. Acikin dukiyarta kaso uku . Kashi biyu ta barwa fawaaz. Lamarin sai Wanda yagani kawai .

Mai karatu kadana cikaka da surutu. Nasan duk wannan zantukan Dana zayyana zaace shagalin biki fa? To amarya da ango dai sunce basasan kowani event sun yafe.

Nabeeha dama irin kyalekyalen nan baso take ba. Tazo Kuma ta samu miji shima Mai masifar kishi bayason biki a kalle masa mata. Don haka tana cewa bataso shima ya amince. Har yafi Mai kora shafawa.

Bayan an gama shagalin dan hidimar cin abinci iya su yan gidan a parlor, an tafi gida cikin farin ciki. Sai dai Fawaaz da Nabeeha ba su bi ayarin mutane zuwa wajen su Gwaggo Hafsatu ba.

A maimakon haka, Fawaaz ya wuce da Nabeeha zuwa gida, inda sabuwar rayuwarsu za ta fara.

Ko da suka isa, yana gama rufe ƙofa, sai ya juyo ya kalleta. Idanunsa cike da natsuwa da wani irin so mai zurfi.

A hankali, ya tako har gabanta. Sai kuma ya ɗan sunkuya kaɗan, yana mai rikota da hannayensa duka

Fawaaz ya janye kaɗan, yana kallonta da wani irin kallo mai cike da zurfin so. Hannayensa har yanzu suna riƙe da nata, kamar yana tabbatarwa kansa cewa hakika, ta kasance tasa, ba tare da shakka ba.

"Kin san me, Nabeeha?"

Ta ɗan lumshe ido, tana jin yadda numfashinsa ke busa fuskarta. Ta buɗe idanu a hankali, tana kallonsa.

"Me?" Ta tambaya da wata murya mai laushi.

Ya yi murmushi, yana sanya yatsansa ya shafi gefen fuskarta a hankali.

"Na dade ina ɓoye SIRRI a cikin KIRJINa. HANKALI na baya sukuni akan ki.... Amma yanzu, ba SIRRI a tsakaninmu."

Zuciyarta ta harba da sauri. Ta ji yadda kalmomin nasa suka gama ratsata, suka shige har cikin zuciyarta.

Hannunsa ya shafi gefen kanta, yana kara matsota kusa da shi. Ta ji yadda numfashinsa ya daki fuskarta, kafin a hankali ya sanya labbansa ya sumbaci nata.

Ta rufe idanuwanta a hankali, tana jin wani irin yanayi mai daɗin gaske yana ratsata.

"Nabeeha…" Ya kira sunanta a hankali, yana sake shafa fuskarta.

"Ba zan iya rayuwa ba ke ba."

Ta buɗe idanuwanta da suka cika da ƙauna. A karon farko, ta fahimci cewa Fawaaz ba wai yana sonta bane kawai, yana jin ta a cikin jininsa.

A hankali ta jingina kanta da ƙirjinsa, tana jin bugun zuciyarsa yana tafiya tare da nata.

"Ni ma, Yaa Fawaaz… Ni ma."

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:56_

Fawaaz ya lumshe ido, yana jin dumin Nabeeha a jikinsa. Kamar a mafarki, yau ita ce a hannunsa, ita ce tasa. Ya dade yana ɓoye soyayyarta a Kirjin sa, yana ƙoƙarin danne zuciyarsa. Amma daga wannan dare, babu wani SIRRI a tsakaninsu.

Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ɗaga hannayensa ya riƙe fuskarta, yana kallonta da kyau.

“Kin san me yasa ba zan taɓa barinki ba, Nabeeha?”

Ta girgiza kai a hankali, tana kallonsa cikin ido.

Ya ɗan yi murmushi, sannan ya shafi kumatunta da yatsansa.

“Domin kece amincina. Kece nutsuwata. Kece wacce zuciyata ta zaɓa tun kafin na san dalili.”

Ta lumshe ido, zuciyarta tana harbawa da sauri. Jin kalmomin da suka gama tafiyar da ita.

“Ya Fawaaz…” Ta furta a hankali.

Ya sake shafa gefen fuskarta. "Nabeeha, ki sanarmun me ke zuciyarki. Na jima ina jira."

Ta ɗan yi shiru, tana kallonsa. Sai ta ajiye tafin hannunta a kirjinsa, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa.

"Ka san me, Ya Fawaaz?"

Ya gyada kai, yana jiran jin abin da za ta faɗa.

"Tunda nake, ban taɓa jin tsaro irin na kasancewa a kusa da kai ba."

Ya ɗan murmusa, yana sake shigar da hannayensa ta bayanta, ya matseta a jikinsa.

"Na jima ina jiran jin hakan daga gare ki."

Ya sunkuya, yana sake sinsinar gefen kunnenta, sannan ya sauke ajiyar zuciya.

"Ina sonki, Nabeeha."

Ta rufe idanuwanta, zuciyarta tana tafasa da kauna.

"Ni ma, Ya Fawaaz... Ina sonka."

A wannan dare, babu wani sirri da ya rage tsakanin zuciyoyinsu. Duk wani tunani da shakku sun ɓace. Soyayya ce kaɗai ta zauna, ta cika sararin zuciyarsu.

A hankali, Fawaaz ya dago fuskarta yana kallon cikin idanunta da ke cike da soyayya. Zuciyarsa tana tafasa da wani irin shauƙi da bai taɓa jin irinsa ba.

Ya sanya tafin hannunsa ya rufe nata a HANKALI, yana jin dumin hannayenta da wani sanyi mai ratsa jikinsa.

"Kin san me, Nabeeha?" Ya furta da murya mai ƙasa, cike da soyayya.

Ta lumshe ido a hankali, sannan ta buɗe su, tana kallonsa. "Me?"

Ya yi murmushi, yana shafa ƙananan yatsunta da nasa.

"Soyayyarki tana da zuma. Amma akwai madaci a cikinta."

Ta ɗan zaro ido, cikin rashin fahimta. "Madaci?"

Ya gyada kai, yana kallonta da ƙwarewa. "Eh. Domin na jima ina ƙaunarki, amma ban iya faɗa ba. Wannan ne madacin."

Nabeeha ta cije laɓɓanta, zuciyarta tana harbawa da sauri. Wata soyayya mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali tana ratsa zuciyarta.

"Kuma zumar fa?" Ta tambaya tana kallonsa da idanunta masu laushi.

Fawaaz ya murmusa, sannan ya kamo laɓɓanta da yatsansa. "Zumar ita ce ke yanzu a jikina. Ba SIRRI tsakaninmu."

Tayi shiru, tana kallonsa da wani yanayi na zurfin soyayya. Sai ta sanya kanta a KIRJIN sa, tana jin bugun zuciyarsa.

"Ya fawaaz…" Ta furta a hankali.

Ya ɗan lumshe ido, yana sake shinshinar ƙamshin gashinta. "Na’am, Nabeeha?"

Ta ɗago da fuskarta, idanunta cike da natsuwa. "Za ka riƙe ni har abada?"

Ya murmusa, yana ɗan kifa goshi da nata. "A duniya da lahira, Nabeeha."

A haka suka kasance, zuciyoyinsu a haɗe, ba tare da shakku ko jin tsoro ba. Fawaaz ya jingina goshinsa da nata, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. A yanzu, babu wani shakku a zuciyarsa. Ta zama tasa, har abada.

Hannunsa ya sauka a fuskarta, yana shafa laushin kumatunta da yatsansa. "Nabeeha..."

Ta lumshe ido, tana jin yadda muryarsa ke ratsata kamar sautin zuma. "Na'am?"

Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya yi murmushi. "Kin taba jin ana yin soyayya a cikin sirri?"

Ta buɗe idanuwanta, tana kallonsa. "Ban gane ba."

Ya dube ta da idanunsa masu cike da zurfi. "Tun da nake, ban taɓa fadar soyayyarki ba. Amma kin zauna a cikin zuciyata, kamar wata ƙaunar da ba kowa ya san tana wanzuwa ba."

Ta lumshe ido, zuciyarta na harbawa da sauri. " Ya Fawaaz..."

Ya yi shiru yana kallonta, yana jiran abin da za ta ce.

"Ina jin kamar ina raye ne a cikin zuciyarka, ba a duniya ba."

Ya ɗan murmusa, yana riƙe hannayenta da ƙarfi. "Kin faɗi gaskiya, Nabeeha. Tunda nake, ban taɓa jin wata mace a zuciyata ba irin yadda kike ciki."

Ta ɗan sunkuya, tana rufe fuskarta cikin tafin hannunta. Soyayyar da take ji a zuciyarta ta yi mata yawa.

Ya kama hannayenta ya janye daga fuskarta, yana kallonta da murmushi. "Ki daina ɓoyewa, Nabeeha. Zuciyarmu ɗaya ce yanzu."

A hankali ya sanya labbansa ya sumbaci goshinta, yana furta cikin siririyar murya,

"A yanzu, babu wani sirri a KIRJINa, Kin zama SIRRI na, Nabeeha."

Idanunta suka cika da hawaye, ba na bakin ciki ba, na farin ciki. "Ya Fawaaz... Ina sonka."

Ya matseta a jikinsa, yana shinshinar ƙamshin fuskarta. "Ni ma, Nabeeha. Fiye da yadda zan iya faɗa."

A yau, zuciyoyinsu sun haɗu gaba ɗaya. Kuma babu wani SIRRI da zai rabu da su. AKWATIN SIRRIN SA ya buɗe, kuma SIRRIN da ke cikinsa shi ne soyayya.

A lokacin da Nabeeha har yanzu ke cikin matsananciyar mamaki, zuciyarta na harbawa da sauri, Captain Fawaaz Dawud ya yi abu da ba ta taba tsammani ba. Kafin ta fahimci me ke faruwa, ya dauke ta cak cikin hannayensa, kamar yadda ake daukar jaririya.

"Ya fawaaz—" Ta yi kokarin magana, amma ya kalle ta da wata irin murya mai kwantar da hankali.

"Shh… you are mine, Nabeeha. Tonight, I will make you understand what that means."

Ya nufi dakin da aka kawata da hasken fitilu masu laushi, yana rike da ita kamar wata amana mai daraja. A hankali ya kwantar da ita a kan gadon da kayan shimfida masu laushi ke lullube da shi, yana kallonta da idanunsa masu cike da soyayya.

Sai ya zauna kusa da ita, yana shafa fuskarta da yatsunsa cikin kwarewa. Ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan kumatunta, a hankali kamar yana jin dadin jin dumin fatarta.

"Nabeeha, do you know what you mean to me?" Ya tambaya, yana kallon ta cikin ido.

"I don't know…" Ta furta cikin wata murya mai sanyi, zuciyarta na dokawa.

Ya yi murmushi mai dauke da wata nutsuwa, sannan ya shafa gefen fuskarta. "You are the most precious gift Allah has given me. My heart, my soul, my peace. You are mine, and I will cherish you forever."

Ya ci gaba da yi mata sumbata a goshinta, gefen wuyanta, sannan ya tsaya yana kallonta da idanu masu cike da shauki.
Chapter 63 · 0% Book details