← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 75

Sashe 60

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa da ido kawai.

Ya lumshe ido kadan, sannan ya bude su da wani yanayi na SIRRIN ta ne kawai zai iya fassara. “Kin taba jin yadda zuciya ke ji idan tana son abu da gaske?”

Ta dan girgiza kai. “Ban sani ba.”

Ya yi murmushi kadan, sai dai murmushinsa mai nauyi ne. “Zuciya ba ta da hayaniya, amma tana da karfi. Idan ta kamu da so, ko da baka fadi ba, sai duniya ta fahimta.”

Tayi shiru, zuciyarta na harbawa da sauri.

Ya dan matsa kusa da ita, murya a hankali. “Kin san nawa lokacin da zuciyata ta dauka tana son ki?”

Ta girgiza kai. “ Yaa Fawaaz…”

Ya kara matsowa kadan, idanunsa cike da gaskiya. “Tun kafin kisan meye soyayya.”

Nabeeha ta kasa cewa komai.

Ya sauke numfashi a hankali, yana kallonta da idanu masu cike da soyayya. “Ke ce SIRRI na, Nabeeha. AKWATIN SIRRIN da zuciyata ta rufe tsawon lokaci.”

Ta lumshe idanu, zuciyarta na bugawa da sauri. Wannan kalaman da yake fada, ba yau suka taso ba. Ya dade yana ajiyesu a zuciya. Kuma yanzu, sun fito fili kamar yadda haske ke bayyanar da komai a dare mai duhu.

A hankali, ta bude ido, tana kallon shi da fassara mai zurfi. “ Yaa Fawaaz…”

Ya dan matse hannunta, yana jin yadda jikinta ya dauki dumi. “Ba zan bukaci komai daga gare ki ba, Nabeeha. Sai dai abu guda…”

Ta kara kasa da murya. “Mene ne?”

Ya yi murmushi, yana juyar da kallonsa gefe kadan. “Kada ki bar zuciyata ita kadai a cikin wannan tafiyar.”

Idanunta suka kada, zuciyarta ta dauki zafi. Shin yana nufin... tana da wani matsayi da ya wuce abokiyar rayuwa a cikin zuciyarsa?

Fawaaz ya dago yana kallonta da ido masu cike da soyayya, amma ba tare da ya ce wani abu ba. Sai numfashinsa da ke bayyana nauyin abin da ke zuciyarsa.

Shiru ya ratsa tsakanin su. Sai dai ba irin shiru na rashin magana ba—shiru ne mai cike da fassara, mai cike da abinda kalmomi ba za su iya bayyana ba.

Fawaaz ya fadi soyayyarsa. Kuma yanzu… Nabeeha ce ke da hakkin yanke hukunci.

Nabeeha ta dauke numfashi a hankali, zuciyarta na harbawa da sauri. Ta kasa dauke idanunta daga nashi, kamar tana neman wani abu a ciki. Fawaaz kuwa, sai ya dan ja da baya kadan, yana kallonta da kwanciyar HANKALI, amma a ciki, akwai abu da yake kokarin boyewa.

Ya san kalmomin da ya fada suna da nauyi. Ya san ya bude AKWATIN SIRRIN da ya daɗe yana adanawa a zuciyarsa. Amma ba ya da nadama.

Shi kam, ba shi da wata bukata sai dai jin abin da Nabeeha ke ji.

“Ina jiranki a mota,” ya fada a hankali, yana dauke kansa.

Nabeeha ta yi shiru, har sai da ya juya zai bar wurin. Da sauri ta kira sunansa.

“Yaa Fawaaz.”

Ya tsaya cak, amma bai juyo ba.

Tayi shiru na wani lokaci, sai kuma ta dan gyada kai. “Ba zan bar zuciyarka ita kadai ba.”

Fawaaz ya runtse ido na wani dan lokaci. Wannan kalma ta shiga cikin zuciyarsa fiye da duk wani abu da zai ji a yau. Sai kuma ya yi murmushi—murmushin da ya saba ɓoyewa.

Ya juyo a hankali, yana kallonta da ido masu cike da jin dadi. “Nagode.”

Ya fadi haka kawai. Amma cikin wannan "nagode", akwai soyayya, akwai nutsuwa, akwai alƙawari.

Tafiyar su gida tayi shiru. Amma ba irin shiru na damuwa ba—shiru ne na zuciyoyin da suka soma fahimtar juna ba tare da kalmomi ba.

A lokacin da suka isa kofar gidan su, Nabeeha, Fawaaz bai yi kokarin bude mata kofa ba kamar yadda ya saba. Sai dai ya tsaya, yana kallonta da nutsuwa.

“Ina so ki huta da kyau,” ya fada a hankali.

Nabeeha ta gyada kai, zuciyarta cike da wani irin yanayi mai daɗi. “Kai ma.”

Ta sauka daga motar, amma kafin ta rufe kofar, sai ta juyo.

“Ya fawaaz.”

Ya kalleta, yana jiran abin da za ta fada.

Sai tayi murmushi. “KIRJIN MAI HANKALI—AKWATIN SIRRIN SA.”

Zuciyarsa ta buga. Bati taba Jin kalamen sun masa dadi, cikin sanyin fuska mai daɗi irin haka ba.

Ta rufe kofar a hankali, sannan ta juya ta shige gidan, zuciyarta tana harbawa da sauri.

Fawaaz kuwa, ya jima a zaune a wurin, yana murmushin da shi kadai ya fahimta.

A wannan dare, zuciyoyin su biyu sun cika da sabbin tunani. Fawaaz bai koma gida kai tsaye ba. Sai da ya dan tsaya a gefen titi, ya sauke numfashi a hankali, yana kallon dare. Bai taba tunanin cewa rana irin ta yau za ta zo ba—rana da zai furta SIRRIN da ya adana tun kafin ya fahimci cikakken ma’anarsa.

A gefe guda kuwa, Nabeeha ta shige dakinta tana jin kamar kanta yana shawagi. Zuciyarta tana bugawa da wani yanayi da ba ta taba jin irinsa ba. "Ba zan bar zuciyarka ita kadai ba." Ta fada masa. Wannan kalma tana maimaita kanta a cikin kwakwalwarta.

Shin menene ma’anarta a gare ta? Ta san cewa tun tuni Fawaaz ya ke kulawa da ita fiye da kowa. Ya riga da ya kafa bango mai karfi tsakanin ta da duk wani hadari. Amma yaushe ya fara ganin hakan a matsayin soyayya? Kuma ita fa? Shin ta riga ta san abin da ke zuciyarta?

Tana cikin dogon tunani, sai wayarta ta dauki ringing. Humyrah.

Ta dauka a hankali. “Hello.”

Muryar Humyrah cike da tsokana ta doki dodon kunnenta. “Kin iso gida lafiya?”

“Eh,” ta amsa a kasalance.

Humyrah ta ja tsaki. “Karki min haka, Nabeeha. Na san kin shige a duniyar tunani. Amma ai babu wanda ya fi ni jin dadin abin da ya faru a yau.”

Nabeeha ta dan runtse idanu. “Meye hakan?”

Humyrah ta yi dariya. “Ke dai bari. Ina ganin yadda Ya fawaaz ya dade a waje bayan na fito. Wallahi idan so yana da fuska, to fuskar Ya fawaaz ce yau.”

Nabeeha ta daure fuska. “Humyrah, ki bar wannan.”

Humyrah ta yi dariya. “Ai ba za ki iya musantawa ba, domin yanzu kowa ya san gaskiya. Yaya Fawaaz yana son ki, Nabeeha! Kuma ba yau ya fara ba. Abin da kawai ya rage shine—ke fa?”

Wannan tambaya ta tsaya a zuciyar Nabeeha, ta kasa amsawa.

Da safe, Fawaaz ya fita da wuri, ba tare da ya jira kowa ya tambaye shi ba. A lokacin da ya dawo daga aiki, yana cikin mota yana kokarin shiga gidan su, sai ya hangi Nabeeha a bakin kofar gida tana jiran abu kamar mai son fita.

Ya dan tsaya a gefe, yana kallonta kafin ya sauke glass na motarsa.

“wani wajen zaki?”

Nabeeha ta juya, ta gan shi, sai zuciyarta ta buga. Duk da jiya sun raba dare da tunani, yau kuma ganin shi a fili ya kara tayar da HANKALIn ta.

“Eh,” ta amsa a hankali.

Ba tare da ya yi wata-wata ba, ya bude mata kofar mota. Ta shiga, zuciyarta na bugawa da sauri.

Lokacin da ya fara tafiya, babu wanda ya fara magana. Sai shiru mai cike da fassara.

Daga bisani, sai Fawaaz ya kalleta da ido mai zurfi. “Nabeeha.”

Ta juyo tana kallonsa.

Ya dauke idanunsa daga hanya ya sauke a kanta. “Jiya na kwana ina tunani.”

Ta hadiye yawu, ba tare da ta iya cewa komai ba.

Ya sauke numfashi. “Kin ce ba za ki bar zuciyata ita kadai ba.”

Ta gyada kai.

Ya dan yi murmushi, sannan ya jefa tambaya wacce ta tsaya mata a zuciya kamar an rubuta da zinariya.

“Amma kin san dalili?”

Zuciyarta ta buga, amma ba ta da amsar da zata bashi.

Shiru ya biyo baya.

Shi kuwa Fawaaz, sai ya mayar da hankalinsa ga hanya, amma da alama zuciyarsa da tunaninsa duk suna kan ita Nabeeha.

A ransa, yana jira ta gane kanta. Amma zai iya jira? Hakan ne tambayar da bai da amsar sa.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:54_

Nabeeha ta dan lumshe ido, zuciyarta na bugawa da sauri. Tambayar Fawaaz ta tsaya mata a zuciya, kamar sautin da ya tsaya a kunne ba tare da ya fita ba.

“Amma kin san dalili?”

Tayi shiru, ta kasa amsawa. Ba don bata da amsar ba, sai don bata san wacce ta dace da furta ba. Shin yana nufin yana son jin idan soyayyarsa tana da amsa daga zuciyarta? Ko kuwa tambayarsa wata hanya ce ta tabbatarwa kansa cewa ba shi kadai yake tafiya a cikin wannan yanayi ba?

Shi kuwa, yana kallonta daga gefen ido, yana jiran ta ce wani abu. Amma babu komai.

Daga karshe, sai ya sauke numfashi a hankali. “Ba sai kin amsa yanzu ba.”

Ya mayar da kallonsa ga hanya, yana ci gaba da tukinsa da nutsuwa. Amma zuciyarsa bata da kwanciyar HANKALI. Ita kuwa Nabeeha, sai ta tsinci kanta cikin wani yanayi na dogon tunani.
..

Bayan sun isa kofar gidan Humyrah, saboda shirye shiryen presentation na term paper da zasuyi na makaranta, Fawaaz ya tsaya yana kallon agogon hannunsa.

“Kar ki daɗe,” ya fada a hankali.
Chapter 60 · 0% Book details