← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 75

Sashe 71

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da jin karar horn din motarsu, sai ga Humayrah da Raudah sun fito da sauri, fuskokinsu cike da farin ciki.

"Ah! Lallai yau mun sha mamaki!" Humayrah ta fada tana dariya.

Raudah ta ruga ta rungume Nabeeha. "Aunty Nabeeha! Kin tuna da mu yau?"

Nabeeha ta rungume ta itama tana dariya. "Ai ba zan iya mantawa da ku ba, kun fi kowa."

Fawaaz ya kalli kannensa yana murmushi. "Ku dai kun fi son Nabeeha a kaina, ko?"

Humayrah ta gyada kai da wasa. "Eh mana, ai ita ce ta fi sanin yanda za ta yi mana lallashi."

Suka yi dariya gaba daya, sannan suka shiga gidan cikin nishadi da farin ciki....

Dake gidan Raudah Dana humyrah ba nisa sosai. A estate daya suke. Shi ya sanya humyrah taje gidan Raudah suka hadu gaba daya...

_____

Tunda safe Gwaggo Hafsatu ke zaune a falonta, tana lazimi cikin nutsuwa. Koda aka sanar da ita cewa Fawaaz da Nabeeha za su kawo mata ziyara tare da Humayrah da Raudah, sai ta ji wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarta.

Bata jima da idar da azkar ba, sai ga su sun iso. Mai gadi ya bude musu ƙofar, suka shigo cikin harabar gidan cikin natsuwa. A lokacin da suka sauka daga mota, suna kokarin shiga cikin gidan, sai ga Gwaggo Hafsatu ta fito zuwa zaure da fara’a a fuskarta.

"Ah! Lallai yau na samu dama. Jikokina sun zo ne gaba ɗaya?!"

Dariya suka yi gaba ɗaya, sannan suka karasa kusa da ita.

Nabeeha ta durƙusa cikin girmamawa, tana fadin, "Granny, ina wuni?"

Ta amsa da fara’a, tana shafa kanta. "Lafiya lau, Nabeeha tah. Yau nasan zan ji daɗi sosai."

Humayrah da Raudah ma suka gaishe ta, sannan suka zauna kusa da ita, suna jin ɗumin soyayyarta.

Daga nan sai ga Major General Dawud ya fito daga sashensa, yana kallon su da murmushi a fuskarsa. "Ah, yau an yi baƙi na musamman."

Fawaaz ya sosa ƙeya yana murmushi. "Ai su suka ce sai na zo tare da su, idan ba haka ba, da an bar ni a gida."

Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da wasa. "Na san dai ke ce kika sa shi ya zo."

Nabeeha ta yi murmushi tana kallon ƙasa. "Ai ya dace ya zo Gwaggo, ba zai tsira ba."

Suka fashe da dariya gaba ɗaya.

Major General Dawud ya zauna, yana kallon su da kulawa. "Yau na samu ikon zama tare da ku, ya kamata ku kawo min labarai."

Humayrah ta yi dariya, tana cewa, "Ai Baba, tunda ba ka fiye zama a gida ba, yau sai mun dame ka da hira."

Raudah ta gyara zama tana cewa, "Ko da yake, Aunty Nabeeha ita ce zata fi ba da labarai, tunda ita ce ta fi shiru kullum."

Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da murmushi. "Yau zan zauna na ji yanda kike jituwa da Fawaaz."

Fawaaz ya yi gyaran murya, yana kallon Nabeeha da wasa. "Ai nasan za ta ce kina son jin SIRRIN mu ne."

Dariya suka yi gaba ɗaya.

Bayan dan lokaci, an kawo musu kayan ciye-ciye da ruwan zafi. Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da kulawa, tana cewa, "Yaya kike ji a gidan Fawaaz? Yana kula da ke sosai kuwa?"

Nabeeha ta kalli Fawaaz, sai kuma ta yi murmushi tana cewa, "Eh Gwaggo, yana kula da ni. Kullum yana kokarin faranta min rai."

Gwaggo Hafsatu ta kalli Fawaaz da murmushi. "Ka ga kuwa? Wannan shi ne abin da nake so."

Major General Dawud ya yi murmushi yana gyara zama. "Ai Fawaaz ya gaji da jin kunya, tunda har Nabeeha ke yaba shi a fili."

Suka fashe da dariya gaba ɗaya.

A haka suka ci gaba da hirarsu cikin annashuwa, suna jin daɗin kasancewa tare da juna. Gwaggo Hafsatu ta yi wa Fawaaz da Nabeeha addu’a, tana rokon Allah ya kara musu soyayya da fahimta, sannan ta shafa musu albarka.

Bayan sun jima, suka tafi da alkawarin cewa ba za su jima ba sosae zasu sake dawowa wata ziyarar bi'iznillah.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:63_

Tunda asuba Nabeeha ta farka tana shirin tafiya gidan iyayenta. Tun a kwanakin baya take shirin wannan ziyara, saboda ta dade ba ta ziyarce su ba. Tun kafin auren ta, Fawaaz ne ya lallaɓa ta suka ɗauki lokaci suna jira har zuwa lokacin da zai dace, don su tafi tare.

A yau kuwa, babu wani uzuri. Sun shirya, suka fita da safe domin yin ziyarar gaisuwa ga mahaifiyarta, Hajiya Zaytunah, da mahaifinta, Alhaji Uzairu.

A cikin mota, Nabeeha ta naɗe kanta da mayafi, tana kallon tituna cikin farin ciki. Fawaaz ya dan juyo ya kalleta yana murmushi.

"Kin yi shiru, ko kina tunanin yanda za a tarbe mu?"

Ta juyo tana murmushi. "A’a, kawai ina tunanin dadin ganin su ne. Na dade ba na tare da su."

Ya girgiza kai yana cewa, "To yau sai an yi zaman hira mai kyau, tunda ke ma kin zo da shirin dadewa."

Tafiyar ba ta dauki lokaci mai tsawo ba, suka iso kofar gidan. Mai gadi ya gansu, da sauri ya bude musu kofa da murmushi.

"Sannu da zuwa, oga Fawaaz da Hajiya Nabeeha!"

"Yawwa Baba Lawal, ya gida?" Fawaaz ya tambaya, yana ajiyar motarsa.

"Alhamdulillah."

Suna fitowa daga mota, sai ga Hajiya Zaytunah ta fito daga cikin gida da fara’a, har tana dan tafiya da sauri saboda farin ciki.

"Ah! Lallai yau na sha mamaki! Nabeeha da Fawaaz a tare?"

Nabeeha ta durƙusa tana gaida mahaifiyarta, tana murmushi. "Ammi, ina wuni?"

Hajiya Zaytunah ta kama hannunta cikin kulawa. "Lafiya lau."

Fawaaz ya gaishe ta da ladabi. "Ina kwana Hajiya?"

Ta amsa da fara’a. "Lafiya, Fawaaaz. Ya aikin soja. Da na bindiga"

Suka yi dariya gaba daya, sannan suka shiga cikin gida.

Da suka shiga falo, Alhaji Uzairu yana zaune yana karanta jarida. Da ganin su, ya ajiye takardun yana kallonsu da kulawa.

"Ah! Nabeeha da Fawaaz kenan?"

Nabeeha ta durƙusa tana gaida shi cikin ladabi. "Baba, ina wuni?"

Ya amsa da murmushi. "Lafiya lau, ‘yata. Ya hanya kunzo kalau"

"Eh Baba, Alhamdulillah."

Fawaaz ya gaishe shi da ladabi, yana zama kusa da shi. "Ina wuni, Alhaji?"

Alhaji Uzairu ya amsa da murmushi. "Lafiya lau, Fawaaz. Yau kun kawo mana ziyara ko?"

"Eh, baba"

Nabeeha ta juyo tana kallon mahaifiyarta da murmushi. "Ammi, ya gida? Ya su Hammad?"

"Lafiya lau, Hammad yana can kasar karatun sa"

Suka zauna cikin natsuwa, ana tattaunawa kan abubuwan da suka faru tun daga lokacin da aka yi aure zuwa yanzu. Hajiya Zaytunah na kallon Nabeeha da kulawa, tana jin farin cikin ganin yarinyarta cikin koshin lafiya.

Bayan an yi dan lokaci ana hira, Hisham dan hajia karama ya shigo parlorn. Dake duk yaran suna hannun hajiya Zaytunah itake rike da su a yanzu..

"Kai! Yau dai Aunty Nabeeha ta zo mana?"

Nabeeha ta kalle shi tana murmushi. "Ai kuwa na zo. Kai ma ka dade ba ka ganni ba."

Ya zauna kusa da ita, yana fadin, "Ai dama kullum muna magana da Ammi, tace za ki zo."

Fawaaz ya kalle shi yana dariya. "Kana nufin ba ka yi missing dinta sosai ba kenan?"

Suka yi dariya gaba daya.

Bayan an sha hira, an ci abinci, sannan suka ce za su wuce gidan Alhaji Amiru da bangaren Gwaggo Zainabu.
..

Da suka iso gidan Alhaji Amiru, mai gadi ya bude musu kofa, suka shigo cikin mutunci. Da zarar sun shiga falon, Gwaggo Zainabu ta fito da fara’a tana kallonsu.

"Ah! Nabeeha da Fawaaz! Wannan ziyara ta musamman ce."

Nabeeha ta durƙusa tana gaishe ta. "Gwaggo, ina wuni?"

Ta shafa kanta da kulawa. "Lafiya lau, ‘yata. Yau kun tuno da mu kenan?"

Fawaaz ya gaishe ta da girmamawa. "Mukace bara mu zo mu gaishe ku."

Alhaji Amiru ya fito yana kallonsu da murmushi. "Kun kyauta. Sannun ku da kokari"

Suka zauna cikin falo, ana hira mai dadi. Gwaggo Zainabu na jin daɗin ganin Nabeeha, tana tambayarta game da zamanta a gidan Fawaaz.

"Kin more zaman aurenki ko?" Ta tambaya tana kallonta.

Nabeeha ta yi murmushi, ta kalli Fawaaz sannan ta juyo tana cewa, "Eh Gwaggo, Alhamdulillah."

Fawaaz ya sosa ƙeya yana murmushi. "Ai ko da ba ta fada ba, nasan cewa tana jin daɗi." Sukayi wasan kaka da jika da Gwaggon.

Suka yi dariya gaba daya.

Bayan sun jima suna tattaunawa, suka sha fura, sannan suka ce za su wuce gida.

Gwaggo Zainabu ta shafa kan Nabeeha da addu’a. "Allah Ya albarkaci zaman aurenku, Ya kara mana fahimta da so."

Alhaji Amiru ya kalli Fawaaz da murmushi. "Ka kula da ita sosai."

"In sha Allah, Abba"

A haka suka yi sallama da iyayensu, suka koma gida cikin farin ciki, suna jin daɗin ziyarar da suka kai.

🎀🎀
Bayan kwanaki da ziyarar da suka kai gidan iyayen Nabeeha da danginta, sai Fawaaz ya shirya tafiya da ita zuwa Bokezuwa – kauyen mahaifiyarta, Hajiya Zaytunah. Tun bayan da ta fara jin labarin tushenta, Nabeeha ta daɗe tana son ganin garin da mahaifiyarta ta fito, wurin da danginta suka rayu kafin rayuwa ta raba su.
Chapter 71 · 0% Book details